Sashe 10
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Haka rayuwa tayita tafiyarwa Ummi, yau dadi gobe babu dadi. Yawanci matsalarta bai wuce Ihsan ba don Mami matukar zata yi abinda ta sanyata to fa babu ruwanta da harkarta. A wannan halin ne wata ranar Asabar ta tashi da ciwon mara marar misali, tun tana dauriya har ta kasa, ko tashi ta kasa yi balle ta kai ga aikace-aikacenta. A wannan hali Ramma tayi sallama ta shigo bisa umarnin Mami da ta dubo ko lafiya bata fito ba har ga Ramma ta rigata zuwa.
Ganinta ba lafiya yasa ta fita ta sanarwa Mami. Kafin su dawo ta soma jin ta da lema, saida Ramma ta d'agata ne suka fahimci abinda ke faruwa. Ramma ta taimaka mata bayan ta kar6o (Always) wajen Mami, ta gwada mata yanda zatayi, saida ta kimtsa sannan suka rankaya kemis da Ramma.
Tun daga wannan ranar Ummi ta fahimci girma ya hau ta, Ramma ta k'ara jaddada mata hakkokin da suke akanta yanzun wadanda ta riga ta sani don a makaranta duk ana koyardasu.
Mami bata yarda da kazantar kunzugu ba, hakan yasa ta bata (pads) cikin na Ihsan wacce ta rigata somawa tuni. Saida tayi kwanaki hud'u sannan tayi wankan tsarki. Daga wannan lokacin ta k'ara kame kanta ta zama mai kula sosai da takatsantsan musamman ma ga sallolinta.
☆☆☆
A KWANA A TASHI...!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
12
Daga haka bata da masaniyar abinda ya karu don kuwa tuni sun bar wajen sun sauka da niyyar dauko sauran kayan. Larai ta taimaka musu itama. Haka sukayita zirga-zirga, bayan sun kammala kawowa, suna shirin tafiya, Hajiya Mama tayi musu magana.
"Yauwa Amina sauranku lemu da ruwa ko?"
"Toh." Amina ta amsa.
"Muje." Cewar Amina tana duban Ummi wacce ke tsaye. Suka nufi falon kasa, suna jin sadda Hajiya Fatima ke tambayar Inna ko Ummi sabuwar yar aikinta ce. Inna ta amsa da aa, Hajiya Mama ta sanarmata a wajen Mami take. Nan fa Alhaji ya hau fadan yawan chanje-chanjen masu aiki da takeyi. Daga haka basu kara jin tattaunawar ba suka yo k'asa suna dariya don abin ma dariya ya basu. Amina ta dubeta.
"Kinsan wani abu kuwa? Duk fa abin su Mami, suna gudun abinda zai 6ata ran iyayensu, duk abinda suka ce suyi basa musawa shikenan ta zauna. Wallahi suna burgeni yanda suke kaunar iyayensu." Ta karashe lokacin da take kokarin bude firij.
Ummi tana murmushi tace
"Toh Anti ai sune abin alfaharin, idan baka da mai maka fad'a ina wani jin dadi a rayuwa?"
Amina ta jinjina kai sadda ta soma ciro lemuka tana dorawa a saman firjin.
"Gaskiyane kam, mik'o tire a kicin mu dora."
Larai ta tambaya ta mikamata, ta goge sannan ta koma suka dora akai, wannan karon Ummi ce a gaba tana biye da ita, saida suka zo daidai dan korido wanda daga shi sai kofar shiga, ta ja baya ta marairaice.
"Don Allah Anti shiga gaba."
Abin sai ma ya bawa Amina dariya, babu musu ta shiga gaba da sallama sannan itama Ummin ta bi bayanta. Ido hud'u tayi da wannan matashin na dazu, ya tamke fuska ya kauda kai, hakan da ta gani yasa itama dauke nata idanun da sauri ta cigaba da tafiya a tsanake, tuni sun soma zubawa, har Hajiya Fatima na yiwa wani cikin matasan fada akan bayason cin abinci alokacin da kowa yake ci, wanda akeyi domin shi murmushi kawai yakeyi.
"Shiyasa fa bana sonshi, wannan idan mukayi aure mai yiwuwa nima haka zai dunga hora ni da yunwa, barni dai na lalla6a da Gadanga." Cewar Inna kenan, aka sanya dariya gaba d'aya.
"Kai tsohuwa, dad'ina dake kenan. Ai Faruk banda harkar neman kudi bana jin akwai abinda yasa a gaba, yanzu sai ya juya miki biyar zuwa dubu."
Cewar wani wanda ga dukkan alamu shine babbansu, don fuskarsa kadai ya nuna akwai shekaru.
"Yauwa Usmanu, ashe ka fahimta."
Ummi da Amina tuni suka bar wajen, Amina na rike da Samir d'a awajen Rahila babbar d'iya ga Hajiya Madina.
Haka sukayita zolayarsa ko kusa bai mayar da martani ba, asalima banda murmushi babu abinda yakeyi, idan kuma abin ya wuce murmushi, sai ya dara.
Acan k'asa suma abinci suka ci sukayi nak, bayan sun kammala kuma sukayi zaman hira har zuwa sadda akayi kiran sallar La'asar. Sai lokacin samarin suka sauko, Ummi ta bisu da kallo kamar yanda Amina ta umarceta. Ta kara jaddada mata cikin rad'a-rad'a.
"Kinga na farkon nan mai dan jiki shine babban d'an Hajiya Babba ta Abuja, Yaya Usman yana da matarsa d'aya da yaransu uku, na biyun shine Yaya Faruk, shine autansu baiyi aure ba, na ukun mai farar shadda shine Yaya Ridwan, shima yana da matarsa daya 'yar Ghana ce, yaransu biyu. Na karshen shine Yaya Haidar, shi ake shirye-shiryen bikinsa yanzu tare da Yaya Intisar babbar d'iya ga Hajiya Mama, bikin baifi ragowar sati uku ba."
Wannan dogon bayanin da Amina takeyi, tuni wadanda akeyi don su sun fice saidai Ummi ta fahimta kuma ta gane, kenan dai Yaya Faruk shine wanda ta gani dazu a tsakar gidan yana waya? Ta tambayi kanta kuma ta bawa kanta amsa. Ba karshen dai Adnan ne wanda ba sai an mata bayaninsa ba.
Koda suka idar da sallah, anan suka zauna tsakar gidan suna ta hirarsu har zuwa lokacin da samarin suka dawo suka shiga ciki banda Faruk wanda ya tsaya amsa waya acan farfajiyar gidan.
Kiran da Larai ta kwalawa Amina yasa ta mikewa tana amsawa. Nan ta bar Ummi da Samir yaro mai shiga rai. Wasa ta shiga yi mishi, babu ruwansa sai 6angale dariya yake. Ya shiga jan dankwalin abayarta yana dariya, ta rike hannun.
"A'a Samir, daina."
Maimakon ya daina, saima ya karasa janyewa gaba daya yana ihu da dariya, ta mike da zummar kamoshi, saidai da gudu ya shiga zagaye a wajen. Abin ya bata mamaki da dariya, a garin ta cafkoshi ganin yayi hanyar kofa, ba tsammani tayi karo da mutum har ya kai ga faduwar abin hannunsa.
"Bismillah." Ta fad'a batare da ta shirya ba. Ta dago kai sukayi ido hud'u da Yaya Faruk, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bakinta ya soma rawa saidai ta kasa fidda ko kalma d'aya, tana so ta bashi hakuri amma batasan ya akayi hakan ya kasa fitowa ba, wani kwarjini kawai ta ga yayi mata. Ta durkusa da sauri ta dauki wayarsa da ta tarwatse ta hado mahadinta wato batir da murfi ta mik'a mishi batare da ta mike ba. Sai lokacin ta samu yin magana.
"Don Allah kayi hakuri."
Ta fada cikin sanyin murya. Yasa hannu ya kar6a.
"Is ok." Ok din karshe kawai ta fahimta, ya kad'a kai ya barta anan, ganin haka da sauri ta mike ta bi Samir wanda maigadi ya cicci6o a hanya ganin zai fice, ta kar6eshi ta kuma kar6i dankwalinta ta rufe gashinta.
Ba su suka tashi tafiya ba sai bayan Magriba, anan dinma kamar baza'a tafi ba, don ta jima a tsaye a farfajiyar gidan bayan ta kammala sanyamusu kayayyakinsu a mota tana jiransu. Su dinma ji sukeyi kamar kada su rabu don dadin da gidan yayi musu ganin kowa an had'u. Haka dai suka fito suka fice. Tana jin sadda Ihsan ke rok'on 'yan Abuja akan su kawo musu ziyara kafin su tafi.
"Haba Lil, ai ba saikin rok'a ba." Cewar Yaya Haidar cikin sakin fuska. Daga haka suka rabu, Ummi ta saki ajiyar zuciya ganin sun hau titi don daman gaba daya ta gaji likis har ta ji inama a gidan suka barta bata biyosu ba.
☆★☆★☆★