← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 116

Sashe 30

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

   44
  Ta bi bayansa kuwa, ta yi mamakin ganin ashe ba wata doguwar tafiya bace, ya bude kofa suka shiga babban falon Hajiya Babba. Wani kamshi sassanya ya bugi hancinta har tana sauke numfashi, kunya da nauyi suka cikata domin falon babu kowa sai samarin da su Baraka da matan yayyun ana hira da dariya. Tun shigowarta ya jefeta da kallo daya ya kauda kansa duk a kokarinsa na yak'i da zuciyarsa game da ita. Ya maida hankali ga Ihsan wacce ke faman yi mishi surutu ko kusa bai fahimtar inda ta dosa ma. Ta russuna ta gaishesu da tattausar murya, suka amsa. Anti Aisha bata falon, hakan yasa ta yi karfin halin tambayar Ihsan.
"Ihsan, ina Anti Aisha?"
Ihsan ta yi tamkar bata ji ba don haka kawai ta tsani ganin Ummi awajen yaran Hajiya Babba, ta rasa dalili don ko Amina bata jin hakan akanta sai ita Ummin. 
  Faruk ya zubawa Ummi fararen idanunsa, ta kauda kai. Alokacin ne Adnan ya bata amsa.
"Tana sama ina ji, jeki ki duba."
Ta dubi hanyar saman, to wane dakin zata dosa ne?
  "Tashi ki rakata." Ta tsinci muryar Faruk sadda ta ke kokarin mik'ewa, sauran yayyun hankulansu naga hirar da sukeyi suna tuntsirar dariya. 
  Ta soma tafiya ta ji Ihsan ta bangajeta ta yi gaba da fadin.
"Ki biyoni."
  Ta jinjina kai ranta na suya saidai babu halin tankawa, haka tayita binta tamkar rak'uma. Ya kasa kauda kai daga gareta har saida ta 6acewa ganinsa kafin ya juyo kansa sukayi ido hud'u da Jidda matar Dr Ridwan. Ta daga mishi gira kadan 
"Ya akayi? Akwai fa wani abu."
Faruk ya yamutse fuska.
"Kefa matarnan kin samin ido wallahi."
  Yan uwan sukayi dariya. Jidda ta dubesu.
"Na gayamaku ai akwai wani abu tsakanin wannan kanin naku da Ihsan kun k'i aminta, bakuga irin kallon da ya bita da shi ba yanzu."
Faruk ya dubeta duban rashin fahimta.
  "Ihsan kuma? Please karki jawomin raini mana."
  "Wane raini anan? Kaidai fadi gaskiya Malam, irin wannan kallon ba'a yinsa sai ga wanda ake tsananin so. Da idona fa na kamashi."
  Haidar ya kai mishi naushi a kafad'a yana dariya.
"Kyalemin kanina Maman Ma'aruf, idan ma hakan ne da bakinsa zai fad'a ai."
 Takaici ya ishi Faruk, ga shi a gaban kannensa ne kada su rainashi, ya watsawa su Baraka wani kallo, ba shiri suka mike har Intisar sukayi sama. Ai kuwa yayyun suka kwashe da dariya.
   "Aa, ya zaka korarmin matata?"
Faruk ya shagwa6e murya.
"Wai ni menene haka don Allah? Kun ta6a ganina da wata nace ina so ne da za a takuramin?"
  "Munfi kaunar ka ce din ai k'anina, akan ka zauna kana kallonsu tamkar wani dutse."
  Cewar Haidar cikin rad'a. Faruk ya lumshe ido ya bude alamar gajiyawa da jin zantukansu, mikewa ya yi tsaye.
  "Please stop this, ku rufamin asiri ma kada ta ji  raini ya biyo baya."
  Daga haka ya bar wajen. Suna kiransa amma ko waige. Adnan dake kallonsu ya riga ya gano wacce bestinnasa ke kallo ya kuma fahimci lallai akwai abinda Faruk ke 6oyewa a ransa, watakil ma bai fahimci komai ba har zuwa yanzun. 

    Acan kuwa Ummi goyon Tahir aka bata, daga nan aka hadata da kayan wankinsa ta sauko. 
   Babu wanda ya damu da kallonta haka ta wucesu zuwa sashensu goye da Tahir a bayanta wanda baikai ga yin bacci ba. Tazo wucewa ta hanyar da ta biyo ne ta hangi kofar nan ta wajen pool a bude.
"Ya akayi na manta ban rufe ba?"
Fadin haka yasa ta nufar wajen don rufewa. Ta hangi Faruk zaune saman kujerar wajen ya jingina kansa jikin kujera, jin alamun mutum yazo wucewa ne yasa shi waigowa batare da ya raba kansa da jikin kujerar ba. Ya dubeta, da sauri ta saki kofar ta juya don barin wajen.
"Kina neman wani abu ne?" Ya kira sunanta a hankali, gabanta ya hau dukan tara-tara ta juyo a gigice ta amsa da "A'a, kayi hakuri na dauka dazu ban rufe ba shine nayi niyyar rufewa yanzun."
  Ya tsaya kawai yana k'are mata kallo, itama kuma ta juya har lokacin bata da nutsuwa ta fice da sauri. Ya numfasa gami da shafar sumar kansa.
"Ya Allah, wannan wane irin yanayi ne? What's about to happen?"
  Ya fada a fili....

Duk iyaka tunaninsa bai fahimci komai ba hakanan ya share zancen, bai mik'e daga wajen ba sai da ya ji ansoma kiraye-kirayen sallar isha'i.
  Bayan an idar suka ci abinci da yan uwansa sannan kowannensu ya kama hanyar gidansa bayan an gaisa da Daddy. 
  Washegari 'yan Adamawa da wasu da yawa daga dangin Daddy na Kano suka iso. Gidan ya cika kwarai kasancewar wannan ne bikin 'ya mace na fari a gidan, sauran duk maza ne. Su Ummi kam babu ta hutu, sune wancan sune wannan, haka suke wuni aiki. Daga rainon yaran su Rahila sai taimakawa wajen wanke-wanke.
   Ranar Asabar aka soma biki inda aka sanya Baraka a lalle. A ranar dai kuma za'ayi kamu, a katon filin farfajiyar gidan akayi, wajen ya tsaru matuk'a sai ka rantse cewar ba a gidan bane. Kwalliyar fari da golden aka yiwa wajen, Amarya Baraka ita kuwa ta fito cikin farin leshi, nad'in kanta kuma kalar golden. Yanmatan kaf din su doguwar riga sukayi (golden), iyaye ne kowa yasa ra'ayinsa. Ummi ta had'e itama cikin wani jan leshi da Mami ta yi mata kyautarsa acikin kayan Ihsan, ta yi kwalliyarta daidai misali har da kwalli a idanunta, duk da hakan ba k'aramin kyau ta yi ba. Amina ita kuwa yadi kore ta saka mai adon fulawoyi. Suna daga can kujerun baya, Ummi na rungume da Tahir tana aikin raino. A haka suke kallon komai. Babu abinda ya burgeta kamar(step-dance) wanda Ihsan, Maryam (mai bi wa Intisar 'ya ga Hajiya Mama), Rukayya (mai bi wa Maryam) da kuma Ikram sukayi na wata wak'ar turanci (Looku-looku) sukayi. Sunyi shigar riga da wando, Ihsan da Maryam kuwa a maza suka fito. Abin ya yi kyau matuka kuma ya burge har ihu da tafi ya cika wajen, ga baibayesu da akayi ana daukar hotuna da bidiyo. 
   Ifice-ificen ne ya hana Tahir nutsuwa, ya hau canyara ihun kuka. Duk iyakar rarrashin da sukayi mishi ita da Amina ya k'i nutsuwa. Amina ta dubeta.
"Ko za ki kaishi wajen Mamanshi?"
Ummi ta hangeta can sai harkar gabanta ta ke yi, ta girgiza kai.
"Bari na dauko zani na goyashi mugani."
  Amina ta harareta.
"Haba dai goyo, kinga kyan da riga da siket din ya yi miki kuwa? Don Allah kar ki soma goyon nan za ki 6ata kwalliyarki."
Ummi ta yi dariya, ita bata ga wani kyau da ta yi ba da suke faman zuzutuwa. Yanda Tahir ke zillewa yasa ta maida hankali gareshi.
  "Oh  Allah, Anti bari mu dan bar wajennan ko zai nutsu."
  Amina ta maida dubanta ga abinda akeyi.
"Jeki ina nan kallo bazai wuceni ba tunda ke kam bakya jin shawara."
  Da murmushi saman fuskar Ummi, ta yi gaba ta kyaleta. 
   Can wajen(garden) ta nufa tana faman jijjigashi, har lokacin bai gama rufe baki ba, zama ta yi a daya daga cikin kujerun dake a lambun. 
"Oh Tahir, don Allah ka yi shiru kaga kallo ya barni saboda kai ko?"
   Kamar ya ji abinda ta ce, ya hau kallonta yana faman sheshsheka irin na wanda yaci kuka, ganin haka yasa ta nufi hanyar dakunansu don 6ulla zuwa kicin ba shi ruwa. 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

43
   Yana daga samansa yana dubansu da murmushi, ya karasa ga Adnan wanda bayan karin safe ya yi wanka ya cigaba da bacci ya kai mishi duka.
"Tashi kaga wani abu." Adnan ya mike da sauri yana dubansa ido waje.
"Sun iso?"
  Faruk na murmushi ya ja hannunsa zuwa barandar. Ihu ya saki wandq har saida su Mami da suka riga suka fito suka kallo shi, dariya suka sanya. Da gudu ya fira ya sauka garesu. Shima Faruk ba shi da za6in da ya wuce na bin bayansa. 
Chapter 30 · 0% Book details