← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 116

Sashe 104

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kinga yanda Allah ke jarraba bayinSa ko Ummi? Kiga dai yanzun kin zame musu wata abar, kinga ikon Allah wannan karon wajenki Ikram ke neman alfarma ko? To don Allah kar ki rikesu da komai duk kuwa na tabbatar ba ki rikesu a rai ba. Yanzu ni bansan me zan ce miki ba akan wannan abu, saidai gaskiya inajin tausayin Ikram kamar yanda rayuwar Gidado da Hafsa ta burgeni, anya kuwa ba za mu yi musu shishshigi ba?"
Ummi ta dan cize le6anta na k'asa gami da mikewa tsaye daga zaman da ta yi a gefen gado. 
   "Shine nima wallahi Anti, wannan ne matsalar, da ma ace Yaya Gidado ba shi da mata ne, da babu abinda zai hanani sanarmishi, kawai..."
  "Ko za ki jarraba fadawa Yaya Abubakar? Watakil shi yasan shawarar da zai bada."
   Ta gyada kai jin abinda Amina ta ce.
"Kuma fa hakane."
Suka tsaida wannan shawarar kafin kuma suyi sallama ta yi kiran Abubakar. Bai daga ba sai ya yi saurin yankewa ya kirata. 
"Innota ya akayi?"
Murmushi ta yi sannan ta gaisheshi ya amsa gami da tambayar lafiyarta da ta maigidan.  Bayan gama gaishe-gaishe ne ta fadamishi maganar Ikram, ta kara da fadin.
"Ni kuma wallahi ina kunyar Anti Hafsa, banaso wani abu..."
  "Kar ki damu, shi aure ai nufin Allah ne, idan Allah Ya yi sai ta zama matarsa to zata zama din. Yanzu dai abin yi bai wuce na a sanarmishi ba, ai ko don halaccin da mutanen nan suka yi mana na rikemana ke amana ba tare da sunsan komai naki ba ya kyautu mu yi musu abinda yafi haka muddin bai fi karfinmu ba, zan nemi shi Gidadon, batun kuma wai Hafsa karki damu kanki, Allah ne Ya bamu damar yin fiye da daya matukar zamu yi adalci tsakani." 
   Ita dai ta yi tsuru da idanu ta rasa abin cewa banda um don kuwa tsoronta bai wuce daukar da Hafsa zata yi mata ba. Abubakar ya ce kada ta damu daga haka ya tambayeta ko akwai wata matsalar ta amsa da babu sannan suka yi sallama. Koda ta shaidawa Amina yanda sukayi Amina ta amsa da cewa.
"To, sai mu tayasu da addu'a, idan akwai kaddarar aure tsakaninsu, Allah Ya hadamishi kansu, Allah Ya kawo lamarin da sauki."
"Ameen." Daga haka sukayi sallama.

  A washegari kuwa Abubakar ya kira Gidado ya sanarmishi, dariya Gidado ya yi don zatonsa wasa kawai Abubakar ke yi.
"Banda abinka, ina diyar birni wacce ta tashi cikin daula ina ni dan kauyen Jar Kwami? Haba dan uwa, gyara zancenka."
   "Kada ka dauka wasa na ke yi Gidado, I'm serious. Ka yi tunani akai please."
Gidado ya yi shiru, daman fa ya tsargu da irin yawan kallon da ta ke mishi hakanan kuma da yawan murmushinta gareshi saidai ba shi da kakkarfar hujja, to shi me zai iya yi mata? Alal hakika babu wacce ya ke so kamar Hafsa, kuma ace ko yanzu ko shekara basu yi ba ya tashi neman aure? Auren ma wacce yasan zai sosa zuciyarta fiye da auren wata a kauyennasu? Ya girgiza kai tamkar Abubakar na gabansa.
  "I'm sorry Abubakar, gaskiya..."
"Karka yanke hukunci da gaggawa mana, ka yi tunani don Allah, ko don irin rikon da suka yiwa Ummi ai..."
"Ya isa, karka sanyo batun wannan don Allah, ana magana ne fa ta aure wanda ya kasance raayin mace da namiji."
"Idan Allah Ya kaddaro fa?" Abubakar ya tari numfashinsa. 
  Ya sauke ajiyar zuciya wanda har kunnen Abubakar.
"Wannan kuma kaddara ce, sai ayi."
"To haka nake so ka saka a ranka, idan Allah Ya kaddara aurenka da Ikram sai fa anyishi koda ace babu son ranka ciki. Ka barwa Allah za6i sannan don Allah zan aikomaka lambarta ka dunga kiranta, mai sonka ai yafi makiyi, don Allah dan uwa ko gaisuwa ce ka daure ku dunga yi, yarinyar na wahala ne akanka."
Dariya Gidado ya yi don abin mamaki ma ya ke ba shi, to me ta gani a jikinsa da har ta ji ya burgeta?
  Haka Abubakar ya cigaba da yi mishi magiya har saida ya aminta da hakan sannan suka rabu. Ko mintuna uku baayi ba ya aikomishi lambar ta whatsapp. Koda ya adana ta cikin wayarsa, ya bude hoton da ta dora, hotonta ne na bikin Haidar da Intisar, da k'ibarta a hoton, tana dariya ta rungume Amarya da Ango aka dauka, ya kuramata idanu, bata da makusa saidai bai ji wani sonta a ransa ba illa tausayi da ta bashi na kamuwa da son wanda ba ya sonta. Ya yi mata sallama gami da cewa.
"Kina magana da Gidado, ina fatan mutanen Abuja lafiya?"
  Daga haka ya rufe wayar ya maida aljihu inda ya cigaba da sauraron (customers) dinsa da ya bari suna cinikayya da yaron shagonsa. 
   Sak'on bai iso ga Ikram ba sai Magriba bayan ta dawo daga islamiyya, ta zauna da zummar duba litattafan makaranta sakamakon jarabawarsu ta karshe da ke k'aratowa, ta janyo wayar ta bude. 
   Ta yi mamakin ganin bak'uwar lamba ta whatsapp dinta, saidai me? Tun bata bude gaba daya ba idanunta ya hango mata sunan da ya ambata nasa, wato Gidado sai kuwa hotonsa da ya dora, hannu na rawa yayinda gabanta ke bugu da sauri-sauri ta soma da budo hoton don gaskatawa, ai batasan lokacin da ta diro daga saman gado ba tana buga tsalle hakanan hakoranta a waje ta kasa rufe bakin tsabar murna har da hawaye farinciki, ta dafe kirji. Oh yanzu ya zata ji idan ya furta yana sonta tunda ganin ya kulata kadai ma ya sanyata farinciki, to wai ma a ina ya samu lambarta? 
'Ummi.' Cewar wani 6angaren zuciyarta. 
  Ta k'ara tsalle tana ihun farinciki wanda batasan da karfi ta ke yi ba saida aka murda kofar aka shigo.
"Lafiya?" Jin muryar Hajiya yasa ta nufarta gami da rungumeta tana murna. 
Hajiya cike da mamakin na abinda yasa Ikram wannan farincikin ta dagota daga jikinta tana dubanta, can kasan zuciyarta hamdala ta yi domin kuwa ta mance rabonta da ganin irin wannan fuskar fara'ar ta Ikram, to amma hawayen na menene?
  "Meyafaru ki ke mana ihu?"
Cikin zak'uwa ta ce.
"Yau Yaya Gidado ya yimin magana, ki tayani addua Allah Ya..."
  Dif ta yi don gaba daya ta mance gaban wacce ta ke, idanunta sun riga sun rufe. Ita kuwa Hajiya ta tsareta da kallo, duk duniya Gidado biyu ta sani. Da wani kawunsu na Adamawa wanda tsoho ne, sai kuwa Gidadon wajen su Ummi. 
  "Wane Gidadon ki ke magana akai?"
Ta hau kame-kame, bata yi zato ba ta ji Hajiya ta zare wayar daga hannunta, kafin ta yi wani yunk'urin ta budo. Ta yi shiru tana duban hoton kafin ta dubi Ikram cikin sanyin murya mai nuni da karaya ta ce. 
"Shi Gidadon ne ke sanyaki rama da tunani dama? Kinsan waye Gidado wajen Ummi kuwa?"
  Shiru Ikram ta yi babu amsa ga kunya da ta cikata, wani murmushi na manya Hajiya ta yi. 
  "Saidai kuma na ji ance yana da mata, kina da tabbacin za ki iya aurensa ki zauna a Jar Kwami? Sannan za ki iya hakurin zama da matarsa?"
  Sai lokacin  ta iya dago kanta ta dubi mahaifiyarta idanunta na zubda ruwan hawaye. 
  "Duk abinda ki ka lissafo Hajiyarmu, babu daya da ba zan iya jurewa ba, ni nasan harda hakkin Ummi ya kamani, saidai wallahi a yanda nake ji a zuciyata, kamar ba zan iya auren wani ba bayan Yaya Gidado."
  Ta karashe cikin kuka, zuciya irin ta *MAHAIFIYA* nan take ta ji tausayin diyarta ya mamayeta, ta share mata hawayen gami da mikawa mata wayarta tana murmushi. 
  "Allah Ya za6a abinda yafi alheri gareku."
  Daga haka ta juya ta fice, Ikram murmushin jin dadin ta saki, ko babu komai ta ji dadin kyakkyawar adduar da ta fito daga bakin Mahaifiyarta. Ta karasa saman gadon ta zauna sannan ta bud'o sak'on. Sallama ce da gaisuwa, nan take ta ba shi amsa, ai ko babu komai samun lambarsa da ta yi cikin wayarta, abin alfahari ne, zata cigaba da janyo hankalinsa da dabara hakanan zata cigaba da tsananta addu'ar neman za6in Allah. 
Chapter 104 · 0% Book details