Sashe 11
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
13
A gajiye likis Ummi take, suna zuwa sallolin dake kanta kawai tayi ta kwanta. Bata kara sanin abinda ke faruwa ba a duniyar sai bayan farkawarta da Asuba. Bayan ta idar da sallah ta zauna anan addu'o'i har garin Allah Ya waye, kasancewar babu makarantar boko ballantana ta tashi had'e-had'en karin yaran yasa ta komawa tayi kwanciyarta, baccin da tayi har ya fiye mata na farko dadi, ta jima tana bacci kafin kuma ta soma jin ana bubbuga kafarta ana kiran sunanta. Farkawa tayi a firgice tana salati, ganin Fahad yasa ta sauke ajiyar zuciya. Kira ne daga Maminsa akan ta soya mishi kwai ta had'a da biredi da shayi. Dole ta mike ba don baccin ya isheta ba ta fad'a bandaki ta wanko bakinta da fuska sannan ta bi bayansa.
Saida ta kammala komai sannan ta fad'a d'akinsu, ganin Ihsan bata farka ba yasa ta fitowa batare da tayi abinda ya kaita ba(wato gyaran daki). Tana gudun ta shiga bandakin don wankewa Ihsan ta yi mata rashin mutunci tace ta hanata bacci.
Misalin karfe biyun rana, kowannensu yayi shirin Islamiyya, kai tsaye yaran wajen mahaifinsu suka nufa sanin da sukayi cewar yana garin suka kwashi gaisuwa ya sallamesu da abin kashewa bayan makaranta sannan suka d'uru cikin mota, suka tafi. Sai lokacin ne Ummi ta samu sararin yin nata shirin na makaranta tana ta zabga uban sauri adalilin lattin da ta so yi, haka ta fito cikin shiri ta yiwa Mami sallama. Mami ta amsa gami da yi mata fatan alheri, har ranta ta ji dadi don abu ne da sam Mamin bata saba ba, alamun Mami gaba daya a yau sun nuna tana cike da nishadi wanda babu damar tambayar dalilinsa. Ta sanya kai ta fice daga gidan.
A makaranta nan dinma ta ji dadi sosai don kuwa ta kai haddarta saidai ta sha gyara duk da baikai yawan yanda a baya Malamin nasu ke cin gyaranta ba, ta lura yana yi mata uzuri ganin ko bak'i bata iya had'awa ba, wannan dalilin yasa ya ware mata lokacinta daban yake koyar da ita wasula da bak'ak'e.
Koda suka tashi, cike da nishadi ta dawo haka kawai a yau batasan farincikin ko menene takeyi ba, ta godewa Allah yafi sau biyar a zuciyarta. A farfajiyar gidan ta iske motar Danliti, hakan ya bata tabbacin cewar Ihsan sun dawo. Hajiya Binta ta gani tare da wata wacce ba yau ta soma ganinta ba ga dukkan alamu kuma kawarta ce. Ta gaishesu a ladabce, suka amsa ciki-ciki suna karemata kallo. Bata kai ga karasawa ba ta ji suna maganarta, inda matar ke cewa.
"Ina mamakin Hajiya Madina, ko a ina ta kwaso wannan mai ruwan buzayen? Wannan ko Alhajinku ya gani mai yiwuwa yayi ta hud'u da ita."
Ta karashe tana dariyar zolaya. Hajiya Binta ta ja tsaki.
"Ai kuwa da anyi girman kwabo, ballantana kuma sanin kanki ne Alhaji banda waccan shegiyar babu mai fad'amasa ya ji acikinmu, abin na kona raina."
"Ai ku kukayi sake, ki bada hadin kai kika yanda komai zai chanja mana."
Iyakar abinda Ummi ta tsinkaya kenan cikin zantukansu kafin kuma ta ta6e baki kawai, a kasan ranta kuwa tana tsoron ranar da Mami zata gaji ta korata daga gidan, watakil shikenan kuma dukkan gatan da ta soma samu na ilimi ya rushe. Saidai kuma tayi mamakin yanda Hajiya Binta take kula kawaye irin haka, da ace sun saba kwarai, da babu abinda zai hanata yin shishshigi wajen bata shawarar watsi da zantukan wannan mata. Da sallama ta nufi shiga falon, saidai kuma tayi turus ganin takalman maza har sawu hud'u da kuma na mata a bakin kofar, haka kawai ta ji gabanta ya fad'i, koda ta shiga bata ga kowa ba a wannan falon, ta numfasa ta karasa ciki, har ta chanja sutura tana cike da tunanin wadanda suka zo, sai kuma ta tunano da su Yaya Haidar, watakila su d'inne suka zo. Ta shirya cikin atamfa riga da zani da dankwali bayan tayi wanka sannan ta d'auro alwala ganin Magriba na dab da yi, fitowa tayi falo, tana son zuwa sanarwa Mami cewa ta dawo saidai kuma batason iske bak'in gaba d'aya nauyinsu take ji.
A kicin ta had'u da Ramma, ta gaisheta. Ramma ta amsa tana fad'in.
"Yanzu kuwa Hajiyar ke tambayarki, ta ji shiru nace kin dawo kina ciki. Kije tana nemanki."
Gaba daya ta ji tsoro ya kamata har yanayin fuskarta ya nunawa Ramma.
"To ai naga tana tare da bak'i yanzu."
Ramma ta kama baki. "Su waye bak'in? Ai 'yan gida ne, Hajiya Babba ce fa da yaranta."
Ta gyada kai sannan ta juya ta nufi hanyar falon Mami gabanta na dukan tara-tara, ita da ba don ance Mami ke nemanta ba da babu inda zata. Har ta kai kofar shiga sai kuma ta juya da sauri don ji tayi ba zata iya ba. Muryoyin da ta jiyo daga bayanta na matasan yasa dole ta juyo. Gaba daya mazan ne suka fito da alamu dai masallaci suka nufa sakamakon kiraye-kirayen sallar da aka soma. Kallo d'aya tayi musu ta durkusa da sauri ta gaishesu. Suka amsa sannan ta basu wuri don su wuce. D'ago idon da zata yi sukayi ido hud'u da Faruk wanda dagaske kallonta yakeyi, ta gwammace ace bai kalleta din ba domin kuwa kallo ne ba na arziki ba face kallon raini, fuskarsa babu wata alamar fara'a; ta sadda kanta da sauri.
"Ai kuwa Mami na ta cigiyarki da alama kin mata wani gagarumin laifi Ummi." Cewar Adnan ya karashe da dariyar zolaya.
"Um." Shine abinda ta furta kawai da murmushi dauke saman fuskarta. Bayan sun wuceta ta bi bayansu da kallo. Wannan karon, Yaya Usman ne kadai ya sanya manyan kaya, gaba daya su ukun k'ananun kaya ne jikinsu. Hajiya Babba Allah Ya bata arziki na zaratan maza wadanda dukkansu basuyi kama da ragwaye ba a komai da ya shafi gwagwarmayar rayuwa da sauransu. Saidai da ace za'a bata za6in wanda yafi kyau da burgewa a fuska acikinsu, toh fa babu abinda zai hanata nuna Yaya Haidar bisa hujjarta na ganin duk ya fisu fara'a. Koda kuwa tasan da yawa cikin wasu matasan yanmata irinta, zasu iya bugun kirji su za6i Yaya Faruk, ita kam banda ita. Tsakani da Allah ta ji haushin kallon da ya bita da shi tamkar wanda ya ci karo da kashi, ta numfasa don tuni sun jima da kauracewa ganinta ta juya, gabanta ya fad'i ganin Ihsan tsaye ta harde hannuwa a kirji ta zubamata na mujiya fuskarta dauke da wani mugun murmushi. Ummi ta kauda kai ta bi ta gefenta zata wuce saidai maganganun da ya soma fitowa daga bakin Ihsan ya tsayar da ita cak!
"Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki."
Daga wannan ta sanya kai ta fita tana kwalawa Ramma kira. Iyakar radadi da bacin rai, Ummi ta ji shi a ranta, batasan sadda idanunta suka ciko da kwalla ba, wannan cin zarafi har ina? Kai tsaye an yankemata mummunan hukuncin da ko a mafarki bata yi zaton koda mak'iyinta zai shaideta da aikatawa ba, toh daman ina ita ina ire-iren wadannan mazan? Yaudarar kai ne, koda ta auna cewa Ihsan batasan irin zargin da ya kamata tayi mata ba, yasa ta yin murmushi mai ciwo, da alama Ihsan bata gama sanin bambancin matsayinta da su ba, tabbas ta cucesu tunda har ta had'asu da ita, watakil da zasu ji da sai sun had'a da kai mata bugu don haushin abinda tayi musu. Ta share batun gami da goge fuskarta sannan ta juya ta koma don ta tabbatar a yanzun Mami ta shiga sallah. Dakinta ta koma itama ta tayar da nata sallar, saida ta idar ta kaiwa Allah kukanta akan Ya ji6anci lamuranta. Bata da kowa sai Shi, Shi ne gatanta. Yayi rahma ga Mahaifiyarta. Haka tayita kwararo addu'o'i har tana fidda ruwan hawaye kafin kuma ta shafa. Bata kai ga mikewa daga wurin ba ta ji Fahad na kwala mata kira adaidai sadda ya murd'a kofar dakin nata.
"Ummi! Kizo inji Mami."
Ta mike batare da ta cire hijabin ba ta bi bayansa.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
15
Anan ta iskesu tsaitsaye ana hira banda babban yaya wato Yaya Usman da ke zaune cikin mota tare da Faruk wanda gaba d'aya ya matsu su koma gida don jinsa yake a gajiye.
Ihsan ta bita da kallon harara, hakan yasa ta kauda kanta.
"Kanki ake ji." Ta fad'a a ranta. Ta dubi wata doguwar budurwa siririya bak'a, bata san itace Ikram ba ko kuma Baraka, don sunayensu kawai Amina ta sanarmata ba ta nunamata su ba a fuska.
"Ga wannan a ina zan ajiye?"
Ta dubeta, sannan ta nunamata motar da yatsa batare da dogon bayani ba.
"Kinga, saka anan."
Ta dubi Yaya Haidar dake nunamata boot wanda yasa hannu ya bud'e. Ta karasa ta ajiye gami da fad'in.
"Allah Ya tsare hanya." Daga haka ta juya ta bar wajen.
"Adnan ina mutuniyata ne? Ban ganta ba."
Adnan ya yamutse fuska yana duban farar budurwar siririya da tayi mishi magana, wato Baraka.
"Wa kenan?" Ya tambaya cikin basarwa kamar bai fahimci ko wa ta ke nufi ba da gaske.
"Abokiyar fad'arka mana, your lil sis."
Ya harareta, ya gane Iklima take magana akai.
"Ai kinsan hanyar gidansu ko? Sai kije."
Baraka tayi dariya.
"Kwarai ma kuwa wallahi, idan ma kana ganin kamar bazan iya zuwa ba zaka sha mamaki. Kada fa ka manta k'awata ce, mun riga mun saba da uta adalilin (whatsapp group) da muke ciki tare. Zo muje Ihsan ki rakani."