← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 116

Sashe 40

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

    Tafe take a hanyarta ta zuwa wajen(garden) don dauraye tsummokaran da ta kammala gyaran dakunan Hajiya da su. Kallon benen da zata yi ta ganshi yana saukowa shima a daidai lokacin ya bar duban wayarsa ya maida ga hanya alokaci daya kuma yana kokarin sanya wayar aljihun wando. Karaf idanunsa cikin nata, yanda ta tsaya bata motsa ba, shima ya tsinci kansa da mutuwar tsaye. Abu biyu ke yawo a kwakwalwarsa. Buri na son kasantuwar abinda ya ke gani yanzu tamkar mafarki da kuma tambayar daman tana gidan? 
  Dakyar ya yi jarumtar k'arasawa har gabanta, alokacin ita kuwa ta sunkuyar da kanta cike da matsanancin fargabar abinda zai k'ara ce mata.
   Saida ya kai dab da ita har suna jin numfashin juna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya matsa, ya tabbata ita din ce ba gizo ta ke mishi ba. A hankali ya matsa baya, cikin rawar murya ta gaisheshi bayan ta durkusa. Ya amsa cikin jin wani irin nishadi a ransa, ta mik'e tsaye, tana shirin barin wajen maganarsa ta dakatar da ita.
  "Daman ba ki tafi ba?"
  Ta dan saci kallonsa, murmushi ta gani dauke saman fuskarsa wanda ya kara fiddo kyawunsa.
  "Eh."
  "Saboda ni?" Ya fada a tausashe bayan ya dan rankwafo da kansa yana kallon fuskarta.
   Ta k'ara satar kallonsa, shi dinma bai kauda nasa idanun daga kanta ba. Ta ji wani iri a jikinta, wai saboda shi. Maganar ma nauyi ta yi mata, ta kauda idanunta.
   "Mami ta ce na zauna zuwa wani lokaci."
   Ya ji dadin maganar, ba zai iya misalta farin cikin da ya shiga sanadin hakan ba. Ya dubi hanya babu wani ko wata da ke tahowa sannan ya dubeta.
  "Ummi, yau kenan za ki tayani hira?"
Ta zaro ido batare da ta dubeshi ba, cikin sauri ta girgiza kai.
  "Kayi haku..."
"Shiit." Ya dakatar da ita ta hanyar dora yatsansa a saman le66ansa.
  "No please, karki hana zuciyarki abinda ta ke so mana Ummi. Ko kina so wani abu ya faru da mu sanadin hana zukatanmu farin cikinsu?"
  Ba amsa sai idanunta da suka kawo ruwa, ya mik'e da rankwafawar da ya yi. 
   "Shikenan, ki tafi, mu had'u wajen pool."
   Daga haka shiru ya biyo baya, karshe ma ya juya ya cigaba da tafiya. Da ido ta bishi, ta tabbatar shi babu abinda ya ke tsoratashi, kamar yanda babu matsalolin da ya ke hangomusu, ita kadai ta damu da duk wadannan. 
  Koda zai shige saida ya juyo domin ganin yanayin da ta shiga, suna hada ido ta juya da sauri ta soma tafiya. Murmushi ya saki kafin ya karasa cike zuciyarsa cike da tsantsar farinciki. Daidai da Ikram da Ihsan sun ga chanji yau wajen yayannasu, don kuwa biyemusu ya yi akayita hira da dariya. Ihsan ji ta ke tamkar ta buga tsalle don murna da farinciki, yau ita Faruk ya dage hira da ita? Tabbas shawo kansa zai zo mata da sauki muddin ya d'ore a haka. 
   A yan kwanakin da ta yi tsaf Hajiya Babba ta fahimci inda ta dosa, a farko bata gaskata Ikram ba da ta sanarmata cewar Ihsan na son Faruk ba, saida ta lura da kanta. Abin ya yi mata dadi, zata so hakan ta kasance, saidai d'annata ne batasan abinda ke ransa ba. A ganinta da wuya ya kaunaci yarinya mai rawar kai irinta, hakanan Ihsan sam bata da hakuri, ga saurin fushi. A raayin Hajiya Babba, bata kaunar abinda zai damu 'ya'yanta, kusan halinsu daya da Mami na son 'ya'ya.

   Acan kuwa Ummi tana isa ta zauna saman kujera gami da zubawa famfo ido, hankalinta gaba daya ba a wajen ya ke ba, ya tafi gaba daya ga tunanin Faruk.
'Dagaske fa ya ke.' Shine abinda ta fad'a a ranta, tabbas Faruk dagaske ya ke, asalima babu wani alama na tsoro ko fargaban abinda zai biyo baya. Yanzu ya zata yi? Bai bata damar cewa ba zata zo ba, ya riga ya yanke cewa lallai kawai ta zo ta sameshi. Ta riga tasan duk ranar da wani a gidan ya gano to fa tashin hankalin da zata shiga ba k'adan bane. Tagumi ta zuba tana tunano da Antinta, yau ne rana ta farko da ta soma jin bukatar waya a rayuwarta, ayau inda ace tana da  waya, tuni zata yi kiranta ta bata shawarar da ta dace. Ta ja guntun tsaki sannan dakyar ta mike ta soma aikin da ya kawota, saida ta kammala ta shanya sannan ta koma ciki.
    Misalin biyar na yamma tana zaune a k'asan bishiyar mangwaro tana wasa da ganyen, hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin Faruk, banda murmushi da wani annuri, baka ganin komai saman fuskarta. Ita tasan tana sonsa, bata ta6a son wani d'a namiji ba sai shi, saidai kawai bambancin dake tsakaninsu, shi kadai zai hanasu aure. 
   Ta jima kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta ga inda ta ji sautin dariyarsu. Ihsan ce da Ikram dukkansu sanye da kananun kaya, riga da siket, sun nad'e kansu da karamin dankwali. Hira sukeyi abinsu da dariya har suka iso wajen motar da tun zuwansu Abuja, Faruk tasan yana hawanta. Suna hada ido da Ihsan ta maka mata harara, Ummi ta kauda fuskarta. 'Kanki ake ji.' Shine abinda ta fad'i a ranta. 
  "Har kun fito?" Tattausar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Ta so ta jure kada ta kalleshi, saidai hakan ya k"i yiwuwa, ji ta yi tamkar bazata nutsu ba idan bata ga tasa shigar ba. 'SubhanAllah!' Shine abinda ta fad'i a ranta. Riga tshirt ce yasa kalar(golden, long sleev) mai mannuwa a jiki, sai (blue jeans) ya sanya gilas dark brown, agogonsa na k'a'ida yana daure a hannunsa sai zobunansa da baya rabo da su. Ji ta yi tamkar numfashinta zai dauke tsabar kyawun da ta ga ya yi mata a idanu. 
  To ba Ummi kadai ba, Ihsan kanta baki ta bud'e tana kallonsa, ji takeyi tamkar ta dora hannu a ka ta ce wayyo Allah, kamar ta matsa bakin Faruk ya furta yana sonta. 
   "Wow Yaya Faruk, kayi kyau wallahi." Muryar Ikram ya katse Ummi da Ihsan daga tunanin da zukatansu suka lula. Ya dan rankwashi kanta yana dan murmushi.
   "Ko?" Ta yi dariya.
"Allah kuwa."
  Ya jinjina kai sannan ya zagaya zuwa mazaunin direba ya bude motar, Ihsan da sauri ta bude gidan gaba ta shiga, hakan bai wani dameshi ba, don shi bai dauketa wata aba ba face k'anwa. 
   Ya bud'e motar kenan yana shirin shiga idanunsa ya kai gareta. 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

57
Chapter 40 · 0% Book details