← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 116

Sashe 5

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

  Ita kuwa Hajiya Lubna, yaranta biyun farko 'yan biyu ne mace da namiji. Hassan da Hussaina, sai Adam da Hajara.
    Bar ganin gidannan kamar ba shi da girma Ummi, sai kin shiga can 6angaren zaki k'ara tabbatar da girmansa. Sashe hud'u ne har na Alhajin. 
   Saidai duk haduwar sashen matan bai kai na maigidan ba, da girma da komai. 
   Hajiya Madina duk ta fisu fada a wajensa, ko don tana ganin ita din 'yar uwarsa ce kuma tana da daurin gindi wajen mahaifiyarsa Gwaggo ne? Bani dai da masaniya. Amma tabbas Gwaggo bataso ko kusa Hajiya ta kai k'ararsa wai ya 6ata ranta, yanzun nan zata bud'emishi wuta. Shiyasa daga Hajiya Binta har Hajiya Lubna, basu kaunar zuwan Gwaggo Kano, kawai saboda bambancin da take nunawa tsakaninsu da Hajiya Madina. Hakanan tafi zuzuta kaunar 'ya'yan Hajiya Madina har yakai ma bata iya 6oyewa.
    Bada son ranta akayiwa Hajiya Madina kishiyoyi ba, saidai kawai don Hajiya Madina ta nunamata tafison kwanciyar hankalin mijinta akan tashin hankali da damuwarsa. 
  Gaskiya Ummi a wani 6angaren, Hajiya Madina tana da mutunci duk kuwa da cewar bata kama k'afar Hajiya Mama ba. Hajiya Mama ciki d'aya suka fito, saidai ita bata da raina 'yan aiki kuma yaranta sunsan girman ★DAN ADAM★ basu rainashi ko yaya ne. Toh yanda Hajiya Mama take, hakanan itama babbar yayarsu, Hajiya Fatima take. Su uku daman cif a wajen babansu, daga su bai kara haihuwar wasu ba kuma matarsa daya, Baba Ummahani.
  Ita a Abuja take zaune. Tana da yaranta hudu samari manya, sai yan mata biyu. Ta aurar da yaranta maxa biyu na farko, matan da ragowar mazan biyu sune dai basuyi aure ba. Mijinta tsohon soja ne kafin daga baya yayi ritaya. 
     Amina ta d'an tsagaita sannan ta d'ora tana duban Ummi wacce gaba daya kacokam ta maida hankali gareta tana sauraro.
  "Hajiya tana da saukin hali idan kika zama mai bin umarninta kan lokaci, sannan tafiso kafin tayi korafi akan bakiyi aikin da kika san kina yi ba toh ki kammala shi. Ko kusa bata son kazanta, hakanan bataso kice zaki wulakanta abinda ta haifa. Batason kuma shigen d'akunan abokan zamanta, idan kika kiyaye bakinki daga daukar magana ki kai wani dakin toh fa zaku d'asa da ita. Ba ruwanki da shishshigi a lamuranta matukar ba ita ta so ki tanka ba. Ki kiyaye kawo mata gulma, nan ma zaku 6ata da ita. Sannan ko wani abu marar dacewa kikaga ta yi, bataso ki tanka mata, nan kuwa zaku 6ata. Batason ta kamaki da cin amanarta. 
Yaranta suna da saukin hali Ummi, matukar kika kama kanki ba zasu rainaki ba. Ihsan ce ma mai matsalar, ita kuma kiyi kokarin fita harkarta. Idan dai ta sanyaki aiki kada ki k'i, kiyi hakuri kiyishi hakan saboda itace ma musabbabin da yan aiki basujin dadin zaman gidan. 
     A duniyar nan, kawai dai ki tsare abinda za'a ci mutuncinki ko yayane, kedai ki tsaya matsayinki baruwanki da cusa kai kinji ko?"
    Ummi ta danyi murmushi alokaci guda hawaye suka zubomata ta sharesu, wai yau itace da samun mai bata shawara a lamarin rayuwa? Itace ta samu wannan gatan har haka? Wani irin kaunar Amina ya k'aru a zuciyarta. 
  Amina da mamaki ta mike zaune.
"Ummi kukan kuma na menene?"
Ummi ta girgiza kai.
"Bakomai."
Amina ta ji wani tausayi ya dabaibayeta. Tasan akwai wata matsala a rayuwar Ummi, tafi kuma tunanin bata da iyaye. Ta numfasa, batason ta matsa mata da tambaya, ta tabbatar wataran don kanta zata gayamata tarihinta. 
   "Komai yayi zafi maganinsa Allah Ummi. Ki bar damun kanki da lamuran rayuwa har haka kinji ko? Ki rik'i addu'a da karatun Alkur'ani da sallar dare. In sha Allah komai zakiga ya wuce."
   Ummi da fuskar tausayi ta dubeta.
"Nifa bansan komai na Addini ba wallahi. Kawai dai ina yin sallah idan naga lokaci yayi mutane sunayi."
  Mamaki karara ya bayyana saman fuskar Amina, batasan ya akayi ta jefomata tambaya ba.
"Wai Ummi, iyayenki basu raye ne? Shekarunki nawa yanzu?"
  Ummi tayi k'as da kanta ta soma hawaye. 
"Mahaifiyata ta rasu tun ina jaririya, babana yana raye. A hannun matarsa na taso."
  Kwallah ta cika idanun Amina, ta gano bakin zaren. 
  "Idan ba damuwa ki sanarmin tarihinki mana."
  Tiryan-tiryan ta sanarmata da irin rayuwar kuncin da ta rayu ciki. Cikin muryar kuka tace.
  "Kalmar da ta kasa ficemin a rai bai wuce da babana yace wai ko birnin sin ne na tafi ba shi ba damuwarsa bace. Babana baya sona yanda yakeson kanwata Mariya."
  Kuka sosai takeyi, itama Amina tana tayata. Wani kaunar Ummi ya k'aru a ranta, ji takeyi tamkar kanwarta ce ta jini. Dakyar Amina ta rarrasheta tayi shiru sannan ta dubeta da kulawa.

"Karki damu Ummi, ki cigaba da hakuri sa mik'awa Allah lamuranki. Komai kika gani, daga gareshi ne. Watarana zaki ga komai kamar ba'ayi ba, nan gaba zakiji dadi a rayuwa in sha Allah. Kada kiyi bakinciki da zuwanki gidan Hajiya, na tabbatar ko a kwana d'ayan nan da kikayi, kinga chanjin rayuwa ballantana kuma idan ya zamana kin shure satittika anan. Nasan dai duk wani wuya da zaki ci anan bazai kai rabin wanda  kika labartamin ba. Hajiya bata duka, bata zagi haka kawai, saidai idan ka ta6a jininta, zata budemiki wuta tayi fada sosai harma idan baki taki sa'a ba ta goranta miki. Duk kuma wani abu na rayuwa ki daukeshi mukaddari ne daga Allah, ba wanda zai tsallakewa kaddararsa kinji ko?"
  Cikin jin wani sanyi ta gyad'a kanta. 
"Toh Anti nagode."
Amina tayi murmushi. Baccin safen da basu samu komawa kenan ba, sukayi ta hira a karshe Amina ta mike ta shiga wanka. Bayan ta fito Ummi itama ta fad'a. 
  Ta kammala ta fito, Amina tuni ta shirya cikin doguwar riga ta yadi, daga gaban rigar, anyi adon duwatsu, ire-iren dai wanda take samu daga Hajiya Mama ko yaranta. Ummi ta dubeta, tayi mata kyau, zata soma duba jakar kayanta ta ji muryar Amina.
  "A'a Ummi, ga kaya ki saka."
Ta juyo don ganin ko ta ciro mata ne, saidai ta ga wasu da ba nata na asali ba, riga doguwa ce ta abaya. Ta dubi Amina ido a waje.
  "Lah, anya kayanki zasu yimin Anti?"
Amina ta murmusa.
"Wannan na jima bana sakashi, na kuma tabbatar ba zai k'i yi miki ba. Kedai gwada mugani. Idan kin kammala ki fito ki gaida Hajiya, nasan yanzu ta farka."
  Ummi ta amsa da toh, Amina ta fice. Rigar ta kar6eta kwarai tayi mata kyau kasancewarta farar yarinya. Ta dauki dankwalin ta d'aure gashinta wanda idan mutum yaga yanda yayi mata, zai iya cewa tayi d'aurin acuci. 
   Saida ta dauke shimfid'a ta d'an gyara d'akinnasu duk da ba daud'ar azo a gani don Amina akwai tsafta, sannan ta bi bayanta.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

07
Chapter 5 · 0% Book details