← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 116

Sashe 102

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin 6ata wayonki Ihsan, kin kuma bani mamaki sosai wallahi, ban yi zaton a duniya za ki iya zurfafa kiyayya ga DAN ADAM ba. Wannan jahilci zan kirashi ko kuwa dai hauka? Tabbas akwai ban mamaki, na daya, idan a baya hujjarki Ummi 'yar aikin gidanku ce, to yanzun ta tashi daga wannan matakin. Na biyu Ihsan, idan rashin dangi yasa ki ke uzzura rayuwar baiwar Allahn nan, toh fa wallahi a yanzun idan bata nunamiki yawan dangi ba, ba za ki fita ba. Ki ji tsoron Allah Ihsan, yarinyarnan Allah Ya kaddara dole zata shiga cikin zuri'armu, kar kuma ki manta Kawunta (Alhaji Kabiru) aminin kut da kut ne da mahaifinki, kinga kuwa babu, babu ta yanda zaayi ki gujewa auren dan uwanta Abubakar saidai idan Allah Ya kaddara ke da shi ba za ku kasance ma'aurata ba. Ihsan ko Annabinmu sallallahu alaihi wasallam ya hanemu da zurfafa kiyayya har haka, akan wane dalili za ki dasawa zuciyarki muguwar tsanar Ummi? Toh wallahi Ummi 'yar halak ce, ta kuma wuce a kirata da Butulu mai mance halacci, Allah Ya bata baiwa ta hakuri, haba jama'a, ki tuna irin wulakancin da ki ka sha yi mata tun zuwanta gidanku har kawo lokacin da akace ta zama matar Yaya Faruk, ki kuma tuna irin yanda hakan baisa ta rik'emu ba a zuciyarta, asalima har yau bata bar bamu girman da ta ke bamu ba, shi DAN ADAM yana da matsala, ya na manta cewar shima halitta ce mai daraja har kiga wasu lokutan yana wulakanta kansa ta hanyar biyewa sharrin zuciyarsa ya yi ta aikata 6arna alhalin a karon kansa yasan cewa lallai 6arnar ce. Ba ku kadai ba, daidai da su Anti Jidda basu kyautawa kansu ba da a baya suka zagi baiwar Allahn nan suka tsangwameta, Yaya Faruk ya burgeni burgewa da bai fasa ja baya ba har ya kai ga cimma burinsa da taimakon Allah, ya auri Ummi. Idan wannan bai isheki ishara na ai ya kamata ace gujewa Yaya Faruk da ki ka yi ki ka za6i Abubakar kuma ya zo ya kasance jinin wacce ki ke ikrarin kin tsana, ya isheki ishara. Saidai na yi mamaki yau da na saurari maganganun da ke fitowa daga bakinki, anya Ihsan kina da imani kuwa? Toh ko kina da shi ba ya tasiri akan Ummi, ina fatan shiriya gareki, Allah Ya ganardake. Ke kuma."
Ta juya ga Ikram wacce ke faman hawaye ga gumi da ta had'a sakamakon da na sani marar misaltuwa da ya k'ara shigarta gami da kunyar Ummi da ta ke gani kamar tana gabanta, bata mance marin da ta yi mata akan an mareta da tozarcin da ta yi mata cikin shago.
  "Ki zauna nan ta zugaki ta baro ki, kuma kinsan Allah? Inaji a jikina soyayyar Gidado sai ya wahalar da ke kamar..."
  Da sauri Ikram ta toshemata baki da hannu, ta soma girgiza mata kai tana kuka sosai. 
"Don Allah karki yimin baki, ki dubi daraja ta zumuntakarmu Sis."
  Ta sauke hannunta gami da rike kanta tana kuka.
  "Na jima da gane laifina, na jima da neman gafarar Ummi, bana fatan soyayyar da nake ji game da Gidado ta fi yanda nake ji a yanzu, na tabbatar zan iya mutuwa aduk sadda ya k'i aminta da soyayyata, in sha Allah shi ba MIJIN MACE DAYA bane, ku tayani addua."
  Ta kara fashewa da kuka, dan uwa rabin jiki, duk sai ta karyamusu zuciya, Ihsan ji ta ke da ace tana da iko da ta raba Ikram da wannan makahon son, da ta raba zuciyarta da son Abubakar. Hawaye kawai suke yi, Intisar ta daure ta hadiye nata kukan don batason kara karya zuciyarta. Ta dafa kafadarta.
  "Allah Yana tare da ke, mu cigaba da mika kokenmu gareShi, zanyi miki taimako daya, zan samu Ummi da kaina na sanarmata na tabbata ba zata bamu kunya ba, ita zuciyarta ba irin tamu bace, ta fimu hakuri."
  Tana kaiwa nan ta mike jiki ba kwari.
"To tsaida hawayen mana Matar Gidado." 
Cewar Intisar tana riko ha6anta, dariya sukayi banda Ihsan wacce ta kasa gane hakikanin abinda maganganun Intisar suka sanya ta ji.

                   ***   ***   ***
 A gidan Ango da Amaryarsa kuwa, babu abinda sukeyi sai dirzar amarci hankalinsu kwance, kwanaki biyun da suka yi sai bak'i suke samu, a rana ta uku ne suma 'yan Adamawa suka je gidanta, Hajiya Salma tuni ta bi yan Gombe har Abubakar sun koma don shi Alhaji Kabiru kwana biyar ya yi ya juya Adamawa. Basu jima gidanta ba suka wuce su dinma a ranar suka tafi. Gidan ya rage su kadai a koyaushe, babu ranar da basa waya da mahaifinta da su Dada, hakanan Hajiya Babba kullum saita kirata sun gaisa. Hatta su Hajiya Mama da Mami Ummi kiransu ta ke yi hakan ba karamin dadi ya ke musu ba. Tsakaninta da mijinta sai sam barka don kuwa kullum soyayyar junansu k'aruwa ta ke a zukatansu. 
   Haka har suka yi kwanaki shida suna tare, ita kadai ce zaune wajejan karfe uku, Faruk bai jima da cin abincin rana ba ya fita zuwa gaida su Hajiya Babba. Zuwansa na uku kenan tun bayan auren, ta ji ana kwankwasa kofar falon, koda ta bude ta yi mamaki na ganin Husna da kanwarta karama Siyama. Batasan sadda ta daka tsalle ta rungumeta suna dariya ba. Sai bayan sun shiga ciki hira kuma ta 6arke, Husna sai kod'a irin chanjin da ta ga ta yi ta ke, Ummi banda murmushi babu abinda ta ke. Sun jima, ta taimakamata hada abincin dare kafin ta dubeta. 
"To sai wanka ko?" 
Ummi dariya ta yi, ba musu ta fafa wanka, bayan ta fito ta soma shiri suna hira da Husna wacce ke zaune saman gadonta tana kallon hotunan biki gami da yaba irin wankuwar da sukayi harda daukar wanda akayi musu su biyu, can ta dago ganin Ummi na kokarin sanya wata atamfa dinkin riga da zani rafa ta dan harareta. 
  "Kar ki cemin tun zuwanki kwalliyar atamfa da lesuna ki ke yi? Gaskiya yau ki sanya kananun kaya."
  Ummi ta murmusa.
"Ke wallahi don ba ki ga kananun kayan ba ne duk kama jiki sukeyi, kusan iyakar tsawon rayuwata ban ta6a sanya kananun kaya ba banda riga da siket su kuma ba matsastsu ba."
  Husna ta  mike tsaye.
"Shiyasa fa na cewa Amina sai mun dunga sanyaki a aji don duk abin Amina wallahi ta fiki wayewar kai, matsa kiga ina suke na za6o miki? Ai nan gidan mijinki ne ba haramun ki ka aikata ba, ko ba ki ji yanda Anti Jamila Bappa ta group ke yawan magana akai bane? Duk kuma litattafan da na ba ki ai anyi bayaninsu."
  Daga haka ta shiga duba kalolin kayan, kananun kaya ne masu kyau matuka da tsada, wata abokiyar kasuwancin Hajiya Babba ta aikomata na Amarya da kuma kudade wanda ta ce na Ango ne. 
   Wata riga (purple) mai hannun shimi ta dauko da wando bak'i dogo mai kama jiki ta dubi Ummi tana mai mik'amata.
  "Kar6i ki saka wadannan."
Ummi ta zaro ido saidai hararar da ta samu daga wajen Husna yasa ta darawa.
"Wannan kallo sai kace na ce bazan saka ba?"
  "Ki ce din ma mana mugani."
Suka dara kafin ta fita ta bata wuri don ta shirya, tana zaune falo Ummin ta fito.
"Masha Allah!"
Shine furucin da ya fito daga bakin Husna ganin irin kyan da Ummi ta yi. Batasan sadda ta mike tsaye ba, rigar har taso matseta hakanan ta fiddo da halittarta sosai kamar yanda shima wandon ya zauna d'abas a jikinta. Fuskar ta sha kwalliya, ta tufke kitsonta da ribbon sai kuwa dan mayafi na pashmina da ta dan daura akanta da kuma dan kunne fashion mai kyau. 
   "Kai Ummi, kin fito wallahi kamar ba ke ba."
   "Anti Ummi kinyi kyau." Cewar Siyama.
  Ummi ta murmusa kadan tana jan riga.
"Nagode, saidai anya zan iya bari ya ganni haka?"
  Tsaki Husna ta ja don haushi ta dauki mayafinta don daman ita ta ke jira ta fito su yi sallama.
"Matsalarki, wallahi da kinsan waye mijinki da ba ki tsaya wannan kauyencin ba, tuni wata a waje ta yi miki sakiyar da ba ruwa, koda su Fati na kafa miki misali ya isheki, ga ki da dan karen kishi kuma kina ja baya wajen gyara, don Allah Ummi ki k'ara sakin jikinki, wallahi duk abinda ki ka yi ga mijinki ba ki fadi ba. Wallahi mata suna nan suna harin miji irin naki basu samu ba, amman Allah Ya damk'a maki ba don wayonki ba, ki watsar da kunyar komai ki rungumeshi hannu bibbiyu. Shikenan dai ni zan wuce sai munyi magana ta whatsapp."
Ummi cike da jin kwarin gwuiwa ta yi mata rakiya iyakar kofa, daman yanzun kusan ma ta rage kunya-kunyar don salo-salon Faruk kadai ya isa sanyata dainawa domin kuwa shi babu ruwanshi koyaushe janta ya ke yi. 
   Ba shi ya shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i adalilin rakiya da ya yiwa Daddy wani wuri. 
    Tana jin tsayuwar motarsa, ta ruga daki a guje ta kara gyara fuskarta ta fesa turare sannan ta fito ta budemishi kofa, sak ya yi yana dubanta, ta yi kasa da kanta gami da sa hannu ta kar6i ledar hannunsa.
"Sannu da zuwa." Ta fada gami da ba shi hanya. Ya shigo ya tura kofar ya rufe har da mukulli, har lokacin dubanta ya ke yi don ya kasa cewa uffan, ya ja hannunta zuwa falon ta ajiye ledar saman tebur, ya riko kafadunta. 
  "Mamaki fa ya k'i saki na, Ummin Faruk ce kuwa?"
  Ta na murmushi amman ta kasa magana saima ta sa tafin hannu ta rufe fuskarta. Ya janyota jikinsa.
"Kinyi kyau fiye da zatonki, ina kara sonki Ummina, ki dunga yimin irin shigarnan ina so."
  Ta gyada kai kawai don ta tsorata da ganin yanda ya susuce tasan babu sauki. 
  Ai kuwa janta ya yi sai sashensa. 
Chapter 102 · 0% Book details