Sashe 108
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Ko bayan wannan, yan aiki mutane ne kamar kowa, hakazalika suma suna da nasu daraja da k'imar, da yawa cikinsu kan fito aiki bisa kaddara ba da son zukatansu ba, wasu anfi karfinsu ne wasu kuwa halin rayuwa ce. Ni Ummi bana fatan ranar da zata zo na wulakanta wani DAN ADAM a duniya, da yawa suna kuskure, sukan dauki kansu wasu har su dunga wulakanta masu tayasu hidima don kawai tak'amarsu biyansu su ke yi, sai yaronki karami ya budi baki ya zagi dattijuwar da ko ke ta haifa amman ba zaki kwa6eshi ba kasancewar kina mata kallon yar aikinki, sai ya zagi direba ko maigadinki duk ba za ki ji ko darr ba, asalima har ya kai ga kin shigarwa danki don kawai kina yi musu kallon kaskantu, watakil kuma sun fiki matsayi a wajen Allah. Ba ma akan masu aiki ba, kowaye kada ka wulakantashi don shakka babu bakasan mai yi maka rana ba, ko ya ya, bana mance halacci."
Fadila da Jidda suka k'ulu da maganganun Ummi, musamman Jidda wacce ke ji kamar da ita ta ke, basu kadai ba har da wasu cikin gayyar sunan wadanda sun kasance suma sukan dauki yan aiki ba komai ba face kaskantu maganar Ummi ta shigesu, nan kuma wasu suka hau fadin ai yan aikin ma suna suka tara akwai mugaye. Ita kuwa Fadila bata kara cewa uffan ba don ta cika da mamakin yanda har Ummi ta yi kaurin wuyar mayarmata da martani.
"Ku bar ganinta haka, yar aiki ce a baya shiyasa ta fiye wannan zakalkalewar, ai duk inda mutum wanda bai saba da arziki ba ya ke to fa sai kun gani ko a jikinsa ko furucinsa." Cewar Jidda a fusace.
Ummi ta dubeta, kamar ta ce wani abu sai kuma ta hadiye kawai tana murmushi.
"Kai don Allah Anti Jidda." Cewar Intisar kenan, Jidda ta watsamata mugun kallo.
"Na ambaci sunanki?"
Ta rausaya kai.
"Ko ba don wani abu, ku yi duba fa da cewar cikin azumi ake..."
"Please ya isheni, wani abin nace?" Jin haka Intisar ta ja bakinta kawai.
Wata hamshakiyar mace da ta hade cikin wani tsadadden leshi ta tofa.
"Kwarai Jidda suna haka, don wallahi wata yar aiki da kawata Mariya Sadik ta ta6a yi, ai kinsanta, yarinyar a dakin mijin ta kamata. Ai babu butulu kamar dan aiki saidai mata mu kiyaye."
Nan kuma babin ya koma hirar yan aiki, Ummi ganin abin nasu kamar da biyu ne, yasa ta mikewa ta bar dakin zuwa falo, Intisar da Baraka suka biyo bayanta har Ikram don abin ya 6ata ransu suma. Ta nunamusu ba komai ganin yanda suka damu. Ita kuwa damuwarsu akai ma kadai ta sanya komai gogewa a zuciyarta.
Sai Magriba Faruk ya zo daukarta, anan ya sha ruwa da su Haidar hakanan suma nan ciki suka sha ruwa sannan ya shigo ya ga bebi, anan ne Fadila da Jidda suka kai mishi k'arar Ummi akan ya ja mata kunne. Ya cigaba da danne wayarsa yana yiwa yarinya hoto, gefensa Haidar ne zaune sai Ridwan wanda shima bai jima da zuwa ba.
"Wai muna magana ka maidamu wasu shashashai." Cewar Jidda mai saurin fusata.
"Wai meyafaru? Me Ummin ta yi muku?"
Cewar Dakta yana duban Jidda. Jidda ta yi kwafa.
"Mene idan ba rashin kunya ba har tana kiranmu masu raina mutane. Yaushe kan mage ya waye da har raini zai shiga tsakaninmu?"
Faruk ya bar abinda ya ke ya dubi Jidda ransa a 6ace kamar ya yi magana saidai shigowar Ummi da Intisar falon Haidar ya katseshi, sanye ta ke cikin wani leshi bak'i mai adon orange flowers, sai mayafinta (orange) da ta yafa, hakanan jakarta da takalminta marar tudu. Idanunta akansa suka soma sauka.
Wani sassanyar murmushi suka sakarwa juna kafin ta karaso ciki ta gaida Angon karni da Dakta.
Faruk ya mik'awa Dakta bebin.
"Bari mu wuce."
"Ai daman fuskar da ta samu wajenka ne yasa ta ke..."
"Ya isa! Haba!" Cewar Ridwan ga Jidda wacce ke zak'alk'alewa.
"A'a Dakta, babu batun ya isa fa, magana ta gaskiya." Cewar Fadila tana taunar cingam da kallon banza.
"Ummi me ya hadaki da yan uwanki?" Cewar Dakta kenan, Faruk na tsaye hannuwa ciki aljihu kawai yana kallonsu.
Ta dan murmusa don ita bata ga abin daukar zafi ba.
"Ba abinda ya hadamu."
"Karya ki ke yi uwar kissa." Cewar Fadila.
"Ya isa, Intisar me ya hadasu ne?" Cewar Dakta.
Tiryan-tiryan ta fadi duk yanda aka yi, Faruk ransa ya yi mugun 6aci ya soma magana.
"Ku rike girmanku, ina girmamaku, kada ku janyo abinda zaisa nabar ganin girmanku. Duk wacce ta kara cin zarafin matata bazan lamunta ba, ko wacece cikinku komin girma da kimarta da nake gani zan yi watsi da shi wallahi!"
Jidda da Fadila ba bakin magana, shiru sukayi sai faman harararsa sukeyi amma ba bakin magana, ko babu komai yana da kwarjini.
Haidar ya dubeshi.
"Ka yi hakuri mana. Gaskiya ba ku kyauta ba Maman Ma'aruf, kune masu laifi ba Ummi ba, sai ku duba matsayinta a yanzu a Family namu, ku dunga sakaya bakinku."
Shima Dakta cikin tsananin 6acin rai ya hau zazzagawa matarsa fad'a, Ummi dai ganin mijinta ya nufi hanyar fita, itama ta yi musu sallama ta bi bayansa.
A mota ta sameshi zaune yana jiranta, ta shiga gami da dubansa, idanunsa sun kada bai ko dubeta ba ya figi motar a guje, ganin Batul yasa ta yin shiru ba don taso ba, duk da haka saida ta mishi magana.
"Don Allah ka rage gudu."
Ta fada gami da dafa hannunsa dake rike da sitiyari. Ya lumshe idanu yana mai jin zafin abinda ya faru, ganin ta damu yasa shi sassauta gudu har dai suka isa gida, Batul ta yi shiru tana mai tausayawa uwar dakinta don kuwa ta ji kadan cikin abinda ya faru.
Koda suka isa, dakinta ta nufa. Ta cire mayafi kenan ta isa gaban madubi da zummar cire dan kunne da sark'a ya shigo, ta dubeshi ta madubi suka hada ido. Murmushi ta sakarmishi a kokarinta na 6oye damuwarta. Karasowa ya yi da sassarfa ya rungumeta ta baya yana sauke ajiyar zuciya idanunsa a runtse.
"I'm sorry." Ya fada a hankali, ta lumshe idanu, sai lokacin zuciyarta ta raunana, ta ji kamar ta zubar da hawaye saboda tsananin farinciki na samun miji kamar Faruk mai so da kaunarta.
Ta juyo ta dago fuskarsa gami da girgiza kai yayinda hawayen da ta danne suka shatato.
"Haba FAR HAS, don Allah ka daina inajin wani iri wallahi."
Ta rungumeshi tana hawaye yayinda lokaci guda ta ke murmushi mai bayyana hakora na farinciki.
"Ko babu komai wannan kaunar da ka ke yimin ta zarce komai a wurina, ta isa wankemin dukkan wani 6acin rai dake zuciyata. Wallahi na yafemusu bazan kuma rikesu da hakan ba, DAN ADAM ajizi ne."
Ya dago kanta yana murmushi gami da share mata fuska.
"Shiyasa nake kara sonki Ummina, halayenki sunfi komai burgeni. Na damu ne don nasan koda ya miki ciwo ba za ki bari na fahimta ba, cin zarafi ne abinda suka yi gareki wanda wallahi Allah idan suka ce haka za su dunga yi gareki bazan lamunta ba, zan jure komai idan ni ka yiwa amman banda abinda ya shafi lamuranki. Kema kin sani ko?"
Tun soma maganarsa ta zubamishi idanu tana murmushi gami da jin tamkar ta hadiyeshi don so, ya hure mata idanu hakan ya basu dariya.
"Eh mana naga kamar mai shirin hadiyeni, wannan kallo haka?"
Ta bugi kirjinsa tana kukan shagwa6a.
"Kai don Allah."
Ya ja karan hancinta yana dariya kafin ya taimakamata da abinda ta soma kokarin yi.