Sashe 50
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Ummi kuwa tana shiga daki ta tarar Binta na zaman jira. Binta na ganinta ta mike ganin yanda jikinta ya ke duk a sanyaye.
"Lafiya?" Ba ta ce uffan ba, sai kayan da ta ajiye saman katifa ta zauna, batasan lokacin da kuka ya kufcemata ba. Binta wacce ta sandare tana kallon waya hankalinta ya komo ga Ummi.
"Me ya faru wai? Ki gayamin don Allah mana."
Ita dai Ummi kukanta ta ke, ji takeyi inama yau ace mahaifiyarta na raye, ta rungumeta ta rarrasheta ta kuma bata shawarar da zai taimaki rayuwarta.
"Allah Ya ji k'an ki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki, na taso ban ta6a jin dumin uwa ba, na taso cikin wahala da tsanani na rayuwa har zuwa sadda aka maidani 'yar aiki. Babu wani mahalukin da ya ta6a rungumeni ya ji matsalata ya rarrasheni ya min addua acikin shak'ik'aina, Babana bai ta6a tarana ya yimin fad'a akan rayuwa ba, ko sau daya bai ta6a sakarmin fuska ba, asalima kyamata yakeyi, bai ta6a tambayar Ummi ko kin ci abinci ba, Ummi zan saki makaranta, Ummi ki kula da kanki, Ummi ki tsare mutuncinki, ko sau daya babu wani cikin yan uwana da suka ta6a nunamin kulawa ko k'auna. Babu, babu su Ummana, Ummana nasan da kina raye da wasu lamuran zasuyi sauk'i agareni, ayau ga wata rana babba da nake bukatarki Ummana, saidai kinmin nisan da bazan iya kamoki ba, kin koma ga Ubangijinmu da ya fini kaunarki, babu wani da ya ta6a ban cikakken tarihinki da kyawawan dabi'unki, asalima saidai ayita aibatamin ke, ana miki kazafi. Nayi rashinki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki."
Daga haka ta k'ara sautin kuka mai tsanani, ta cukuikuiye jikinta wuri guda, a rayuwa koda a gaba wata sila tasa Antinta Amina da yar uwansu juyamata baya, koda shima Faruk zai juyamata, bazata ta6a mance da tarin kaunar da suka nunamata ba. Sun nunamata itama DAN ADAM ce. Faruk ya gwada mata cewar itama ta cancanci komai a rayuwa, ya dauketa a mutum, haka nan danginsu gaba daya, banda matsala ta Ihsan da kishiyar Mami, babu wani abu da ta ta6a fuskanta na cin zarafi cikin zuri'arsu. Watakil a gobe zama da su zai k'are. Ta daga kai tana mai duban dakin, sheshshekar kukan da ta ji ne ya tunasar da ita cewar bafa ita daya bace a dakin. Ta kai duba ga Binta, kuka takeyi kwarai. Ta share hawayenta tana mai dukar da kanta k'as.
"Meyafaru Binta?"
Binta wacce zuciyarta ta cika da dumbin tausayinta ta dago kai tana dubanta.
"Shakka babu ke abar a tausayawa ce Ummi, saidai ki yi hakuri, komai na rayuwa mai wucewa ne, babu abinda ya ke dauwamamme a duniya. Wataran sai labari, Ummi akwai wadanda idan kika ji matsalarsu sai ki gane naki ba komai bane, za ki gane ke lallai kina cikin rufin asiri, ina wadanda suke kare rayuwarsu a wahala babu ko digon jin dadin rayuwa? Ummi akwai matsalolin da suka sha gabannaki, wata ma iyayenta na raye uwa da uba, amma bata ji dadinsu ba ko kusa, kuma tana gabannasu. Ina ji a jikina za ki auri Yalla6ai in sha Allahu, kuma za ki ji dadi a rayuwa. Ki cigaba da mik'a lamuranki ga Allah, in sha Allahu zai magance miki. Nima ina so ki sanyani cikin layin masu kaunarki, har abada bazan cutar dake ba, wanda mukayi a baya ma, ina neman afuwarki, ajizanci ne na DAN ADAM."
Ranta ya dan yi sanyi da jin zantukan Binta masu dadi. Haka ta cigaba da yi mata 'yan nasihu da misalai da wandanda suka fita shiga matsala kuma cikin ikon Allah ya wuce kamar baayiba. A karshe Ummi ta labartamata yanda Faruk ya ce na ta shirya gobe zai kaita gaban iyayensa matsayin wacce zai aura.
'Tirk'ashi!' Shine abinda Binta ta fad'i a ranta
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
67