← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 116

Sashe 33

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                  ***   ***   ***
                      ABUJA
Ranar da ya kama na yini da(mother's day) ranar akayi sanya ankon atamfa mai fari da bulu. Sunyi kyau matuk'a. Gaba daya abin ya burge, sai bayan magriba kowa ya soma shirin tafiya wajen fatin. Abin nasu ya yi kyau matuka, su Ummi a gida aka barsu rainon yara, har saida suka yi hira suka gaji suka soma gyangyadawa sannan suka soma dawowa. Alokacin suka koma dakinsu suka kwanta. 
   Washegari kuwa tun asuba basu koma bacci ba, suna kicin suna dirkar aiki na hada karin kumallo. Sai wajejan tara suka kammala komai suka mik'amusu. 
  Wajejan sha daya na safe sunyi wankansu tsaf, Aisha ta hada Ummi da wankin Tahir. Haka ta kar6a don ba ma su yawa bane sosai. 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  46
   (Sadaukar ga shafin nan gareki sisna...forgive me... Meena Yoruba)
Wajen garden inda ta ga anan suke wanki da shanya ta zagaya ta soma yi. Tare suke da Amina suna hira inda Amina ke labartamata batun aurenta da ya taho, Sa'a ta zo ta sanarwa Amina kiran Hajiya Mama. Wajen ya rage Ummi kadai cike da tunanin duniya. 
To ita meyasa bata ta6a jin son wani ba ne? Ga dai maneman suna tururun zuwa har da yaran manyan dake layin makarantarsu masu son ta kulasu saidai ko kad'an babu wanda ta ta6a saurara, maganar Antinta ta fad'omata a rai.
"Kema auren nan ya dace kiyi Ummi, shi kadai ne jin dadinki, ki tara zuri'ar kanki."
   Abinda tace mata kenan a wannan hirar da sukayi. Ta girgiza kai tana duban wani dan lilo dake a wurin.
  'Babu wanda nake so a raina yanzu Anti.' Ta ayyana a ranta. Haka ta k'arasa wankin ta mik'e ta nufi wajen shanya, tana cikin shanyar ne ta ji sallamar mutum agefenta. Da sauri ta dubi wajen jin muryar namiji. Ta gane ko wanene duk da batasan sunansa ba, amman cikin bak'in Adamawa ya ke. Kana ganinsa shima kaga bafulatanin usuli, ta gaisheshi ya amsa da harshensa mai sirkin yare biyu(Hausa fulani).
  "Sannu, ina daga can ina ganinki tun dazu ai, ya sunanki ne?"
  Mamaki karara ya bayyana saman fuskarta, baiyi kama da saurayin arziki ba, yafi yin kalar 'yan duniya. Ta k'ara kare kirjinta da ya zubawa ido don kuwa doguwar rigar jallabiya ce jikinta kusan duk ta jik'e agarin wanki.  Murya na rawa batare da ta k'ara kallonsa ba ta amsa.
"Ummi."
Ya lura da abinda ta yi din sai kawai ya yi murmushin duniyanci ya shafi ha6ansa.
"Wow, kina da suna mai dadi fa. Ni sunana Kabir but you can call me KB. Ke 'yar uwar su Daddy na Baraka ce?"
  Ta girgiza kai don ta k'osa ya bar wajen.
"Aa, ni 'yar aiki ce."
Ya zaro ido da mamaki.
"Yar aiki? Kike da wannan kyan?" Ya ta6e baki 
  "Gaskiyar magana bebi kin fi karfin zama yar aiki. Idan za ki ban had'in kai to zakiji dadin rayuwa son ranki."
  "Innalillahi..." Ta karashe a fili. Zaiyi magana, Amina ta katse hirar ta hanyar gaisheshi. Suka dubeta don basusan ta iso ba, ya amsa ba don yaso zuwannata ba, ya wani tamke fuska gami da fadin.
"Sai wani time din bebi, zan nemeki."
Daga haka ya fice, da sauri Amina ta nufota gami da rike kafadarta a tsorace.
  "Mene hadinki da Kb? Kinsan kuwa ko wanene?"
  Itama Ummi duk sai ta k'ara rud'ewa.
"Wallahi shi yazo nan yanamin magana." Ta zayyanemata yanda sukayi. Amina ta numfasa.
"Nagode Allah da ba ki ce komai bayan wannan ba, ki yi kokarin nisantarsa, yaron dan iska ne fiye da tsammaninki. Akwai sadda ya ta6a zuwa gida Hajiya Mama basunan sai ni kadai, wallahi Allah ne kawai ya kwaceni daga hannunsa, ya so 6atamin rayuwa. Ki kiyaye Ummi, nasan halinki, ki k'ara akan wanda nasanki na tsare mutunci."
  Ummi ta dubeta.
"In sha Allah Anti zan kiyaye."
Ta taimakamata wajen k'arasa shanyar sannan suka nufi ciki. Da gudu Sa'a dake la6e ta koma ciki. Kai tsaye dakinsu ta nufa kicin ta nufa inda Binta ke goge-goge ta fesamata yanda Kb da Ummi sukayi harma da nasihar Amina gareta. Binta ta ja tsaki.
"Banza da ita, ta samu damar da muke nema ta yi watsi da shi, ji dai yanda ya nemeki sau d'aya kuma ya dawo ya juyamaki baya sai zagi idan ya zo kamar gidan ubansa."
  Sa'a ta yi kwafa cike da jin takaici.
"Bari kawai, ni su Ummin ma sunfi ban takaici su basu yarda ba masu tsoron Allah. Gulma ce dai, ta ciki na ciki."
  Binta ta ajiye tsumman hannunta.
"Ke, ga hanyar samun kudi wajen Kb. Mezai hana tunda ya ganta ya kyasa, mu kai mishi ita kinga kuwa ba karamin kud'i zai bamu ba."
Sa'a ta yi shiru tana nazari, tasan Kb akwai sakin aljihu musamman akan mace. Ta dubi Binta suka kyalkyale da dariya sannan suka cafke.
"Shegiya, kina ja wallahi. Bari zan sameshi a 6oye mu ji yanda zaayi."
  Cewar Sa'a, Binta ta jinjina kai cikin gamsuwa.
      Da yamma kuwa duk ana ciki ana shan kid'a da rawa kasancewar an daura aure kuma ba wani(event) da suka shirya zasuyi sai dinner wanda Ango ya shirya kayansa. Sa'a ta yi nasarar ganin Kb a farfajiyar gidan yana amsa waya can gefe, da sauri ta karasa wajensa tana fadin. "Yalla6ai." Ganinta yasa ya ja guntun tsaki ya daure fuska, saida ya kammala waya ita kuwa na waige-waige bata hangi wani mai ganinsu ba. 
"Lafiya?" Ta dubeshi tanq murmushi.
"Lafiya kalau, daman wata magana na zo maka da ita."
  Ya daga kafada.
"Ta mecece?" 
"Dazu na ganka kana magana da Ummi, nasan kuma ka kyasa dw ita ne. Idan babu damuwa ni zan kawomaka Ummi, idan har ka yarda za ka biyani."
  Wani sanyi ya ji a ransa, sai lokacin ya sakarmata wani shu'umin murmushi ya sosa kai yana duban farfajiyar gidan, babu wani mai kallonsu sai tsirarun ma'ikatan gidan dake harkokin gabansu.
  "Idan kudi ne, kinsan bani da matsala da su. Kedai ki cika alkawari."
  Ya kara dubanta fuska babu wasa.
"Kada kuma ki kawomin rainin hankali idan ba haka ba kinsan sauran. Ki zauna cikin shiri, yau da zarar kowa ya tafi wajen(party) ki yi yanda zakiyi ki kawomin ita sashenmu, zan iya biyanki ko nawa ne."
   Daga haka ya fiddo dubu biyu ya damk'a a hannunta. 
  "Ga wannan ki sanyawa wayarki kati, ai kina da lambata ko?"
Ta gyada kai farinciki ya cikata ganin dubu biyu, wanda idan ta yi wayasan ko nawa zai bata.

"Eh akwai." Daga haka suka yi sallama fuskar kowanne a sake. 

  Faruk dake daga sama yana dubansu ta windo, mamaki ya cikashi, shi yasan wanene Kb, yasan kuma illarsa ga diya mace. Babban abin daure kan menene hadinsa da Sa'a? Ko har ita din ma akwai abu tsakaninsu? Ya girgiza kai cike da jin tsanar Sa'ar domin ita ta bada fuska. Ya juya ya koma falo cikin yan uwansa kusan sa'anninsa kuma bak'in Adamawa aka cigaba da hira kafin duk su fito waje don shan iska. 
     Misalin takwas duk an soma tafiya wajen party da zaayi a Nicon, su Ummi dai na tsaye a farfajiyar wajen sai kallon kwalliya sukeyi. Kowacce ka gani ji takeyi da kanta, duban kanta takeyi a had'add'iya. Wajen sai kamshi kakeji, matasan ma kuwa da alama har da samarin wasu cikin yanmatan. Duk wadannan ba su suka damu Ummi ba face ta inda zata ga 6ullowar Faruk. Shi kadai zuciyarta ta kwadaitu da gani batare da tasan tak'amaiman dalili ba.  
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  47
  Daga gefensu ta ji Ikram na balbale  Ihsan da fad'a.
"Wallahi zakiyi asarar fatin yau matukar kika kafe sai tare da Yaya Faruk za ki je, idan ma kin shirya tafiya gwara tun wuri ki taho mu tafi don wallahi a yanda nasa halin Yaya Faruk zai iya cewa ya fasa. Mun tafi na daukarmaki komai a waya." Daga haka ta yi gaba.
Ihsan ta yi saroro, ganin dai dagaske Ikram take yasa ta bin bayanta da gudu-gudu, abin sai ma ya bawa Amina da Ummi dariya. 
"Wallahi yanzu lamuran Ihsan dariya sukeban." Cewar Amina.
Ummi ta ta6e baki.
"Ato, tunda ta maida kanta wata tsiya ba."
    Saida suka ga tafiyar kowa amma basu ga na Faruk ba. Hankalin Ummi ya tashi, ranta ya sosu, ta so kwarai ta ga tafiyarsa, ta kwadaitu matuka da ganin kalar wankansa. Haka suka koma falon, iyayen daga Hajiya Babba sai Inna da wasu dattijai mata yan Adamawa ya rage, suna sama, suka tattara komai sannan suka wuce 6angarensu.
  Suna zaune anan sai ga Sa'a ta shigo.
  "Ummi, ki zo Adnan na nemanki."
  Da mamaki ta dubi Amina.
"Na dauka Adnan ya wuce."
"Tabbas nima naga shigarsu mota."
  Sa'a ta yi yak'e.
"Dawowa ya yi, wai ki zo sak'o zai ba ki daga Mami."
  Basuyi tunanin komai ba don babu wanda ya kawo Sa'a zatayi hakan cikinsu, Ummi ta mike da sauri yana gyara zaman daurin dankwalinta na atamfa, don sauri ko hijab bata tsaya sanyawa ba ta zura takalmi tana fadin.
"Bari naje."
Amina ta kishingida tana fadin.
"Wash!" Gami da lumshe ido, Sa'a ta kunce gefen zaninta ta yi amfani da hodar da Kb ya bata ta wuce sadaf-sadaf ga Amina ta shek'a mata a hanci, Amina kafin ta yi wani yunkuri bacci ya sureta. Da sauri Sa'a ta bi bayan Ummi. 
  Ita kuwa Ummi kai tsaye waje ta nufa saidai bata ga mota ba, hakan yasa ta zuwa wajen fakin motoci nan ma bata ga mota ba sai guda daya, da alama da mutum ciki sakamakon kidan da ke dan tashi amma zuwanta aka kashe. Zata nufi wajen Sa'a ta karaso tana kiranta. Ta tsaya gami da juyowa.
'Yauwa ina Adnan din?"
  Sa'a ta dubeta.
"Yanzu na ganshi ya nufi sashensu, shima nemanki yakeyi."
Ummi ta jinjina kai.
"Munyi sa6ani kenan, bari na je."

Da sauri ta nufi hanyar sashensu Adnan, Sa'a ta saki dariya yanda ba zata ji ba, ta bi bayanta. 
Chapter 33 · 0% Book details