← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 116

Sashe 93

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

112
Sanye ya ke da shadda kalar sararin samaniya sai hula shima bulu, sai murmushi ya ke bugawa yana gaisawa da yan uwa har da mikawa Dada hannu suna gaisawa gami da dariya.
Ummi bata iya motsi ba hakanan ta kasa cewa uffan saida ta tsinci muryar Amina na fadin.
"Wai daman *ABUBAKAR* dan uwa ne gareku?"
  Ta girgiza kai sannan ta maida dubanta ga Amina kamar wata doluwa. 
  "Wallahi bani da masaniya nima."
Basu kai ga tsinkewa da lamarin ba saida suka ga shigowar Alhaji Kabiru Jimeta da sallamarsa. Mamaki, rud'ani da tsananin faduwar gaba duk suka tararwa Ummi da Amina, aka rasa mai magana cikinsu har wasu cikin mutanen Jar Kwami suka shigo wasu rirrike da jakunkunan kaya. 
  "Wai ina Amaryar?" Cewar wata mace da zata kai shekaru arba'in a duniya. 
   Da sauri ta ja baya daga jikin windon tana sussunne kai, wata gwaggonta ta riko hannunta tana dariya.
  "Oh 6uya ki ke? To fito nan ga uwarki da ba ki sani ba, Safina, sannan kuma (ta nuna wata doguwa mai rike da bebi a hannunta, bazata wuce talatin da tara ba) itama uwarki ce Nafisa sunanta, duk yaran gwaggonki ce Binta."
Sukayi dariya, wacce aka kira da Nafisa ta ce.
"Maza fito na kaiki ku gaisa da Innarmu ta ga Innonta ta dawo."
Amina ta hau janyo musu ita don ta mak'ale a bayanta, ita kanta dauriya kawai ta ke yi saidai jikinta ya yi mugun sanyi, tambayar da kowannensu ke yiwa zuciyarsa bai wuce na son sanin dangantakar Alhaji Kabiru da mutanen gidan ba. 
  Ummi na kallo suka ja ta har rumfar Dada inda ake zazzaune ana gaisawa, kan Ummi a k'asa yayinda aka zaunar da ita gefen wata dattijuwa wacce shekaru suka ja saidai garas tana gane mutane sannan tana fahimta. Da harshen fulatanci ta ji wacce ta zaunar da ita ta yi magana. Abinda ta fada ne ya janyo hankalin sauran bak'in duk suka dubeta, Abubakar da hankalinsa ke kan wayarsa yana kokarin turawa uwargidansa sak'on isowarsu lafiya, shima ya dago kai yana duban wacce aka kira da Amarya kuma jininsa mai kama da Innonsa. 
  Mamaki k'arara ya bayyana saman fuskarsa, a yayinda shi kuwa Alhaji Kabiru ke kallon Ummi cike da al'ajabi na kamanninta da Antinsa Inno wacce a girme ma ya girmeta saidai duk da hakan kanwa ce ga mahaifiyarsa GWAGGO BINTA babbar Yaya ga Manu Lamido uba ga marigayiya Hasiya...!
    Hannun Gwaggo Binta na rawa ta kamo na Ummi tana mai rike kafadarta da hannun damanta.
  "Sannu Hasiya, shakka babu wannan jininmu ce diya ga diyata Hasiya, ashe da rabon mu k'ara sanyaki a idanunmu?"
Sai ta janyota jiki tana hawayen farinciki ga kuma bakinta da ya k'i rufuwa don murna.  
   "Ke ce?"
Cewar Abubakar da mamaki yana nunota da yatsa, hakan yasa duk wanda ke fahimtar hausa sosai ya kalloshi don ba kowa cikinsu ne ke jin hausa ba, Malam Balarabe da Alhaji Kabiru har suna hada baki wajen fadin.
  "Ka ta6a ganinta ne?"
Ya jinjina kai yana murmushi mai bayyana hakora.
"Tabbas Dad ita nace maka na gani fa a gidansu Abban Kano mai kama da Inno. Saidai..."
Sai kuma ya yi shiru, har lokacin bai bar mamaki ba. Kallon Ummi kawai ya ke yi kamar Innonsa, Innonsa Zahra mai matukar kaunarsa, sun shaku sosai, ayi wasa ayi dariya, yana mata kallo kamar wata sa'arsa kuma kanwa gareshi don koda zata girmeshi ba da wasu shekaru na azo a gani bane sannan gajeriya ce bata da jikin girma. Sune har guje-guje, komai na shawararsa idan ya dauko to fa da Inno zasuyi ta, sau da yawa kafin iyayensa su san wani abu nashi, Inno ta sani don gaba daya tare suke zaune har Gwaggo Binta a gidan Baffansa Kabiru.
   Bai mantawa ana shirin bikinta ta yi bankwana da duniya, mutuwar da sosai sun ji ta a zukatansu don har kwantar da shi ta yi, hakanan mahaifiyarsa Hajiya Salma ita kanta saida ta yi kamar ba zata rayu ba tsabar razanar da ta shiga sanadin mutuwarta. To me ya kaita Kano? Me kuma ta ke yi gidan su Ihsan? A ina Faruk ya ganta ya ce yana so?
   Wannan shine tambayoyin dake  yawo a kwanyarsa da ba shi da mai amsa mishi. 
  Kowa a wajen ya cika da mamaki banda wadanda sukasan silar zaman Ummi a Kano da Abuja.
Chapter 93 · 0% Book details