← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 116

Sashe 72

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

  Yana zaune yana shan(coffee) alokaci guda kuma ya lula duniyar tunani har Alhaji Kabir na mishi magana sam bai ji ba. Ya dan ta6o shi.
  "Abubakar." Ya dan dubeshi sannan ya sauke ajiyar zuciya.
"Naam Baffa."
"Tunanin me ka ke yi ne har ina magana ba ka ji ba? Me kuma ya faru? Ko akwai wata matsala?"
  Ya girgiza kai.
"Aa, saidai Baffa jiya naga wata yarinya mai kama da Inno sak, na yi mamaki."
    Alhaji Kabir ya dan yi shiru kafin kuma cikin rashin fahimta ya ce.
  "Ikon Allah, watakil kawai kamanni ne. Kasan ana samun haka sosai."
Abubakar ya girgiza kai.
"Wannan kamar har ta so ta 6aci, ba don sanin da na yi cewar Inno bata raye ba da sai na ce itace, anya wannan itama ba daga Gombe ta fito ba?"
  Shi dai Alhaji Kabir abin mamaki kawai ya ke ba shi, wacece wannan da har ya ke had'ata da danginsu na Gombe?
Har suka bar Kano Abubakar bai kara sanyata a idanu ba wanda ba haka yaso ba. Yaso ko hotonta ne ya daukarwa mahaifinnasa ya ganta.

                 ***   ***   ***
A satin Ummi ta soma zuwa islamiyya yare da Ikram duk kuwa da cewar Ikram din bata so hakan ba, saidai dadinta daya, ita tana aji na karshe na yan hadda ita kuwa Ummi aji biyu aka sanyata. Ta hadu da wata daliba mai kokari, Husna, wacce a kwana biyu kacal jininsu ya hadu da ita. Ita din diyar wani mai kudi ce don kuwa makarantar ta masu da shi ce, wayayyiya ce amma ba irin wayewar nan ta banza ba. Har musayar lambar waya sukayi. 
    Ranar juma'a Yaha ta dira a Abuja, Hajiya Babba har tasha ta sanya direba ya daukota. 
   Wannan ne zuwanta na farko gidan Hajiya Babba, lallai Mami ba cikin gida take ba, ga inda gida ya ke. Bayan gama cin abincinta ta shiga dakin Ummi inda anan ne zata kwana. Yaha baki ta saki tana mai karewa ko'ina kallo har sadda Ummi ta shigo dakin ta ajiye mata robar ruwa a gefen gado. 
   Ta bi Ummin da kallo.
"Ummi, wannan dukiya har haka?"
Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da ta san abin cewa ba. 
   "Kinsan fa ban sanar da Saude batun zuwanki ba don kuwa sam bata kaunar ki je."
  Tasan hakan daman ba wani sabon abu bane, matar da ta yi mata mummunan rik'o ina za ta amince da k'ara sanyata a ido? 
  "Ina Minna ta kirani ta jaddada min cewar kada na yarda ki je Ringim, acewarta ko nawa nake so zata dunga bani cikin albashinki, ita dai fatanta kada ta budi ido ta ganki a Ringim, ta ce na yi mata wannan taimakon har zuwa sadda wani buri nata a kanki zai cika."
  Gaban Ummi ya fad'i, wannan tsana har haka? Yanzu ko me zuwan nata zai haifar? Ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa. 
   "Idan ma wani mugun abun ne ki kwantar da hankalinki, Allah zai kareki."
                ***   ***   ***
                  RINGIM
((Pls kuui manage))

DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

91
Chapter 72 · 0% Book details