← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 116

Sashe 37

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

   KB ya ji haushi matuk'a akan abinda Faruk ya yi mishi, kuma ya tabbatar muddin ya ce zaiyi wani yunkurin na daukar fansa, to fa Faruk ba karamin aikinsa bane ya tona mishi asiri. A karshe ma sai ya ga menene abin tayar da jijiyoyin wuya akan wacce yasan ya ketare a komai, saidai ya fahimci tabbas akwai wani abun a zuciyar Faruk akan Ummi. Ya yi murmushi a yayinda ya ke kwance saman kujera da misalin karfe uku na rana.
  'Baka san wacce ta dace da wacce bata dace ba Faruk, duk abina bazan ta6a ajiye 'yar aiki a matsayin matata ba. Zubda aji kawai.'
  Ya ayyana a ransa sannan ya ja tsaki a karshe ya shafi goshinsa wanda ya kumbura ya yi dariyar da shi kadai yasan manufarsa.

Misalin takwas na dare, gidan babu kowa sai kalilan cikin iyaye da kuma yan aiki, sauran duk an tafi raka Amarya Baraka gidan mijinta. Amina na hanyarta ta komawa sashensu bayan ta yi aikin da Hajiya Babba ta sanyata na watsawa gaba daya jikokin nasu ruwa da sanyamusu kayan bacci, ta gyaresu tsaf ta shafa musu hoda sannan ta barsu anan falon k'asa suna kallon(Cartoon), alokacin Faruk ya sauko da zummar neman mai kira mishi Ummi, cikin sa'a ya had'u da ita, ita kanta Amina saida gabanta ya fad'i.
  'Ina Ummi ina wannan babban goron? Tab!' Ta ayyana a ranta, a fili kuwa durkusawa ta yi ta kwashi gaisuwa ya amsa yana mai dubanta.
  "Lafiya, idan kin shiga ki cewa Ummi ta sameni a inda muka had'u jiya."
   Ta amsa da to sannan ta bar wajen, tana shiga ta tarar da ita sai faman danne-danne takeyi a wayar ita Aminan, Amina ta kwace tana jan tsaki.
  "Kefa yanzu sai ki hargitsamin ita, ya kamata ki koyi sarrafa waya sai bala'in son wayar amma babu abinda kika iya ciki."
  Sukayi dariya, Amina ta bar dariya, fuskarta ya nuna alamun damuwa da kulawa.
   "Ummi ke din kina da babban matsayi gareni wallahi, ina son don Allah ki kula ki kuma dauki dukkan abinda na gayamaki. Nasan tabbas kina son Faruk shima kuma yana sonki , saidai ki dunga tunanin ke wacece ki kama kanki. Yanzu ki tashi ki je yana kiranki, yace ki sameshi a inda ku ka had'u jiya."
   Ummi ta yi dumm ta tabbatar dukkan abinda Amina ta fad'i gaskiya ce, hakazalika kauna ce ta sanya ta kwa6arta. Ta jinjina kai tare da yin murmushi.
  "In sha Allah Anti zan yi aiki da shawararki. Daman nima ina tsoron shiga kowace matsala adalilin Yaya Faruk."
  Amina ta yi murmushin jin dadin irin wannan matsayin da ta samu wajen Ummi wacce a shekaru bai fi biyu ko daya ta bata ba. 
  "Nagode Kanwata, sai kin dawo."
Daga haka Ummi ta zura hijabinta ta fita bayan ta duba babu wanda ya ganta. Kai tsaye wajen (swimming pool) na gidan ta nufa ta murda kofar ta shiga. 
   Zaune ta sameshi yana waya, ya juyo yana dubanta yana cigaba da wayar, alama ya yi mata ds ta rufe kofar, hakan yasa ta juyawa gami da rufewa, itama zata fi son hakan kada wani ya iskesu tare. 
   Tana kokarin durkusawa ya ja hijabinta hakan yasa ta dubansa.
  Da ido ya yi mata alama da ta zauna gefensa akan daya kujerar. Ta numfasa gabanta na dukan tara-tara ta zauna. Ko kamshin turaren Faruk ta ji, takan ji sauyi a jini da tsokarta, ballantana akai ga jin muryarsa da kuma kallonsa. 
     Tunda ta zauna bata dubeshi ba, shine ma ya karkato yana amsa waya yana karewa fuskarta kallo. Ga dukkan alamu da ogansa awajen aiki ya ke magana, ganin yanda ya ke bawa mutumin girma hakazalika batu ne na kudade da wasu takardu sukeyi. Maganarsa tafi yawa da harshen turanci.  A jikinta ta ji yana kallonta, ta dan juyo ta saci kallonsa, ya kuwa kafeta da ido kafafunsa saman kujerar ya tankwashesu. Ta kauda kanta ta yi shiru, ji ta ke tamkar ba zata iya rabuwa da Faruk ba, saidai hakan dole ne agareta, ko ta karfi ko kuma ta lumana. Ta karfin kuwa, daga yan uwa da danginsa ne, wadanda a karshe zasu ci zarafinta su korata kauyensu, ta lumanar kuwa shine ta bi shawarar Antinta wanda idan har ta kiyaye to fa baza'a kai ga sauran matakan ba masu ciwo. Saida ya kammala wayar sannan ya ce.
  "Bari kiga na kashe wayoyinnan, ko waye zai k'ara nemana saidai ya hakura na kammala da iyalina ko?"
  Kanta ya yi dumm, jin kowanne kalamansa ta ke yi tamkar sun fi gwal da daham tsada a wajenta. Da a bata komai na jin dadin rayuwa ta gwammace a mallakamata Faruk a matsayin mijinta, saidai me? Wutsiyar rak'umi ta yi nesa da k'asa.
Tunaninta ya katse sa'ilin da ya dora wayoyinsa a saman cinyarta. Ta dago ta dan dubeshi fuskarsa babu alamun wasa hakan yasa ta maida kanta ga duban wayoyinsa biyu manya wadanda ta tabbatar masu tsada ne saidai hankalinta yafi karkata ga son son jin abinda zai fito daga bakinshi.
   DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  53
   Washegari kuwa tun safe mutane suka soma tafiya, yan Adamawa kaf dinsu suka fice, Gwaggo surukar Mami bata zo wannan karon ba saidai ta aikowa Mami tsaraba hakanan ta aikowa Hajiya Babba g2udunmuwa. 
     Sai bayan Azahar su Mami suka soma shirin tafiya. Ummi suma sun kammala hada komai nasu ta tsinci sak'on kira daga Mami. Mamin na daki daga ita sai Ihsan wacce jin cewar zata karasa hutunta a gidan su Faruk ya sanyata kasa rufe baki don tsabar farinciki. A haka Ummi ta shiga ta riskesu, Mamin na faman kimtsawa don tafiya. 
   Bayan an gaisa ta ce. "Gani Mami."
Mami ta dubeta.
   "Yauwa Ummi, anan za ki zauna har muga abinda hali ya yi, saidai bayan komawata tukunna."
  'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Shine abinda Ummi ke ambata a can kasan ranta, ta ya ya zaayi a barta a gidan su Faruk, ina laifin ma idan sun je Kano ta je koda gidan su Hajiya Mama ne ko gidan su Inna?
  'Ai ba danginki bane.' Cewar wani sashen zuciyarta. Ta ji babu yanda ta iya don yan uwannata basu ma damu da sha'aninta ba. 
   "Wai bakya ji ne wani sabon wulakanci ana ta yi ma ki magana kin yiwa mutane banza kamar tsararki?"
  Maganar Ihsan kenan wacce ta maidota hayyacinta batare da shiri ba.  Ta dubi Ihsan din wacce a take ta watso mata harara kamar idanunta zasu zazzago, gaba daya bakin cikin jin cewa har Ummi itama anan zata zauna ta ke, kamar ta shak'eta haka ta ke ji, tsaki ta ja ma a karshe ta fice daga dakin cikin kunar rai. 
    Ummi ta maida hankalinta ga Mami.

"Toh Mami. Allah Ya kaiku lafiya, Ya gyara lamura."
    Har cikin ran Mami ta ji dadin addu'ar.
   "Amin. Kina iya tafiya."
  Ta mike jikinta babu kwari ta fita, tana zuwa dakinsu ta fad'a saman katifa ta yi tagumi. Haka Amina wacce ta fita kai kaya mota ta shigo ta risketa.
  "Aa ya ki ka zauna, yanzu fa zasu fito."
  A sanyaye ta dubeta ta sanarmata yanda Mamin ta ce. Amina ta numfasa.
  "Allah Ya sa alheri ne ya tsayar da ke Ummi. Nidai fatana ki kiyaye dukkan nasihuna gareki, ban zama mai cutarwa gareki ba."
   Ummi ta yi yak'e tana duban Amina.
"Wallahi Anti babban ma fargabata bai wuce Ihsan ba, na tabbatar zan sha wulakanci daga gareta."
  Amina ta girgiza kai da dan murmushi saman fuskarta wanda na yak'e ne.
  "Karki damu Ummi, Allah Yana tare da ke. Kedai kiyi takatsantsan da lamura, bari naje kada su Hajiya Mama su rigani fitowa."
     Ummi ta mike sanye gami da zura hijabinta a saman riga da siket na koriyar atamfa ta bi bayanta. 
     A fusace ta shiga dakin babu ko sallama, hakan yasa su Ikram, Intisar harma Anti Aisha da Rahila dubanta.
  "Ke lafiyarki kuwa? Ku ganemin yarinya kamar mai iskokai yanzu kika fita kina murnar za'a barki garin masoyinki, kin shigo kuma kina fushi, meyafaru?" Cewar Rahila kenan.
   Ihsan ta zauna gefen gado inda Aisha ke sanyawa Tahir famfas ta ja tsaki.
"Wai don Allah meyasa Mami ta ke yin haka ne? Ya zaayi don nima zan zauna anan ace itama Ummi nan zata zauna? Wannan abun ya isheni, Mami bata da masaniyar yanda na tsani yarinyarnan wallahi da bata soma cewa ta zauna inda nake ba."
   Mamaki ya bayyana a fuskokinsu.
"Sannu sarauniyar wauta, sai akace zamanku a rumfa daya yana nufin matsayinku daya? Kai wallahi har gobe banga randa kuruciya zata fita kanki ba Ihsan."
  Fadin Rahila kenan kafin ta fice daga dakin rataye da jakar kayanta.
   Dariya sauran suka sanya, Intisar ta ja rigar Ihsan kadan.
  "Kina bani mamaki, kodai kishi kikeyi don Ummi ta fiki kyau ne? Wannan tsana haka?"
  Ihsan ta yamutsa fuska, kusan ma har da hakan saidai ita kanta tasan da abu k'alilan zata fi Ummi, shi dinma wuyarta Ummin ta samu hutu kamar yanda ta ke samu. Saidai kuma ta fusata sosai da zancen Intisar. Ta mike a fusace ta fita suna mata dariya wanda hakan ba karamin k'ara rura wutar kiyayyar Ummi ya yi a ranta ba.
Chapter 37 · 0% Book details