Sashe 79
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
96
"Ina a Tudun Wada?" Cewar matuk'in.
"Bayan gidan Sarki."
Suna tafe Malam Balarabe na nunawa Ummi wurare gaba daya ya kasa ma rufe bakinsa, itama saita tsinci kanta da farinciki, Mariya ma kalle-kallen ta ke yi bakinta washe har suka iso unguwar. Wayar Ummi ta yi k'ara ta amsa. Hajiya Babba ce don kuwa ta yi kiranta kwanakin, suka gaisa kafin ta tambayi ko sun isa, ta amsa mata da eh. Ta ce ta gaishe da mutanen gidan. Daga haka suka yi sallama alokacin da kuma ta ga sun tsaya daidai wani gida karami ya sha fenti ruwan madara, wanda a kusa da shi wani gidan ne shima shigensa don hatta da fentin iri guda ne. Zaune a kofar gidan, wani dattijo ne kishingide saman tabarma, a gefensa kuwa wani ne da bai wuce shekaru hamsin ba suna hira da dariya saidai tsayuwar tasi din a kofar gidannasu yasa hankalinsu ya dan koma gareta.
Jikin Malam Balarabe har rawa ya ke don ko shekaru nawa ya yi ba fa zai mance wadannan fuskokin ba, Haruna yayansa ne sai kuwa Mahaifinsa.
Shima Harunan mik'ewa ya yi da sauri.
"Abdullah!" Jin sunan da ya ambata yasa Dattijo Malam Buba mikewa zaune daga kishingidar da ya yi yana mai gyara zaman gilas dinsa na masu ciwon ido gami da k'urawa wanda aka kira da sunan Abdullah dansa idanu.
Tuni Malam Balarabe ya karaso da sauri suka rungume juna shi da yayannasa. Kawai sai suka fashe da kuka, Ummi ganin haka itama ta soma hawayen tausayamusu. Duk a silar kaddara sun rabu da juna. Ganin mai tasi ya gama sauko kayansu daga boot, ta tambayeshi ko nawa ne kudin sannan ta zaro a jakarta ta biyashi ya wuce.
"Abdullah ashe za mu k'ara sanyaka a idanunmu?" Cewar Harunan kenan cikin zubar hawaye.
Malam Balarabe ya na sharar hawaye ya karasa ga mahaifinsa wanda ya yi shiru yana ta faman jera hamdala a zuciyarsa ganin addu'arsa ta shekara da shekaru ta kar6u a yau. Ya riko hannuwan mahaifinsa shi kuwa Haruna ya nufi wajen su Ummi wadanda ke gaisheshi.
"Malam gani gabanka, ka yankemin dukkan hukuncin da kaga ya dace, na yi babban laifi, na manta da dukkan hakkinku da ya wajaba a kaina na kula da shi, ka gafartamin Malam, na tabbatar har da k'in jin maganarku da na yi na auri son raina."
Malam ya damk'i hannunsa cikin rawar murya ya ke fadin.
"Ba ka da laifi Abdullah, na jima da fahimtar hakan, shiyasa ban ta6a rik'eka ba a raina. Gareni, na yafemaka, tashi mu shiga ciki Abdullah mahaifiyarka ta sanyaka a ido ka nemi gafararta." Da taimakon Malam Balaraben Mahaifinnasa ya mike, suka yi ciki, yana dogara sandarsa.
Ummi wacce Haruna ya gama ja da hira yana fadamata irin matukar kamar da sukayi da mahaifiyarta, itama tasan hakan sakamakon hotonta da mahaifinnata ya bata. Suka mara musu baya suna mai daukar jakankunan wadanda uku ne kacal.
Saida suka shiga ta fahimci ashe dai ginin nada dan girma, irin ginin nan na gidan yawa, yara suka yita binsu da kallo, Abida mata ga Usman wato Baffa ta dubi Haruna bayan shigewar su Malam Balarabe da Malam.
"Waye wannan?"
Yana murmushi mai bayyana hakora ya amsa.
"Har kin mance da Balarabe? Ai shine da iyalinsa."
Ta zaro ido tana mai dafe kirji, yayinda ta ke bin su Ummi da kallo, Ummi ta gaisheta sannan itama Mariya ganin haka ta gaidata.
Dada na zaune a rumfarta tana gyaran wake, tsohuwa mai ran karfe, idan ka ganta ba ka ce yara bakwai sun fito daga jikinta ba don kuwa da kuzarinta.
Ta ajiye waken gefe ta yi sakato tana duban wanda ke rike da mijinta. Ko shekara nawa Malam Balarabe zai yi ita din mahaifiyarsa ce da ba zata ta6a mance fuskarsa ba. Kafin su kai ga karasawa gareta ta mike da sauri ta shige dakinta. Suka karasa suka isketa zaune saman gadonta na karfe tana faman sauke ajiyar zuciya. . Bayan zamansu ne ta dubeshi kamar ta tashi ta makureshi.
"Me ka zo yi mana?! Ka zo ka ga ko mutuwa muka yi ka ci gado ne?!!!"
Tana maganar a zuciye, hakan ya karyawa Malam Balarabe zuciya ya hau zubda ruwan hawaye.
"Haba Fatima, ban sanki da zuciya ba, kada fushi yasa ki aikata abinda za ki nadamarsa nan gaba."
Cewar Malam cikin harshen fulatanci.
"Nadamar..."
Sai kuma ta kasa magana sai kawai ta fashe da kuka sosai don kuwa ita bata ta6a takawa ta je inda suke ba, hakazalika tun zuwan da ya yi sau daya bayan aurensa ya wuce da Hasiya bai k'ara takowa garesu ba don ko mutuwar Hasiya sai Jar Kwami ta je musu gaisuwa. Har da wannan zafin ta ke ji na dumbin shekaru har goma sha takwas da aka kwashe ba tare da ta sanya dannata a ido ba.
Duk iyakar lalla6awa da ban hakuri da Malam da Malam Balarabe suka bata, babu alamar saukowarta haka suka tattara suka fita inda Malam ya ba wa dansa shawara akan ya yi hakuri har ta huce don a yanzun tana cikin zafi ne.
Ko bayan fitarsu, dakin Malam din suka nufa har Haruna don Baffa yaba can kasuwa har lokacin bai dawo ba, nan Malam Balarabe ya yi sallar la'asar sannan ya yi zaman hira da mahaifinsa. Acan suma su Ummi sun samu tarba kwarai daga matan gidan da yan uwansu, daidai da Dada ta ja su jiki musamman Ummi wacce ke tunano mata Hasiya yarinya mai shiga rai da sanin ya kamata don shekaru biyun da ta yi a nan wajensu kafin zuwan mijinta sun saba kwarai da ita.
Haruna ya hau ba shi labarin bayan rabuwa, Malam na sauraronsu, anan ne Malam Balarabe ya dubeshi.
"Ni kuwa Malam ya labarin Kanwata Aisha? Har yanzu suna can Adamawan? Yaranta nawa da Yakubun?"
Shiru ya biyo baya kafin Malam ya yi dauriyar ba shi amsa.
"Sai hakuri Abdullah, Allahn da Ya fimu son Aisha ya kar6i abarsa, yanzun ta shekara da rasuwa."
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun!" Cewar Malam Balarabe kafin ya soma kuka har da sheshsheka, kanwarsa ma ciki daya ta rasu ba tare da ya sanyata a idanu ba? Rabonsa da ita tun kafin tafiyarsa Ringim.
"Addu'a za mu yi mata, ciwon koda ta ke fama da shi har da abin ya gagara Yakubun suka dawo nan tare da ita don ta yi jinya, saidai takan yawaita tambayarka, har Yakubun yaso zuwa wajenka ya kira mata kai amman Allah baiyi ba, har ta rasu. Yaransu uku, babbar wacce ta ci sunan Hasiya, shekarunta sha shida, tana can Jar Kwami hannun Lamido kakanta, Yusuf da Aminatu kuwa suna can Adamawa hannun mahaifiyar ubannasu.
Malam Balarabe ya jima kwarai cikin jimami don kuwa bayan mutuwar Hasiya, wannan ce mutuwa ta biyu da ta girgizashi. Rayuwa kenan.
"Allah Ya ji kan Aishatu, Yasa ta huta. Zuwa jibi sai naje Jar Kwami mu gaisa da su."
"Ku tafi gobe, Manu ya jima yana son ganin jikarsa." Cewar Malam kenan, ya amsa da toh.
Garin ya yiwa Ummi dadi matuka, har hawaye ta yi ganin irin gatanta, ashe daman tana da gata har haka? Kwanon abinci kuwa sai wanda ta za6a ta ke ci, don daga matar Baffa har Halima matar Haruna kowacce saida ta aiko, aka yanka kaji aka soyamusu. Dada sai nan nan take yi da su, acewarta su basu da laifin komai awajenta.......
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Wannan naku ne..
SallyMoh
Sadia maman ashraf
AB Kura
95
Malam Balarabe da Ummi saida suka yi kwanaki uku kafin su bar Ringim zuwa Gombe don kuwa saida aka yi shari'a a babban kotun jaha dake birnin Jigawa a karshe aka yankewa Habiba hukuncin daurin rai da rai. Ita kuwa Saude bayan an tabbatar dagaske ta haukace kai tsaye aka mik'ata asibiti, cikin danginsu babu daya da ya zo banda Malam Yahuza.
A motar suna tafe har Mariya saidai ran kowannensu babu dadi suna cike da tunani, shi Malam Balarabe tunaninsa bai wuce na irin kar6ar da danginsa za su yi gareshi ba sakamakon watsi da su da ya yi, yayinda a 6angaren Ummi ta ke tunanin rayuwa ta DAN ADAM mai cike da kalabule, ga jarabta kala-kala. Shi dan Adam kwata-kwata a rayuwa ba shi da wani jin dadi da hutu face na idan ya kyautata mu'amalarsa da Mahaliccinsa, wannan kadai zai tsira da shi har mutuwarsa. Abin sai godiyar Allah, kaga dai duk mutum mutum ne amman a halayya da dabi'u an bambanta, wani sai ka rikeshi da gaskiya ya ci amanarka, wani sai ka dunga yi mishi kallon mak'iyinka, batare da sanin shi din mai sonka domin Allah bane, DAN ADAM ne zai fidda makudan kudade, ya aikata dukkan wani nau'i na sa6on Allah don kawai ya k'untatawa dan uwansa DAN ADAM rayuwa, haka kawai sai ya tsaneshi, ya hana kansa sukuni idan ya ganshi cikin jin dadin rayuwa batare da shi din ya yi mishi laifin komai ba, dan uwa sai ya cuci dan uwansa, ya kasheshi.
Ta sanya hannu ta share hawayen da suka zubomata tana mai k'ara rungume Mariya wacce ta yi filo da cinyarta tana bacci.
'Ya Allah, mu bayinKa ne masu yawan zunubai, Ya Allah ka gafartamana, Ka barmu kan tafarki na gaskiya. Ya Allah ka sa mufi karfin zuk'atanmu. Mun shaida babu abinda bautawa sai Kai, mun yi imani Annabi Muhammad(s.a.w) ManzonKa ne. Allah Ka jik'an wadanda suka rigamu gidan gaskiya.'
Tana maganar a zuciyarta, sannan ta k'ara goge hawayenta, kwantar da kanta ta yi saman kujera ta lumshe idanu tana tunanin rayuwarta har zuwa yau, tamkar rana makamanciyar yau ba zata zo ba, ranar da komai zai zo karshe.
Haka ta yi ta tunane-tunane har suka iso cikin Gombe bayan sun ci awa kusan biyar akan hanya. Kai tsaye Gombe Motor Park suka shiga sannan kowa ya soma saukowa.
Malam Balarabe ya tarar musu taxi.
"Tudun Wada zaka kaimu."
((Pls manage...dare ya yi sai da safe zan dora in sha Allah))
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Kin cancanta....
Sis Aisha Kalli...Allah Ya bar zumunci duniya da lahira...ameen.
97