Sashe 6
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A falon ta tarar da Hajiya Madina zaune cikin kwalliya tana karyawa, Amina bata nan, ta karasa ta durkusa ta gaisheta a ladabce. Hajiya Madina ta amsa fuskarta a sake, bai wuce ganin yanda Ummin tayi fes ba don ita ba mace ce mai son zama cikin k'azanta ba.
Ummi ta zauna, idanunta akan talabijin, saida Hajiya ta kammala sannan ta umarceta da d'auke kayan, ta d'aukesu ta kai kicin. Acan ta had'u da Ramma tana faman gyare-gyare. Ta gaisheta a mutunce, Ramma ta amsa har tana zolayarta wai har ruwan birni ya soma kar6arta ta chanja saidai k'ashin wuya. Ita dai murmushi tayi kawai.
Tana shirin fitowa sukayi kici6us da Amina, hannunta rik'e da tsintsiya da kwandon shara.
"Kinga yayi miki kyau ko? Nima na gyaro d'akin Hajiya ne, kije tana kiranki ma."
Ai da sauri Ummi ta fita don amsa kiran.
Wannan karon a kan kujera ta sameta tana amsa waya. Zama tayi har ta kammala sannan tayi magana.
"Gani Hajiya." Ta dubeta a nutse sannan ta soma magana.
"Yauwa Ummi, dafatan dai Amina ta nunamaki dukkan ayyukan da takeyi? Toh inaso ki zamo mai rike amana, muddin kika ci amanata, bazan kyaleki ba. Yanda zan rik'i amanarki da gaskiya a matsayinki na Amanar a hannuna, haka kema nakeso ki rike, ki kula da dukkan ayyukan da zaki dunga yi." Ta k'ara karanto mata ayyukan harma da na gyaran sashenta ciki da falonta na biyu, banda wannan da suke ciki don duk cikin aikin Ramma ne. Ta k'ara jaddamata cewar batason k'azanta, hakanan ta kiyaye tsaftar suturunta, duk sadda zatayi wanki, ta tambayi omo zata samu. A dai maganganun Hajiya, Ummi ta fahimci cewa dagaske batason k'azanta kuma tana da kyankyami.
Ta rausaya kai.
"In sha Allahu Hajiya zan zama mai kula da dukkan abinda kukace, nagode Allah Ya k'ara girma da arziki."
Har a ranta ta ji dad'in maganganun Ummi.
"Shikenan kina iya tafiya."
☆☆☆
Tun daga wannan ranar, Ummi ta kama aikinta sosai, Amina na taimakonta. Har ya kasance wani sa'in kafin Amina ta tashi, ta rigata tashi. Tana jin dad'in zama da Amina saboda shawarwarin da take bata, har karatu tana koyamata. Duk da cewar Amina na cin wuya don Ummi ko bak'i bata iya ba. Duk sai ta bata tausayi, haka take lalla6awa ta biyamata, amma ta tabbatar muddin tana wajen Hajiya Madina, bazata ta6a bari ta zauna mata da jahilci ba, duk wadanda suka ta6a zama sukayi aiki awajenta, ba wacce bata sanya a islamiyya ba, boko ne dai ba lallai ka samu ba.
Saida Ummi tayi sati da zuwa, sannan Amina ta soma shirin tafiya don Hajiya Mama sun dawo. Gaba daya ta ji babu dadi, tana zaune gefe tana duban yanda take ninke kayanta tana sanyawa ciki jaka. Amina ta ankara da duban da takeyi mata, itama sai taji batason rabuwa da ita.
"Haba Ummi, menene abin damuwa har haka alhalin muna gari d'aya? Karki damu, na tabbata zamu dunga ganin juna. Kedai ki cigaba da hakuri da zama da su tsakaninki da Allah."
Ummi ta gyad'a kai.
"Toh Anti." Sai yamma suka tafi har Hajiya da su Adnan, gidan ya rage Ummi kad'ai da Ramma. Bayan ta kammala ayyukanta ta fito farfajiyar gidan tayi zamanta. Bata kai mintuna biyar a zaune, budurwar da bazata ta6a mance fuskarta ba wacce suka samu sa6ani da Adnan a farkon ganinta da su, ta fito daga sashensu tare da k'awayenta har su biyu suna dariya.
Hararar da ta sakarmata ne yasa ta dauke kanta babu shiri ta saddar a k'asa, ta gabanta sukazo wucewa, ai kuwa ta sanya takalminta mai tsini ta take yatsun k'afarta har saida tayi k'ara. Ta juyo ta rankwasheta.
"Munafuka, sharri zakiyimin kina gidan ubana kina cin arziki? Shegiya kawai."
K'awayen dariya kawai sukayi, d'aya tana fad'in "Kai Iklima baki da kirki."
Iklima ta ta6e baki.
"Na kaiku?"
Suka fice Ummi ta mike da sauri tabar wajen, saida ta tsaya a lungun ta share kwallah sannan ta k'arasa ciki. Ta zauna a kicin tana kallon yanda Ramma ke faman had'a miya, tana dan jan Ummin da hira har ta share batun Iklima ta saki jikinta.
☆☆☆
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
08
Bayan tafiyar Amina, Ummi dole ta sabarwa kanta hira da Ramma, don Ramma mace ce mai abin dariya. Ayyuka ko kusa basu bata wuya sosai don a ganinta ta saba da fin haka acan gidansu. Sau da yawa takan tuna Mahaifinta, tana tunanin ko wane hali yake ciki yanzu, saidai daga zuciyarta ta tunano mata irin tsana da tsangwanar da take sha a wajen shi kansa, sai ta ji tunanin ya kau.
A d'an zaman da sukayi da Hajiya Madina ta fahimci Ummi lallai bata da wani ilimi da addini, ta lura ko sallolinta akwai gyara ciki, wannan dalilin ne yasa ta sanya Ramma kaita makarantar da yaranta(ita Rammar) ke zuwa, karfe biyu suke zuwa su taso k'arfe biyar na yamma. Babu ruwanta da shiga sashen kowace matar gidan don sosai ta dauki gargadin Hajiya Madina, hakanan tana rike da nasihar Antinta.
Alokacin Hajiya Lubna amaryar gidan sun dawo daga Maiduguri, ta lura yaranta suna da kirki basu da hali irin na yaran Hajiya Binta. Saidai uwarsu ce sai a hankali, mace ce mai shan k'amshi, saika gaisheta sai ta ga dama take amsawa.
Maigidan ma bai rufe sati biyu ba ya dawo. Ranar da ya kasance Hajiya Madina ce da aiki, sun ci aiki sosai, har da Hajiya Madinar. Ummi banda wanke wannan mik'o wancan babu abinda takeyi. Abinci kusan kala uku ta ga anyi ciki harda suyar kaza bayan an tafasa an tura shinkafa da kayan hadi a k'asanta an toshe bakin da dankali babba guda d'aya. Sai lemun zo6o da taga sun had'a sai kamshin abarba yakeyi. Aka kammala aka zuzzuba, suka ajiye a saman tebur. Ummi da Ramma suka tattara kicin din, can bayan magriba, lokacin Ramma ta tafi, sai ga Hajiya Madina ta fito daga dakinta ta ci ado cikin wani (yellow lace) wanda ya sha adon duwatsu, tayi kyai sai k'amshi kawai ke tashi a jikinta.
Ummi na rak'u6e a can gefen kofar kicin tana kallon wani fim na yak'i da su Adnan suka nutsu suna kallo.
"Wow! Wallahi Mom kinyi kyau."
Cewar Ihsan tana mikewa tsaye, daga ita sai riga iyaka gwuiwa da riga tshirt kanta hula ce ta sanya. Ta isa ga Mamin tana mai sanya hannu ta k'ara gyara mata zaman d'aurin. Murmushi kawai Hajiya Madina tayi.
"Naji, taho ki kaimin kayannan sashen Abbanku."
Ihsan tayi dariya.
Tare suke fice ta dauki wasu Ihsan ta dauki sauran. Ummi ta bi Hajiya Madina da kallo cike da sha'awa don kwalliyar ta burgeta. Idan kana da kudi babu abinda ba zakayi ba.
Har ta gaji da kallon, ta koma daki ta hau duba karatunta, a karshe da ta gaji, kwanciya tayi abinta wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita don bata ta6a aikatuwa irin na yau ba saboda girkin dawowar Alhaji da ta taimaka da shi.
Bayan kwanaki biyu da dawowar Alhajin, ranar juma'a bayan ta je ta gaida Hajiya. Hajiya ta dubeta a nutse. Doguwar bakar abaya ce jikinta na wajen Amina.
"Wai ke baki da kaya ne sai wadannan guda ukun? Yau idan kin saka doguwar riga bak'a, gobe sai jan atamfa kodadde, jibi ma haka? Bakizo da kaya bane ba?"
Ummi ta sunkuyar da kai gaba daya jikinta yayi sanyi, cikin rawar murya tace.
"Eh su kadai ne masu d'an dama-dama Hajiya."
Hajiya tayi shiru da mamaki, kafin tace. "Daukomin duka kayanki nagani."
Ta mik'e da sauri ta cika umarninta, Hajiya ta sanyata ta zazzagesu. Kayan duk ba wani na kirki kam da gaskiyar Ummin.
"Kwashesu ki maida ledar, kada su koma wannan d'akin. Fita kimin kiran Ramma."
Ta amsa da toh, ta mayarda kayan jaka sannan ta fita ta kira Ramma. Tana ji Hajiya tace idan ta kammala tayi magana zata bata kudade gobe ta shiga kasuwa ta siyo mata kananun atamfofi guda hud'u sai dogayen riguna yan kanti su kuma guda uku sai wanduna da vest guda shida-shida. Ramma ta amsa da toh, zata mike Hajiya ta dakatar da ita.
"Tafi da wannan ledar a zubar don Allah." Ramma na dariya ta dauka tayi gaba tana fadin toh.
A washegarin kuwa Ramma bata zo da wuri ba sai wajen sha d'aya na safe. Sai gata da kayan da Hajiya ta umarceta. Hajiya ta duba sannan ta bata atamfofin ta kai dinki, tayi kiran Ummi ta mik'a mata ledar kayan ta kara jaddada mata cewa ta kula da tsaftar jiki da dakin da take kwana. Ummi ta amsa tayi godiya ranta fari k'al ta zubawa Hajiya ruwan addua wanda hakan ba k'aramin faranta Hajiya Madina yakeyi ba. Saida ta shiga ta zazzage kayan tana duba, ai kuwa dai abinda Hajiya ta karanto shi d'in aka sissiyo harma da k'arin man shafawa da turare (Lovilla) na roba. Har wani tsalle tayi na murna, ko babu komai a makaranta yan ajinsu zasu dinga jin tana k'amshi kamar yanda ta ga yan babban aji a makarantar suna yi idan sunzo giftasu ko kuma monitoci.
☆☆☆
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
10