Sashe 36
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
49
Amina bata k'ara kulata ba saida ta sanya kaya, ita kuwa ta yi mutuwar zaune kawai tana bin ta da kallo duk inda tasa k'afa. Sai lokacin ta dubeta.
"Muje mu gaida su."
Ummi ta girgiza kai ta rik'o hannunta.
"Wallahi ba inda za muje sai kin amsamin, me kike nufi da muna son juna?"
Amina ta dara ta koma ta zauna gami da cire wasa a maganganunta.
"Ummi kina jin Faruk a ranki, daidai da kallon da ku ke jifan juna da shi abin a tambaya ne. Karki 6oyemin abinda na sani, kina son Faruk so na AURE. Hakazalika shima yana sonki, kuma ya sani nafi zaton gwadaki kawai yakeso ya yi ya ji ko ke din kina sonsa. Bar wannan batun, Faruk ya fi karfinki Ummi, ina gujemiki matsala. Wallahi na daukeki tamkar ciki daya muka fito, bana son abinda zai sa a ci mutuncinki. Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu 'yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu. Ki cire Faruk a zuciyarki Ummi, babban goro sai magogin k'arfe, ina gujemiki shiga matsala. Abinda ya shafeki ya shafeni. Sannan ina so duk juyin duniya idan Faruk ya nemi amsa ki tabbatar mishi cewar babu wani abi da kika fahimta game da hakan haka kuma ke babu abinda kikeji game da shi. Kinji?"
Ummi ta yi iyakar kokari wajen maida kwallar da ya tahomata, ta aminta hakan ne tana son abinda ya yi mata nisa. Ta yi murmushin yak'e.
"Naji Anti kuma in sha Allah zan dau abinda kika shawarceni akai."
Ta murmusa.
"Nasan da ciwo Ummi, amman gwara kiyi jinya daya da k janyowa kanki jinya na har abada....."
Ta gyada kai tana murmushi.
Daga haka suka fita, kai tsaye wajen iyayen suka shiga suka gaishesu sannan suka fito. A hanyarsu ta zuwa taimakawa su Binta da aiki ne suka hadu da Faruk ya shirya zai wuce aiki. Ummi ta dan saci kallonsa, shi dinma idanunsa akanta. Suka gaisheshi, ya amsa.
"Fatan babu wani matsala?"
Ya cewa Ummi, ta girgiza kai a tsorace.
"Kinji?"
Ta yi shiru, ya k'ara maimaitawa. Hakan yasa ta dubeshi da mamaki.
Ya kashemata ido daya daman fuskar ya ke son k'ara kallo daga haka ya wuce. Amina ta kama baki.
"Mun shiga uku, Yaya Faruk da gaske ya ke fa."
Ummi dai ba bakin magana don gaba daya ya kashemata jiki. Suka karasa ciki, sunyi mamaki na rashin ganin Sa'a, sai Binta ke basu labari ai tun daren jiya ta harhada kayanta ta bar gidan ba anan ta kwana ba. Suka ta6e baki, anan Amina da karfin hali ta yi ta yiwa Binta nasiha har tana nunamata ba yi bane abinda sukeyi don abokin 6arawo 6arawo ne. Sai kuma Binta ta hau borin kunya da fad'an wai kazafi akayimata batasan komai ba.
*** *** ***
KADUNA
Dija tuni ta kammala dukkan abinda aka sanyata, zaman jiran sakamakon kawai takeyi wanda hakan ya soma faruwa domin a yanzun koda bata fito ta karya ba, Deen da kansa ya ke aika su Tasleem kiranta.
Yau ta kama ranar talata, misalin daya Munira ta fice domin daukosu. Tana zaune tana karanta sakonnin Raihana wanda ya kasance naci ne ta ke mata tana rok'on ta rik'e alk'awarinta. Banda tsaki babu abinda ta ke ja duk da cewar zuwa yanzun Raihana ta dan burgeta bisa taimakon da ta yi mata akan Masoyinta.
Tsayuwar motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa, jikinta ya gama bata Deen ne ya dawo cin abincin rana don Munira sau da yawa sai wajejan uku ta ke shigowa gidan. Tana lek'awa kuwa ta hangeshi, da sauri ta saki labule. Ta k'ara gyara zaman rigarta k'arama wacce ta tabbatar ta fiddo komai na jikinta. Babu laifi Dija na da kyau daidai gwargwado, bata da k'iba sosai, ba kuma ta kasance cikin masu rama ba, bak'a ce, dogon hancinta da fararen idanunta ne suka taimaka matuka wajen k'awata fuskarta. Tana da dirin jiki daidai.
Da kanta ta isa ta bud'e mishi k'ofa. Idanunsu suka tsarku cikin juna, ya ji wani abu ya dakeshi. Kwanaki biyu kenan yana fama da tunaninta da kuma wani shauki na soyayyarta wanda ya ke jin zai iya mutuwa idan har bai sameta ba.
Ta kasheshi da murmushi wanda ya kara rud'ar da shi. Ya bi jikinta da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya.
"Sannu da zuwa Deen."
Ya amsa da sauri yana kallonta. Ta ba shi hanya ya wuce, ta rufe kofar ta koma ta zauna a falon. Babu jimawa da shigarsa daki ya fito.
"Sannu Dija, kin ci abincin ne?"
Ta yi dariya a ranta, shakka babu aiki ya soma ci. A fili ta danyi kasa da kanta.
"A'a, bana iya ci ni kadai ina jiran su dawo ne."
Ya zaro ido.
"Haba Dija, sai ki zauna da yunwa? Wannan bai yi ba, yaushe za ki tsaya jiransu alhalin daga nan zata biya kasuwa? Taso maza ki ci abinci please."
Ta girgiza kai tana jin dadi a zuciyarta kamar zai kasheta, yau Deen ne ke rarrashinta haka? Ai ji ta yi wani kaunar Raihana na kwararuwa cikin zuciyarta. Gudun kada ta yi saurin bayar da kai ne yasa ta ce "A'a, zan bar..."
"Ki bar me? Lallai nima kinaso na juya da yunwata kenan."
Ta zaro ido tana dubansa fuskarta dauke da murmushi.
"Ina zan so haka? Muje."
Ya bita da murmushi sannan suka dunguma zuwa tebur.
Da kansa ya ja mata kujera ta zauna tana jin dadi a ranta tamkar ta mike ta daka tsalle.
Ya zauna ya yi (serving) dinta shima ya zauna ya zuba nasa sannan ya dubeta da murmushi har lokacin dauke saman fuskarsa yana kasheta da wani irin kallon da tun da suke bata ta6a ganinsa a tare da shi ba sai idan yana tare da Munira.
"Bismillah."
Itama ta kasheshi da nata salon kallon sannan ta murmusa ta soma ci, tana ci amma ta lura shi sam hankalinsa baya kan abincin. Ta dubeshi cikin alamun tambaya, ya sauke ajiyar zuciya.
"Kinga nakasa cin abincin ko? Naga kinmin kyau ne."
Ta yi dariya.
"Kai Deen, ba fa wani kwalliya nayi ba."
Ya kashemata ido d'aya.
"Anya? Kamar kin yi kurkur kin shafa jan baki da kwalli, haka nake ganinki a idona."
Suka tuntsire da dariya lokaci guda. Ta shagwa6e fuska.
"Abin har da tsokana?"
Ya yi dariya gami da lakuce hancinta.
"Ba zancen tsokana."
Ta yi soror tana dubansa, tamkar fa a mafarki ta ke gani, anya kuwa ba mafarkin bane? Cikin dabara ta kai hannu ta mintsili fatar hannunta.
"Wash!" Ta fad'a a fili, a rikice ya dubeta.
"Meyafaru?"
Ta dan dara.
"A'a bakomai, gaskiya ka ci abinci idan ba haka ba nima zan daina ci."
Ta karashe gami da ture farantin, ya maida mata filet din gabanta.
"Na tuba, zan ci. Don Allah karki fasa ci."
Sukayi dariya suka hau cin abinci. A ran Dija murna fal ya cikata, ashe akwai sauk'aki'yar hanya da zata samu zuciyar Deen amma ta tsaya shirme da wahala?
Deen ji yakeyi kamar ya rungumeta don tsabar so da kauna, bayan sun kammala ta rigashi mikewa ta koma falon, ya bita da kallo cikin shaukin so.
Da biyu ta koma falon tasan dole ya bita da kallon. Wayarta ta janyo ta tarar da missedcalls har goma, kasancewar a (Vibration) ta sanyata ne yasa basu ji k'arar ba. Ta dauka ta duba, duk daga Raihana ne, dogon tsaki ta ja, tabbas Raihana dagaske ta ke. Kafin ta yi yunkurin ajiye wayar kiran ya k'ara shigowa. Saida ta waiga bata hangi Deen ya taho ba sannan ta d'aga.
"Ina jinki."
Raihana ta marairaice murya ta hau yi mata magiya akan ta sanarmata dalilin da yasa ta k'i d'aga wayarta da wuri. Wani bakinciki ya tokare zuciyar Dija, sa'ar da Raihana ke ci awajenta bai wuce na ita din itace silar taimakonta wajen samun Deen ba. Ta daure ta 6oye 6acin ranta.
"Kiyi hakuri, ina tare da Deen ne."
Wani bakinciki da kishi ya turnik'e zuciyar Raihana, ta daure ne kawai don tana taya masoyiyarta son abinda take so. Ta daure ta ce.
"Allah Sarki, ya ji dadinsa tunda yana samun kulawar da bansamu ba."
Dija ta ji kamar ta shak'eta. Motsin da ta ji na Deen ne yasa ta fadin.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
50
"Zan kiraki karki k'ara kirana." A hankali yanda bazai ji ba, wannan muryar ta k'ara kashe Raihana da dadi. (Wa'iyazubillah) ji ta yi kamar ta shiga wayar ta rukunkumeta, dole ta yi mata sallama ba don taso hakan ba.
Deen ya karaso, ya kammala shirinsa zai koma ofis, ya dubeta lokacin da ta ke k'ok'arin ajiye wayar. Suka yiwa juna murmushi.
"Har zaka koma?"
Ta tambaya cikin kankan da murya.
Ya gyada kai.
"Zan koma, ga shi basu dawo ba kamar kada na tafi nayi zaman tayaki hira."
Ta kasa jurewa ta dubeshi fuskarta na nuni da tsantsan farin ciki.
"Wai don Allah kaine kuwa? Ashe akwai ranar da za ka nuna kulawarka a kaina har haka?" Sai kuma ta yi shiru a tunaninta ta yi azar6a6i, amma sai bai bata kunya ba ya amsa.
"Idan ban kula da ke ba ai bazan iya kula da kaina ba kenan Dija, bakisan yanda nake jinki a zuciyata ba wallahi."
Ta lumshe ido don jin dadin maganarsa gami da murmusawa.
"Nagode Deen, yanzu kayi hakuri ka tafi ofis, ai idan ka dawo ina gidan."
Ya nok'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro.
"Aa." Sukayi dariya. Ya kar6i lambar wayarta don a baya ba shi da, sannan sukayi sallama. Ai yana fita ta hau doka tsallen murna, daga wancan kujerar sai wannan tana yi tana dariya.
Ba ita ta nutsu ba saida su Munira suka dawo bayan la'asar alokacin har kiranta saida ya yi suka sha hira. A gefe Raihana na faman jaddadamata cewa ta rik'e amana ta cika alk'awari ta yanar gizo. Banda toh babu abinda ta ke cewa a fili kuwa ta ja tsaki don haushi.
*** *** ***
ABUJA