← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 116

Sashe 115

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Sannu Anti, ko za ki sanarwa Yaya?"
Ummi ta girgiza kai tana dan yamutse fuska.
"Kayya, barshi, nasan yanzu yana tare da su Hajiya, in sha Allah idan na samu  na dan runtsa zai bari."
  Ta gyada kai.
"Allah Ya baki lafiya." Ta lumshe idanu tana mai amsawa, bayan fitar Batula daga bacci ya dan fisgeta sai ciwo ya motsa ta farka, lokacin karfe biyar na yamma, can dai ta ji ciwo ya motsa babu kakkautawa, firgigit ta mike zaune tana ambaton sunan Allah gami da rike cikin. 
   Ta kasa jurewa ta sauko kasa bayan ta dafe gadon da hannunta na dama. 
  "Wayyo Allah."
  Ya yi daidai da shigowar kiran Faruk wanda ta sanyawa sauti na daban, ta daure ta kai hannu saman dirowarta ta dauka gami da sanyawa a kunnenta. 
   "Ummina kina lafiya?"
"FAR HAS zan mutu..."
Ta fada cikin rawar murya wacce ke nuni da jigata. 
  "What?! Nakudar ce?!!!"
Ina! Tuni ta ajiye wayar sakamakon murdawar da cikinta ya k'ara yi. 
   A wannan yanayin Batula ta iso domin ta lek'ata ko ta samu baccin, gaba daya ta diririce ta hau salati, ganin yanda Ummin ta ke ba'a hayyaci ba kawai sai ta soma kuka don ta rasa taimakon da zata bata. Dabarar kiran direba ne ya fadomata, a guje ta fita tana kiransa. 
  "Malam Musa! Malam Musa!!"
Da sauri suka shigo gidan har maigadi kasancewar suna waje saman benci suna hira.
"Lafiya?" Suka fada har suna rige-rige. 
  Ta nuna hanyar gidan dakyar ta iya magana.
  "Anti..Anti zata mutu."
Ai da gudu suka nufi ciki, saidai kafin su karasa ciki suka ji ana doka mahaukacin hon, da gudu kuma suka fito, har suka ci karo da Faruk wanda ya bar motar waje ya shigo Hajiya Babba da Dakta na mara mishi baya. 
  Suna shiga suka tarar tana ta fama, da sauri ya riketa.
"Sannu Ummina."
Ya dauketa cak ya nufi waje, lokacin har maigadi ya bude kofar. Suka sanyata a mota sai asibiti. 
  Shima Haidar wanda isowarsa kenan tare da Intisar suma har da su a gidan sadda Ummi suka yi waya da Faruk, suka bi bayansu zuwa asibitin. 
   Dakta Ridwan wanda tun a mota ya yi kiran wayar abokiyar aikinsa Dakta Farha, ita ta kar6i Ummi suka shiga dakin haihuwa. 
   Suna nan tsaye suna faman adduoi, Faruk ya kasa mance furucinta na ambaton mutuwa da ta yi gareshi, ya runtse idanu ya budesu, tuni suka kada zuwa ja. Hajiya ta umarci Intisar da ta koma ta dauko akwatin Ummi na kayan haihuwa, Haidar ne ya jata suka koma. 
   Mintuna talatin da shigar da Ummi, lokacin an soma kiraye-kirayen sallar Magriba har Intisar sun dawo, kukan jariri ya cika kunnuwansu, suna cikin wannan farin cikin, suka kara jin wani kukan. Fitowar Dakta Farha ne yasa su maida hankali gareta.  
  "Alhamdulillah, ta sauka lafiya ta haifi...." Sai kuma ta sanya dariya lokacin da ta kar6i akwatin kaya tana mai mikawa nos din gefenta dake dariya, nos din ta yi ciki. Su kuwa duk sun k'agu da son jin abinda zai fito bakinta. 
  "Me ta haifa?"
Cewar Haidar. 
Dakta Ridwan wanda ya riga yasan manufarta ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo dari biyar ya mik'amata yana dariya.
   "Ga abinda ki ke jira." Ta kar6a suka yi dariya, Faruk ji ya ke kamar ya tura kansa dakin. 
   "Na kar6a amman ya yi kadan kaima ka sani, ta samu twins mace da namiji."
  Ai Haidar da Faruk tuni suka rungume juna suna dariya, Hajiya murmushi kawai ta ke yi tsabar farinciki ta rasa inda zata saka ranta, wai Sadaukinta ne da d'a, har biyu ma, kyautar Allah. Hawayen farinciki ya tahomata ta yi saurin daukewa da hannu.
  "Dakta jikin Ummi fa?" Cewar Faruk.
"Alhamdulillah, babu wata matsala."
  Ta koma ciki, nan fa suka shiga kiran abokan arziki suna sanarmusu. Ihsan saida ta ji kamar ta budi ido ta ganta a Abuja tsabar murna don yanzu sosai su ke dasawa da Ummi saika rantse wani abu  bai ta6a giftawa tsakaninsu ba. 
   Bayan an gama gyara yaran wadanda sak kamannin mahaifinsu suka dauko, aka miko musu.  
  "Masha Allah." Cewar Dakta Ridwan wanda ke rike da macen yayinda Haidar ya matsa ga Hajiya yana kallon namijin. Faruk ya kuramusu idanu yana kallo cike da sha'awa da tsananin so da kauna, burinsa ya yi tozali da Umminsa wacce ta haifa mishi wadannan kyawawan halittar abin so da kauna. 
    Koda suka shiga, kasa daga idanu ta yi ta dubesu haka kawai ta ji tana kunya musamman ma ganin har Hajiya Babba aka zo. 
   "Madam sannu, kin kawowa Hajiya miji, Daddy kuma mata ko?"
Cewar Haidar, akayi dariya.
Faruk dake rungume da macen ya saci kallon Ummi saidai bata ko kallo inda ya ke ba, murmushi ya yi yana ji kamar ya hadasu duka ya rungumesu. 
  Ko awa uku ba'a cika ba, su Baraka da Jidda duk aka iso har babban Yaya. 
   Haka suka cika daki mai lamba hudu wanda aka bawa Ummi don ta huta. Faruk da kansa ya kira Gombe ya sanarwa Malam Balarabe da Gidado,  wannan abu ba karamin dadi ya yi musu ba. Dada ta hau shirin tahowa Abuja don daman ta ce ita da zuwa Abuja sai idan Ummi ta haihu. 
  Ana gobe suna yan uwa duk suka zo har mutan Kano da Gombe, Amina ta so zuwa saidai babu dama don ita kanta tana fama da jikinta, Binta itama ta yi farinciki sosai don itama ga kusa aure lokacin. 
    Yara suka ci suna Afra da Afreen, da yawa tsoffin suka kasa maimaitawa. 
  "Dan nema, za ka zo ka sameni, idan ba mugunta ba mene na saka sunan da bamu iya fad'i ba sai kace sunan aljanu?" Cewar Hajja kenan lokacin da sukayi waya da Faruk, banda dariya, babu abinda Faruk ya yi. A karshe suka gaisa da Modibbo wanda ke kwance ba lafiya har lokacin. Dakyar ya amsa wayar kafin su yi sallama. 
   Sati biyu da haihuwar Ummi, Dada ce awajenta tana kula da ita, alokacin ne kuma aka soma bikin Ikram da Gidado wanda babu abinda Ummi ta halarta a ciki bisa umarnin Faruk, acewarsa yaushe ma ta haihu da zata soma fita? 
   Haka aka yi biki aka k'are, Ihsan itama ta zo daga Adamawa anan gidan Ummi ta yada zango, sosai Ummi ta ji dadi, tsakanin Ihsan da Faruk zumunci na yan uwantaka ke wanzuwa ba kamar a baya ba da ya ke daddauremata, hatta Badiyya kishiyarta ta zo wannan karon. 
  Haka aka kammala bikin Ikram aka mik'ata Jar Kwami, gidan da Gidado ya gyarashi kaika rantse cikin birnin Gombe ne don daman ko kadan basu da matsalar wutar nema. To me zai dameta tana tare da masoyinta?
  Bayan Ummi ta yi arba'in babu inda kafarta bai taka ba itace har Gombe, a wannan lokacin ne kuma Faruk ya biyamusu Umarah, har hawaye ta yi don tsabar farinciki.
                  ***    ***    ***
           BAYAN SHEKARU UKU
                     DAN ADAM
Chapter 115 · 0% Book details