Sashe 75
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Saude tana shiga gidan Bokanya ta yi turus sakamakom ganin Habiba da ta yi zaune itama tana faman kuka. Habiba na ganin Saude ta mike da sauri ta nufi wajenta.
"Yanzu Mai Bori ta ke gayamin kin tafe daman, munyi sake Habiba, lamura sun yi 6acin da gyarasu sai Bokanya. (Wa'iyazubillah)"
Saude ta wuce zuwa gaban Bokanya ta zauna. Bokanya tana dubansu tun soma maganganinsu tana dariyar k'eta. Kafin Saude ta ce komai ta rigata.
"An sakeki Saude, Balarabe ya miki saki biyu ko? Hahaha."
Ta kyalkyale da dariya, Habiba ta razana da jin wannan, ta zaro ido ta dubi Saude ta koma duban Bokanya.
"Kunyi kuskure babba! Kun kasa kiyaye dokokina, yanzu ku ka soma fuskantar kalubalen rayuwa! Babu wani abu da zan iya, lokacin afkuwar ABINDA AKE GUDU ya iso!"
"Karya ki ke wallahi! Ke din banza, idan ba ki yi mana aikin ba kin dauka babu dubunki?" Cewar Saude kenan wacce sam ba cikin and hayyacinta ta ke ba. Ita kuwa Bokanya dariyar keta kawai ta ke yi babu kakkautawa.
"Allah Ya isa tsakaninmu da ke, ashe bokancin naki ya k'are tunda ki ka kasa gyara abinda ki ka san zai 6aci."
Cewar Habiba itama cikin kuka. Sai lokacin Bokanya ta dan tsagaita dariyarta tana mai duban Habiba.
"Kun yi kuskuren zagina! Sakamakonku zai biyo baya! Ke Habiba! Ke ki ka kashe Hasiya! Tare da taimakon Saude! Diyarki tana can ta fad'a harkar madigo! Aurenta zai mutu! Sai na karya duk aikin da na yi mata! Sai kun koma abin tausayi. Asirinku sai ya tonu! Ku tashi ku bar nan azzalumai!!"
Ta karashe fuska a daure, suka mike don ko damar bata hakuri basu samu ba, Bokanya ta karanto musu laifinsu wanda duk a zatonsu asirinsu ya rufu ruf babu ta inda zai fito don kuwa su biyun cewarsu sun aminta da juna.
Suna tafe ga duhun Magriba, Saude fadi ta ke.
"Allah Ya isa tsakanina da ke, duk kece ki ka soma kaini wajen bokanyar nan yau ga shi nan abinda ya afku. Ga shi yau aurena ya mutu."
Habiba da ke kuka da tunanin tashin hankalin da ke gabanta na mutuwar auren diyarta ta dubeta.
"Au, haka ma za ki ce? Kin mance dadin da ki ka ji a baya ta sila ta shine yau da akayi miki ba dadi za ki zageni? Lallai DAN ADAM mai mance halacci, DAN ADAM butulu, ban ta6a kashe rai ba sai akan kishiyarki, shi ne tsabar son ki nunamin ke kina cikin masu mance halacci za ki ce na cutar da rayuwarki? Ai babu wacce aka cuta sama da ni."
Wannan kalamin na Habiba ya tunzura Saude, nan suka hau cacar baki suna tafiya, wannan ta fad'a, wannan ma ta maida martani, karshe haka suka rabu baram-baram, Saude kai tsaye ta kama hanyar gidan kawunta wanda shi da banza duk daya ta daukesu, sai kuwa a yau din da ta ke neman agajinsu kan su rok'i mijinta akan ya maidata dakinta.
Habiba hankalinta idan ya yi dubu to fa ya tashi, babu abinda yanzu ke damunta kamar batun diyarta Dija, yanzu idan auren ya mutu ta yi ya ya? Ta dauki waya da zummar kiranta saidai ko kusa batasan yanda ake sarrafa wayar ba, sau da yawa idan za ta yi kira saidai ta shiga makwafta budurwar gidan ta danna mata. Tana nan zaune duk tunaninta ya jagule, Malam Yahuza ya shigo gidan da sallamarsa saidai bata ko amsa ba.
"Habiba, lafiyarki kuwa ina sallama ba ki ko kalleni ba balle ki amsa?"
Sai lokacin ta dubeshi gami da jan tsaki.
"To menene kuma? Za ka cikani da hayaniya, mtsw."
Ta karashe gami da jan tsaki.
"Habiba ni ki ke yiwa tsaki kuma? Toh bazan dauki wannan rashin kunyar banzar ba, ki kiyaye!"
Sakato ta yi tana duban mijinnata, yau Yahuza ne ya samu 'yancin d'aga murya sama da nata? Tabbas Bokanya dagaske ta soma karya dukkan ayyukan da ta yi musu, ta yi tsuru don tsoro ma ya bata, ya kammala komai ya dubeta.
"Ina abincina?"
A sanyaye ta amsa.
"Ai ba ka bada kudin cefane ba."
Ya yi kwafa kafin ya mike ya fice zuwa masallaci. Ta bishi da kallo kafin ta dora hannu a ka ta hau kuka.
"Oh ni Habiba wannan wace irin bak'ar rana ce gareni?"
Ta fad'a a fili babu mai amsa mata.
Ummi farincikinta ba ya misaltuwa a wannan rana, ta yi sallar Magriba anan tsakar gidan, saida aka yi sallar Isha'i sannan Malam Balarabe ya shigo rike da leda, da sauri ta mike ta kar6a suna duban juna da murmushi saman fuskar kowannensu. Kauna ta da da mahaifi shi ke yawo a jinin jikinsu. Tarr ya ke ganin diyartasa sakamakon wutar lantarki da suke da shi don a baya sosai suna samun wuta a kauyen, sai ayi kwana biyu ba'a dauke ba, koda kuwa an dauke, to fa babu jimawa za'a maido musu, yanzun kuwa da aka shiga yanayi an dan rage samu kamar da.
"Sannu da zuwa Babana." Ta karashe cikin jin wani irin sanyin dadi a zuciyarta, yau ga ta ga mahaifinta kamar yanda ta ke yawan mafarkin ta gani har ya damu da ita ya sakarmata fuska. Kwalla ta cika idanunta sa'ilin da ta ke kokarin ajiye ledar ya dakatar da ita da fadin.
"Sannu 'yar Baba, dauko faranti a ciki nama ne da gurasa ku ci."
Ta bi umarninsa, ta kawo ta juye, ta dubeshi.
"Baba mu ci."
Yana murmushi lokacin da ya ke share hawayen da suka zubomishi ya soma ci shima. Mariya itama ci ta ke sosai don daman da yunwarta.
Bayan sun kammala ta debomusu ruwan randa mai sanyi suka sha kafin su yi zaman hira. Malam Balarabe ya dubi Ummi.
"Kamanninki da mahaifiyarki har ya 6aci, tamkar an tsaga kara an karya, hatta sanyin muryarta."
Ya danyi shiru kafin ya numfasa.
"Allah Ya jik'anta."
"Amin." Ummi ta amsa jikinta a sanyaye tana dubansa kafin ta ce.
"Baba kana da hoton Ummana?"
Ya gyada kai yana murmushi.
"Bazan rasa ba saidai yanzu nasan yana cikin kaya, sai zuwa gobe zan dubo miki. Bani labarin zamanki a hannun bayin Allahn nan."
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta soma labartamishi tun farkon zuwanta har kawowa yau da suka taho nemawa dansu aurenta.
Malam Balarabe dake ta faman jinjina kai, wani abin ya yi murmushi ya ce"Allahu Akbar" wani abin kuwa ya yi hamdala idan ya ji. Bayan ya kammala ya dubeta.
"Babu abinda zanyi na biya mutanen nan da shi sai addu'a. Hakika sunyi abinda Allah baiyi ni zan miki shi ba. Babu abinda yafi faranta raina kamar sanyaki a makaranta da suka yi basu barki kin zauna da jahilci ba. Haka kuma rayuwarki bata lalace ba, har kuma suka tako daga Abuja zuwa kauyenmu don kawai su nemawa dansu aurenki, tsakanina da su sai addua, Allah Yasa aljanna ce makomarsu, in sha Allahu ba ki da miji sama da Umar. Zuwa yanzu na dakatar da maganar don nafison ki soma sanin dangina da na mahaifiyarki, ayi aurenki kina cikin dangi. Itama Amina Allah Ya yi mata albarka, Ya bata mijin da zai rik'eta rik'on Amana."
"Amin Baba." Ummi ta amsa da murmushi mayalwaci saman fuskarta, ai ko don zagin da su Ihsan ke mata, zata so ta hadu da dangin iyayenta, ta ga gatanta. Sai kuma ta dubi mahaifinnata, lokacin Mariya ta soma bacci saman tabarmar.
"Baba inason jin tarihinku da Ummana, ku din 'yan ina ne?"
Malam Balarabe ya murmusa kafin ya ja baya ya jingina da bango ya soma magana.
"Yanzu za ki ji takaitaccen tarihinmu da Ummanki, sauran idan munje kya ganewa idanunki."
Suka yi murmushi tare kafin ya cigaba da magana....!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
93
((Wannan shafin naku ne yan uwa sis Aisha Samarou & Maman Adil))