Sashe 54
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ummi " Ya kira sunanta wanda ya yi sanadin katsewar aikinta da baya sauri don kusan rabinsa tunani ne ja gaba da zubda hawaye. Ta d'ago a sanyaye ta dubeshi, ya zauna gefenta duk jikinsa a sanyaye, ganin haka yasa ta yi kokarin maida kanta ga aikinta, saidai bai bata dama ba don kuwa da sauri yasa hannu ya taro ha6anta. Gefen fuskarta na hagu ya zubawa ido ganin yanda shatin yatsu ya fito 6aro-6aro, hakazalika wajen ya yi jawur, ya dubi tsakar idaninta da nasa idanun wadanda har sun soma kad'awa don 6acin rai.
"Wa ya mareki?" Shi ne tambayar da ya jefamata cikin kakkausar murya. Ta girgiza kai tana sheshshek'a.
"I'm asking you, who slap you?!!"
Ya yi maganar cikin tsawa batare da ya ko tuna cewar wacce ya ke yiwa bata jin yaren ba. Ta runtse ido don a zatonta ma duka zai kawomata.
"Ka yi hakuri don Allah."
Ta yi maganar cikin muryar kuka, ya sauke hannunsa gami da yamutsa sumar kansa idanunsa a runtse, baya son jin kukanta ko kadan. A tausashe ya kara fadin.
"Naji, gayamin wa ya mareki?"
Ina, ba fa zata fad'a ba, batason tashin hankali ya k'aru a gidan sanadiyyarta.
"Idan kana kaunar Allah da Manzonsa (S.a.w) abar maganar, ni ba wanda ya mareni ma."
Yanda ta ke maganar gwanin ban tausayi yasa shi saukowa.
"Shikenan tunda kin 6oyemin, share hawayen fuskarki."
Ba musu ta sa hannu ta sharesu.
"Meyasa ba ki sanardani yau ake shirin tura ki Kano ba?"
Ta sunkuyar da kanta, dagaske ba kaunar Kanon nan take ba don ta tsorata da kalaman Ihsan.
"Kin dauka bazan sani ba? To babu inda za ki k'ara takawa da sunan aikatau in sha Allah, idan kinga kin bar nan to fa sai da niyyar tafiya gidanku."
Jin haka yasa ta dubansa, ya gyada mata kai.
"Dagaske."
Kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa, ta tuna Ihsan da alwashin da ta ci akanta, kenan dai Allah Ya yi nufin ku6utar da ita?
"Tunanin me kike? Kin ma karya kuwa?"
Kai ta gyada.
"To yanzu wannan ruwan da ki ke faman tsoma yatsunki ciki, zai iya sanyaki mura, kinga tashi mu shiga ciki. Bala!"
Ya juya ya soma kwalawa mai kula da shukoki kira, mintuna k'alilan sai ga Bala ya iso, ya russina a ladabce.
"Ranka ya dad'e."
"Matse ka shanya wadannan."
"To."
Ya dubi Ummi da wani kallo wanda ta kasa jurewa.
"Muje ko?"
Ta kauda kanta ta soma tafiya. Bala ya soma wanki yana binsu da kallo cike da tunane-tunane a ransa da kuma mamaki, to me ya had'a kashi da fura?
"Ikon Allah." Ya fad'a a fili sannan ya cigaba da abinda ke gabansa.
*** *** ***
KANO
Ta kama baki cike da mamaki sadda ta ke fitowa daga d'aki sai kuma ta saki fuska tana 'yar dariya-dariya.
"Ikon Allah, ashe dai yaronnan da gaske ya ke, to, halan dai yau 6atan kai kikayi?"
Hajiya Mama ta ja guntun tsaki tana dariya alokacin da ta cire takalmanta ta k'arasa har falon Mami na biyu tana fadin.
"Jimin ke da wata magana? Sai kace wacce ta kwashi shekaru bata lek'o ba."
"Aa, ba zancen shekaru, saidai idan ban manta ba rabon da ki zo gidannan tun kafin bikin Baraka, saidai fa a waya ko kuma idan na je."
Ta dan dara.
"To naji marar mantuwa, ai gani yau na lek'o."
Mami ta zauna tana dariya.
"Na ganki kam."
Hajiya Mama ta bi Mami da kallo cikin shak'iyanci ta ce.
"To wannan k'ibar kuma fa? Anya Fahad bai kusa samun k'anwa ko k'ani ba?"
"Um, haka fa shima Abbannasu ke fad'i, wai duk na chanja kodai juna biyu gareni."
Hajiya Mama ta gyada kai.
"Da alamu dai wallahi, amman ki je asibiti ki ji tunda ba kiyi girman da za ki tantance ko kina da ciki ko babu ba."
Ta k'arashe tana 'yar harararta, sai ma ta bawa Mamin dariya, suka dara. Sun dan ta6a hira sai kuma Mamin ke sanarmata cewar yau Ihsan zata dawo tare da Ummi. Alokacin ne Hajiya Mama ta taso da maganar da ya kawota.
"Ke, ni wata magana ma na zo miki da shi, aikoni Hajiya Babba ta yi wajenki."
Cikin rashin fahimta Mami ta ce.
"Toooh, meyafaru? Ba dai wani abun na rashin d'a'a Ihsan ta yi musu acan ba."
Hajiya Mama ta ja tsaki tana mai kokarin cire mayafi.
"Kinji wata maganar kuma, to idan hakanne ai bata wuce Hajiyar da kanta ta lallasata ba, wa zai tsaya wani kawo miki k'ara?"
Murmushi Mamin ta yi, tasan hakanne don ko kusa Hajiya Babba bata fiye daukar raini ba ba dai kamar Hajiya Mamar, wacce ita sha yanzu magani yanzu ce duk kuwa da cewar tana da mutunci kwarai.
"Abinda ya ke faruwa shine..." Ta kwashe bayanin cikin hikima ta gayamata. Mami tunda aka ambaci Ummi aka jogana da Faruk ta daure fuskarta tamau, duk da Hajiya Mama ta lura da hakan, bata fasa cigaba da bayaninta ba saima kauda fuska da ta yi daga dubanta har ta kawo karshe da fadin.
"Kinsan dai Yaya Fatima awajenmu da kuma yanda muka dauketa, ba zata so abinda zai ta6amu ba, nikam ban ga wani aibu a yin haka ba, duk da kema nasan babu wani abu da..."
"A ina? Bazai yiwu ba wallahi. Haba Hajiya Mama, ban ta6a zaton zakuyimin haka ba, da ace ba ciki daya muka fito ba zan iya kiran haka da 'YAN UBANCI! Abin kunya abin turr ace keda Hajiya Babba jinina, ku ne kuka amincewa Faruk had'a Ihsan kishi da 'YAR AIKI? Ko don Ihsan ba ku ku ka haifeta ba? Wannan wane irin magana ce haka kika zo da ita?"
Maganar ta ke yi a matukar fusata, idanunta ya rufe akan makahon son da ta ke yiwa d'iyartata wacce ita ta kasance mace d'aya tilo awajenta, wacce ta ci burika akanta da kuma ranar aurenta, ta ya ya tashi guda zaayi tunanin had'ata kishi da wacce bata isa ba? Lallai acewarta wannan tsagwaron cin amana ne da yan uwanta sukayi gareta.
"Kina da hankali kuwa Madina? Yau ni Sadiya ki ke yiwa haka? Anya kina cikin hankalinki?"
Ta dubi Hajiya Mama da idanunta wadanda suka cika da 6acin rai.
"Ina cikin hayyacina wallahi, amman tabbas idan magana ce ta gaskiya wannan rashin kyautawa ne, Hajiya Babba ta nuna kaunar nata a fili."
"Wallahi Madina kin ban mamaki, ashe haka kike?!! Ashe son diyarki zai iya chanjaki bansani ba? Aure ba kaddara bace? To wallahi bar ganin ana lalla6aki, ba fa tsoronki mukeji ba don ba kece sama da mu ba, aurene kuma yanda Hajiya ta fada hakan zaayi idan Allah Yaso, idan kin isa saiki hana!"
"Ayi, amman ba dai da diyata ba, har abada ba zata yi zaman kishi da Ummi ba, abu ne da Ihsan ba zata ta6a aminta ba, ni na haifeta kuma nasan halinta, bazata ta6a son haka ba. Idan dagaske kaddarar ne, meyasa bai fad'o kan diyarki ba..."
Bata kai ga karasawa ba adalilin marin da ta dauketa da shi.
"Bansan ba ki da kunya ba sai yau, kuma wallahil azim muddin ina raye idan Allah Ya kaddaro babu mahalukin da zai hana auran Ummi da Faruk. Kina nan kuma itama 'yar taki tana nan tana gani za'ayi, ta je kada ki barta ta yi kishi da 'yar aikin da kike ikrari, akwai mazajen 'ya'yan masu kudi da mulki, kina iya had'ata kishi da su. Sannan ina mai tabbatar miki Madina, akwai ranar k'in dillanci, sai kinyi dana sanin wannan abu da kikayi, sai kinji kunyar kanki Madina."
Daga haka Hajiya Mama ta dauki jakarta da mayafi ta kama hanya tana zubda hawaye, a haka ta shuri takalmanta har tana had'a hanya.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR