Sashe 96
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Misalin karfe takwas da dare, Amarya ta kammala waya da Angonnata wanda sai gobe zasu iso da tawagarsa don budar kai, tana tare da yan uwanta ana hira da dariya, Ikram ta shigo da sallama. Duk suka dubeta suna masu amsawa, Ummi ta saki fuska saidai can kasan ranta gabanta ne ke dukan tara-tara to da me kuma ta zo mata?
"Amaryata ki zo mijinki na kira."
Fuskar kowannensu da mamaki, sauran mamakinsu na zuwan ango, Amina da Ummi kuwa bayan haka harma da na sabuwar fuska da suka ga Ikram da shi wanda basu saba ganinta da shi ba akan lamura na Ummin, wato fuskarta a sake saidai idan ka nutsu za ka fahimci a kunyace ta ke dakewa kawai ta ke yi. To ya zata yi? Tunda tana son dan uwan Ummi ai dolenta ta sauko.
"Wai Angon ne ya zo?" Cewar wata budurwa.
Ikram ta dubeta tana 'yar dariya.
"Gani nan, ai nima miji ce tunda kanwar mijin ce."
Sukayi dariya gaba daya har Ummi, ta saci kallon Amina, Amina ta yi mata alama da ta je. Ta mike ta bi bayanta, anan kofar dakin suka tsaya. Ikram ta ga shirun ba zai amfaneta ba ta yi magana cikin sanyin murya.
"Don Allah Ummi ki yafemin abubuwan da na yi..."
Sai kuma ta ji kunya, hakan yasa ta yin shiru.
'Rayuwa kenan." Cewar Ummi a zuciyarta. A fili fad'ad'a fara'arta ta yi don dagaske ta ji dadi kamar ta shid'e. Hannunta ta riko.
"Kai haba, ni ban rike ki da komai ba, daman nafi daukar hakan a rashin fahimta, na yafemiki duniya da lahira nima don Allah ki yafemin."
Dariya ta yi ta dafa kafadarta.
"Nagode Ummi."
Ummi ta ja hannunta.
"Zo muje kiga yan uwana."
Daman haka ta ke so, ta bi bayanta suka koma ciki. Zama sukayi ana hirar tare, yawanci duk Ummi suke koyawa yanda ake kula da miji ita kam shiru ta yi don ta ga su babu ruwansu, Ikram dinma da ta ke kunyar ita dinma ta biyemusu. Sallamar Gidado ce ta katsesu, suka amsa, yana daga kofa yana dubansu, sanye ya ke da shadda ruwan toka babu hula akansa, gashinsa ya yi luf-luf.
"Me ake tattaunawa ne aka manta da kawomin furata?" Cewarsa yana duban Matarsa Hafsa dake aikin dama mishi fura, ita kuwa baiwar Allah Ikram tun shigowarsa ta daskare a wajen gami da k'ura mishi idanu.
Shi kam sau daya ya kalleta kallo na ganin bak'uwar fuska daga nan bai k'ara dubanta ba.
Hafsa ta bishi da murmushi.
"Na gama yanzu zan kawo."
"To saiki hanzarta, kinzo kin biyemusu kun samin kanwa a gaba kuna cikata da surutu ko?"
Aka dara, Ikram murmushin yak'e ta yi gabanta na bugu da sauri-sauri jin wai Gidado na da mata, ta dubi matarsa, babu laifi bata daga sahun munana amma a diri na halittar jiki ba zata nunamata ba, babu gaba balle baya. Ta kara satar kallonsa. Ta ko'ina ya kere matarsa saidai ta kula kallon ma da ya ke jifar matartasa da shi wacce ta ji a dazun sun ambata da Hafsa, kallo ne na musamman mai nuni da tsantsar so da kauna. Ta sauke ajiyar zuciya yayinda ta ke ji kamar ta dora hannu aka ta hau rusa ihun kuka.
"Kai Yaya Gidado, ba kunyar idanu irin wannan kallon?"
Cewar wata Maimuna abokiyar wasansa, ya kai mata duka ta kauce.
"Kefa kin raina ni yarinyarnan, kinga taso ki ji zan dan fita ne da Abubakar."
Ba musu Hafsa ta mike ta bi bayan mijinta, su kuwa yan dakin aka sanya dariya banda Ikram. Duk zaman ya gundureta, ji ta ke kamar ta bar wajen, ai kuwa da sauri ta mike.
"Bari na tafi na kwanta na gaji."
Ta yi maganar a sanyaye tana duban Ummi, Ummi bata kawo komai ba bayan rashin sabo don kuwa ita kanta bata sake da ita ba ganin abin ta ke banbarakwai wai namiji da suna HAJARA.
A nan soron gidan ta yi kici6us da Gidado da Hafsa, ya wani kankance murya yana magana kamar saurayi gaban budurwa, suka dubi juna ya jefeta da murmushi.
"Sannu da bakunta." Ya bata haushi saidai ta danne.
"Yauwa." Ta amsa a dakile kafin ta wuce da saurinta zuwa wajen yan uwanta.
Koda ta shiga su Jidda ke kwasar hira akan yan uwan Ummi kowacce na tofa albarkacin bakinta, sam basu dauka zasu gansu kai a waye ba, sun yi zaton kauyen da zasu je yafi haka muni sai kuma abin ya basu mamaki ganin komai tsaf.
"Ke kuma daga ina?" Cewar Baraka.
Ta yamutse fuska.
"Wajen matar Yaya mana."
Mamaki yasa su sakin baki kafin su hau dariya.
"Shishshigi ko?" Cewar Fadila.
Ta daure fuska gami da kwanciya saman katifa ta basu baya.
"Ba ruwan mutum."
Suka shareta. Wannan daren har hawaye ta zubar na tausayawa kanta haka kuma bata ji komai na digon son Gidado ya ragu a zuciyarta ba...!
WASHEGARI BUDAR KAI....!
Karfe biyu Ango ya iso da tawagarsa saidai a Otal suka sauka....!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Wannan naki ne yar uwata...
Sis Aisha Samarou...
115
Ranar ko waya bai samu damar yi da amaryartasa ba.
Dukkan wani masoyi ga Ummi zai so ganinta a wannan rana don kuwa ta yi kyau ainun, har wani kumatu ta ajiye, kasancewarta fara k'al, sai kunshinta ya yi kyau ainun, hakanan siraran kitson da akayi mata shima ya taimaka kwarai wajen fiddo da zahirin Hasiya Abdullahi. Karfe hudu aka sanya na yin Budar Kai saidai ba'a soma ba sai karfe biyar harda mintuna, anan kofar gidan zaayi.
Ummi ta hade cikin wata hadaddiyar shadda kalar sararin samaniya wacce ta sha aiki, suka sanyamata Alkyabba, duk a cewarsu itama jinin sarauta ce don kuwa jika ce gidan Lamidon Jar Kwami. Shima angonnata ya sanya riga da wando sai kuwa babban riga ta shadda kalar na Amaryartasa. Hular nan ta zauna d'abas a kansa, shi kansa Angon wani kamshi da annuri kawai ka ke gani saman fuskarsa.
Fuskar Amarya a rufe ruf, haka aka riketa har mazaunin da aka tanada mata, Ango na zaune tare da su Haidar sai kuwa abokan karatu da na aikinsu, sannan danginsa mata a baya suna fuskantar Amarya Ummi da nata dangin itama daga bayanta.
Algaita kawai ka ke ji ana busawa awajen, nan aka soma inda Ango Faruk ya mike, Haidar da Jafar wano abokin aikinsa sune a gefensa, haka ya nufi wajen Amaryarsa mata na faman gud'a da hanci ya bud'e fuskar Amaryarsa kuma matarsa, idanunta a k'asa tana faman doka murmushi yayinda ta ke kokarin danne kukan da ke son kwace mata. Nan ya soma zuba ruwan kudi waje ya cika da sowa da gud'ar mata, bayan ya gama nasa suma abokansa suka soma kafin daga bisani bayan komawarsu danginsa su tashi suma su yiwa Amarya nasu lik'in. Bayan sun kammala ne, itama Amarya ta mike da Amina da Abu kanwar gidado suka isa ga Angon wanda ya kasa dauke idanu daga kan Amaryarsa yana ji kamar ya dauke abarsa su gudu. Durkusawa ta yi suka mik'a mata turare na maza mai tsada da dadin kamshi ta hau fesa mishi, ya lumshe idanu ya bude yana dubanta, hawayen da ta ke kokarin dannewa saida suka zubo, ta daure ta daukesu da sauri, sannan ta amshi hankicif a kunyace ta hau goge mishi gumi kamar yanda aka koyamata, habawa zo kaga sowa da gud'a, su kuwa su Mami, al'adar Gombe ta tafi da su matuka don abin ya burgesu musamman ganin ba kure kamar yanda Abubakar ya koyawa Faruk haka din ya yi shima.
Daga haka Amina ta mik'amata bandir na dari-dari, nan ta shiga lik'amishi itama, abin ya burge matuk'a, bayan ta kammala suma danginta suka dan yi nasu lik'in sannan aka dau hotuna wannan karon Ango Faruk babu wani batun iyayi na rashin son hoto har yayyunsa na zolayarsa yana dariya, daga nan kuma aka tashi taro....!
((Ku yi hakuri da wannan ba chaji ne...))
[2/5, 6:52 AM] +234 703 962 5239: DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
116