← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 116

Sashe 77

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan kana bani hakuri bana jin dadi wallahi Baba, ni na hakura komai ya wuce awajena. Abinda ya faru kaddara ce, kuma Allah Ya yi ba makawa sai ya faru. Ka daina damuwa kada wani ciwon ya kamaka."
  Ya jinjina kai yana murmushi can kasan ransa kuwa, yabawa ya ke da kaifin basira irin na 'yartasa. Damuwa dole ce a wajensa, ko don ma rashin sanin irin kallon da danginnasu zasu yi gareshi. A fili kuwa ya nunamata komai ya wuce. Wayarta da ke(ringing) ne ya katsesu, ta sa hannu ta janyo jakarta ta ciro don ita ta mance da ita ma, ganin mai kiran yasa ta ajiye wayar don kunyar dauka ta ke ji gaban Babannata, lura da hakan yasa shi yin murmushi sannan ya mike.
"Bari dai na lek'a wajen abokan hirata yau sun ji shiru, daga nan na saka kati na kira su Yalla6ai na ji yanda suka isa. Wannan ki kaita ga daki nan akwai katifa ku kwanta anan." Ya karashe yana nuni da Mariya. 
   Ta amsa da to, bayan fitarsa ta janyo wayar da sauri saidai kafin ta kai ga amsawa har ta yanke, ta bi wayar da kallo cike da shauki anan take ta kira ya kuma shigowa. Ta d'aga da sallama. 
   Faruk da ke kwance saman gadonsa rungume da filo ya lumshe ido jin muryarta ya amsa sallamar ciki-ciki. 
  Jin yanayin muryarsa ne yasa ta fadin.
"Kun isa lafiya? Ya mura?"
"Alhamdulillah, kin samu Baba kin mance da mijinki ko?"
  Ta ji kunyar maganar, har lokacin bata gamsu da yanayinsa ba, kamar dai akwai damuwar da ya ke 6oyemata.
  "Ummina." Ta kasa amsawa sakamakon jin kiran sunannata da ya yi yana zaga dukkan ga66an jikinta, ta lumshe ido gami da jingina kai da bango tana kallon sararin samaniya wanda ke cike da taurari. 
    "Ba za ki amsa ba?"
Ta daure ta amsa.
"Um." Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce.
"Ina kewarki. Ina matukar kewarki Ummina, ban gane hakan ba saida muka dawo gida, duk sai ya yimin fad'i."
   Murmushi ta ke yi saidai ta kasa cewa komai don ita kunya ma ya bata, ga kaunarsa da ke k'aruwa sosai a ranta. Ita kanta ta yi kewarsa fiye da tsammaninta.
  "Ba magana ko? Wannan kunyar fa ta gulma ce akwai ranar da zan kaudata don na gaji da ita tana cutata."
   Ta rufe idanunta da hannu tamkar yana ganinta, banda "Um" ba abinda ta ce. 
   "Banso aka k'i tsayar da maganarmu ba yanzu ba, saidai Baba yana da gaskiya, ni kaina zanfi so kiga danginki ko burinki zai cika tukunna. Ina kara tayaki murnar sasantawa da mahaifinki, Allah Ya k'ara kauna tsakaninku."
  "Amin Yaya Faruk, nagode."
"Na gaji fa da Yaya yayannan, ki chanjamin suna."
   Ta danyi dariya kawai. 
"Dagaske nake, ana muku ruwa?"
Ta girgiza kai.
"A'a."
  "Ayya, mukam ruwa sosai ake yi."
Murmushi ta yi.
"Alhamdulillah, kun ji dadi."
"Ina wani dadi, babu Ummina a gida?"
Kamar ta nutse don kunya ta kasa magana can kuma ta ce.
"Saida safe."
  Ga mamakinta ta ji ya saka dariya sosai, sai itama yasa ta murmushi. Bayan ya tsagaita ya ce.
"Allah Sarki Ummina, ina son wannan kunyartaki saidai please ta kasance iyakar yanzu kafin mu kai ga aure kin ji ko?"
   Murmushin dai ta ke yi ba ta ce komai ba. Atishawa ya saki har uku a jere, ya karashe da fadin Alhamdulillah, ta amsa da YarhamukAllah sannan ya amsa mata da 
"Yahdikumullahuwa wa yuslihu balakum."
   Shiru ya biyo baya kafin kuma ta daure ta ce.
"Don Allah ka sha maganin mura."
Ya ji dadi ainun na kulawar da ta nuna gareshi. 
   "Banason magani, sau daya na sha ya sanyani bacci ban k'ara sha ba."
  "Haka za ka daure ka..."
Sai kuma ta ji nauyi ta yi shiru.
"Kin damu da ni har haka Ummina?"
Wasa ta hau yi kawai da jelar dankwalinta batare da ta ce uffan ba. Ya sauke ajiyar zuciya.
"Zan sha tunda ba kya sona da mura."
  Ta murmusa.
"Ka turomin lambar Hajiya don Allah."
   "Me za ki ce mata?"
"Gaisawa za mu yi."
"Shikenan zan aikomiki."
Daga haka suka yi sallama, ta mike ta shiga dakin da Baba ya yi mata nuni da makwancinsu, ta gyara shimfidar, dakin katifa ce kawai sai shirgin kaya a gefe. Da taimakon wayarta ta haska ta dauko Mariya bayan ta kai ta ta yi fitsari ta shimfideta. Ita kuwa kayan jikinta ta rage ta d'ebi ruwa ta zagaya kewaye don garin akwai zafi, bayan ta yi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga na bacci cikin wadanda Faruk ya siyamata. Ta feshe jikinta da turare mai sanyin kamshi sannan ta zauna gefen katifar tana tunanin ko ina mahaifinta ya wuce? Sallamar Saude ta ji wanda ya sanyata jin wani mugun faduwar gaba, kafin ta amsa, ta tsinci muryar Babanta wanda daman ba nisa ya yi ba yana zaune kofa. 
  "Me ki ka zo yi a gidana?"
Saude ta dubeshi, daman a k'ule ta ke don acan Kawunta Isah ci mata mutunci ya yi ya nuna babu inda zaije daman tuni ta bar ganinsa da daraja. Da ta gaji da zama ta ga dai babu wanda ya kulata an barta a tsakar gida yashe yasa ta taho ko tayin abincin da akayimata bata ci ba don ta rantse gidanta za ta kwan. 
   "Ka manta inada 'ya? To babu inda zanje sai na yi idda."
"Idda a gidan wa? Wallahi ba ki isa ba Saude, ke ba irin matar da zan yi marmarin na komawa aurenta bace, tun muna mu kadai ki tattara ki barmin gida kafin na jibgeki na tara miki jama'a!"
  Ummi dai tana daga daki tana lek'ensu don tsakani da Allah har yanzu tana jin tsoronta sosai. 
   Saude ta yi shewa.
"Ahayye! Lallai Abdullahi wuyanka ya isa yanka! Har ni Saude ka ke gayawa haka? To ni kuwa yau babu inda zanje, anan gidan zan kwana don uban mutum!"
   Tana maganar kamar ta6a66iya, daidai da su Habiba da sauran makwafta mafi kusa suna ji, ko daga majalisar su Malam Balarabe suma suna jiyo ihunta da maganarta. Zagin da ta yi ya firgita dukkan masu sauraro, ai Malam Balarabe baisan lokacin da ya janyo igiyarsu ta shanya ba nan take ta tsinke, ya soma tsulamata yana fadin.
"Kinyi kadan, karyarki ta yi karya ki zagi ubana! Kin yi kadan Saude."
Ihunta yasa mutane suka shigo, itama Ummi fitowa ta yi tana rokon mahaifinta da ya kyaleta. 
"Haba Malam Balarabe da girmanka? Wannan ba girma bane, dukan mace don Allah ka yi hakuri." Cewar Malam Yahuza kenan, Saude wacce ta ci duka ta hayayyako mishi.
"Kai dalla can rufewa mutane baki, solo6iyon banza da wofi, duka-duka yaushe ka samu kwato kanka a hannun Habiba?"
  Hakan ya harzuka Malam Balarabe ganin bakar maganar da ta ke fadawa abokinsa, ya k'ara tunzura zai kai mata duka, gam! Ummi ta rike igiyar gami da durkusawa tana fadin.
"Don Allah Baba ka yi hakuri, ka kyaleta."
Saude ta mike tana gyara zaninta tana ihun kuka, Malam Yahuza da sauran mazan suka rasa bakin magana, suna shirin fita ai kuwa ta cakumo wuyan Ummi ta baya tana fadin.
"Kema sai kin bar duniya yadda Hasiya ta barshi, sai na kasheki!"
  Ummi da ta ji shak'a ta soma kwatar kanta saidai ta kasa, cikin zafin nama mutanen suka yo kanta, dakyar aka yi nasarar kwatar Ummi daga hannunta, kuka sosai Ummi ke yi tana shafa wuya tana tari don ba kadan ba, ta ji shak'ar. Mari lafiyayye Malam Balarabe ya wanke fuskar Saude da shi, ai kuwa ta hau tsalle tana zage-zage, ya finciki hannunta tana tsalle tana ihu tana zagin iyayensa da Ummi har tana fadin "Da nasan haka za ki zama da tun kina jaririyar kema mun kasheki!!" Haka har ya watsar da ita a kofar gidan ya kulle ta waje. 
Mutane sai hakuri suke bata daidai da mata fitowa sukayi kallon wannan abin al'ajabin. Bata jira komai ba ta nufi kofar gidan Malam Yahuza. Hannuwanta a k'ugu tana karkad'a jiki.
"Ina ki ke shegiya bak'ar munafuka? Ki fito! Ki fito nace!!!"
Tana shirin shiga gidan Malam Yahuza ya tureta daman cike ya ke da haushinta.
"Karki sake ki shiga gidana, kada na k'ara ganin kafarki wallahi."
  Dariya ta shiga kyakyatawa ga hawaye jage-jage saman fuskarta kamar mahaukaciya sabuwar kamu tana nunashi daga sama har k'asa kafin ta rangad'a bud'a. 
  "Ayyiririii! Eh babu shakka akuyar daure ta samu sake! Yahuza kai ne ka samu iko haka? To wallahil azim yanda aurena ya mutu kema Habiba yau naki zai mutu!"
    "Idan ke ce da shikan a hannu sai ki zo ki rabamu!"
  Cewar Habiba sa'ilin da ta leko kanta, Malam Yahuza na kokarin tsawatarmata akan ta koma ciki saidai maganar Saude ya dakatar da shi, duk jama'a na kallo, Malam Balarabe kuwa jira ya ke yi ta gama haukanta ta bar wajen ba zata shigar mishi gida ba. 
   "Keda ki ka kashe rai! Wallahi jama'ar gari ku shaida Habiba da hannunta ta kashe Hasiya!!!"

   Can na hango Bokanya tana faman kyakyata dariya tana kara jijjiga abin tsafinta a hannu, cikin ihu da kururuwa ta dauki wata kwarya ta fasa tana fadin.
  "Kadan ku ka gani shegu! Kadan ku ka gani!! Na soma karya dukkan mugun aikin da na k'ullamuku!  Daman kwa yarda da wani bayan Allah? Hahaha! Mu daman ta6a66u ne mun yarda!!! Hahahaha!!!" Wannan furucin Bokanya kenan sa'ilin da ta ke kallon dukkan abinda ke faruwa ta cikin wata k'atuwar kwaryar sihiri. (Wa'iyazubillah).
Chapter 77 · 0% Book details