← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 116

Sashe 58

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Yi ta ke babu kakkautawa duk ta hargitsa mutanen dakin, suka rirrik'eta, fadi take. "Zata kasheni! Wayyo zata kasheni wallahi! Ku taimakeni!" Cikin gigita Saude ta kai hannu ta toshemata baki. 
  "Ke Habiba shiga taitayinki, mafarki kikayi?"
  Sai lokacin Habiba ta gane ta farka, ta dubi jama'ar dakin 'yan rakiyar amarya Kaduna ta sauke ajiyar zuciya gumi yana ta tsastsafowa daga goshinta, ita kuwa Habiba idanunta a zazzare, rashin gaskiya ya bayyana k'arara akan fuskarta. Tana jin matan na fadin addua ya dace ta dungayi idan ta yi mafarki. Har dai kowa ya koma makwancinsa. Dabara ta fadowa Saude.
"Tashi muje ki sha ruwa."
Suka mike suka fita zuwa kicin, ta dakata gami da rike kafadar Habiba. 
  "Gayamin wane irin mafarki kika yi?"
Habiba wacce har lokacin jiki ke rawa ta zayyanemata komai, hankalin Habiba ya tashi, ji ta yi hanjin cikinta sun kad'a. 
"To, meke shirin faruwa haka? Mun shiga uku."
  "Ba ke kika shiga uku ba Saude, ni da na ganta ganin idona ai ni ce da shiga uku."
  Saude ta dubeta da idanunta da sukayi kwalkwal.
"Kada fa allura ta tono garma?"
"Kar ki damu, da zarar mun koma zanje wajen bokanya, ko menene zata sanarmana sai a dauki mataki."
Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa. A karshe suka koma makwancinsu batare da ko ruwan Habiba ta iya sha ba.
                  ***   ***   ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
75
                       KANO
  Da yamma suka isa, direba na fakin, ta sauko daga motar a hargitse, tana rataye da jakarta ta hannu. Sukayi kici6us da Iklima wacce ke shirin fita zuwa makwafta, daga ita sai doguwar riga(fitet gown) da mayafi karami kalar kayan. Ta watsamata kallon tara saura.
"Akwadaita an dawo?"
Ihsan ko kallonta bata yi ba ta gifta ta wuce. Iklima ta bita da kallo gami da sakin dariya, batasan meyasa yanzu gaba daya ta tsani Faruk ba, wani mugun so ta ke yiwa dan wata k'awar Hajiya Binta, Mu'azzam, shima sonta ya ke yi tamkar ya mutu.

Ihsan bata zarce ko'ina sai sashensu, tuni Fahad ya isar da zuwanta ga Mami wacce ke kicin tare da Ramma suna aiki, saidai duk fuskarta babu digon walwala. Jin zuwa Ihsan yasa ta fito, Ihsan na shiga itama uwar ta hau kwalawa kira. Suna yin kici6us ta fad'a jikinta gami da ruk'unk'umeta ta soma hawaye. Mami ta lumshe ido tana mai rungumeta, ta riga tasan meke damunta. 
  "Aa lale da manyan gari." Maganar Ramma ya katse tunaninsu, jin hakan Mami sakinta.
  "Shiga ciki ina zuwa."
Bata ko amsa sannu da zuwan Ramma ba, ta yi gaba abinta, wannan ya bawa Ramma tabbacin akwai matsala kenan. Mamin tasa Ramma mik'amata kayan sama. Tana jin Ramma na fadin. "To ita kuma Ummin tana ina?" Saidai babu mai amsamata, koda ta shiga dakin Ihsan harara ta samu da ta kulata. Ramma ta kama baki.
'O'o, ko ta yi gamo ne a hanya?' Ta tambayi zuciyarta don tasan ba mai amsamata. Ta fice tana jimamin wannan lamari na sauyin da aka samu daga uwar har d'iyar, tana nan Hajiya Mama tazo saidai kafin ta je gida ta dawo ta tarar batanan. 
     Sai bayan Magriba, Mami ta yi wanka ta shirya tsaf da nufin zuwa turaka, alokacin ne ta shiga dakin diyarta ta inda ta tarar da ita tana goge jikinta alamun wanka ta yi.  Ganin Mami yasa ta zama gefen gado, itama zaman ta yi.
"Mami kin ji..."
"Kar ki ma 6ata bakinki, nasan komai."
Cike da mamaki ta ce. "Au Mami har daman zasuyi mana wannan cin fuskar su iya kiranki su sanarmiki?"
  Ranta ya dan sosu da jin kalma ta cin fuska da 'yarta ta jefi Hajiya Babba da shi, zata so ita ta kirata da komai amma bataso yaranta su rainasu.
"Kar ki k'ara fad'ar haka tunda ba ke ta ciwa fuska ba, ni ta yiwa. Kuma idan har muna raye zasu ga sakayya."
Ihsan ta yi kwafa tana mai jin zafi a zuciyarta.
"Wallahi Mami ni na hakura da Yaya Faruk, na ji na tsaneshi ma. Wai akansa aka ci zarafina, banda cin zarafi ta ya ya za'a had'ani kishi da 'yar aiki, wallahi nafi karfinnan."
Ta ji dadin kalaman Ihsan din, daman ita ta ke ganin zata bata matsala sai kuma ta bata mamaki. Cikin murmushi ta dafa kanta. 
"Kin burgeni matuk'a, barni da su suna gani sai kin auri mijin da yafi Faruk komai da komai, sai sunyi mamakin mijinki Ihsan. In sha Allah kuma sai kin riga d'anta aure. Ita kuwa Ummi su jik'ata su shanye, mu ba'a koyamana yawan malamai ba, idan ita ta bisu don kawo mana rashin jituwa a zuri'armu to ta cigaba idan zaiyi tasiri."
  Ihsan ta dan ji wani iri, so daban ya ke, anya zata so wani nan gaba irin son da ta yiwa Faruk? 
Tana ji Mami ta gama maganganunta kafin ta mike bayan ta ce idan ta kammala ta zo ta gaida Abbanta, daga nan ta fice, Ihsan ta bita da kallo. Sai kuma ta dan ja guntun tsaki gami da cije le6e. Ummi kadai ce matsalarta fa, da babu ita, babu abinda zai hanata auren Faruk. Amma kuma Mami na da gaskiya, watakil fa ba banza ta bar su ba, ta yi kwafa.
"Babu abinda yafi karfin addua, za ki gane kurenki." Ta yi furucin a fili.
Saida ta kammala shiri cikin doguwar jallabiya ta fito, bayan kammala cin abinci da Fahad ta ja hannunsa zuwa ga Abbansu, Adnan tun maganar da sukayi da Mami ya bar gidan. 
    Abba ya yi farinciki da zuwanta, ita kuwa dadin sake ganin dariyar Abbanta ne ya cika zuciyarta, gani ta ke yi kamar a mafarki. 
    Sun jima suna hira kafin Mami ta umarceta da shiga sashen matan gidan a gaisa. Haka ta soma da zuwa sashen Hajiya Binta, babu kyakkyawar tarba daga gareta harma yaranta, itama ganin haka ta nuna yar zamani ce ta fito batare da ta k'ara kallonta daga gaisuwa daya.
    Kai tsaye wajen Anti Amarya ta nufa, ta sakarmata fuska fiye da baya don ita bata da matsala a hakan, hakanan su hussaina yaranta, har Anti Amarya tayita janta da hira tana fadamata ta yi k'iba. Ihsan ta ji dadin zuwa sashenta kafin su yi sallama.
  Haka halayen Anti Amarya ya ke saika rantse dagaske so na tsakani da Allah ta ke maka, takan yi iyakar kokarin boye ainahin sirrin zuciyarta agabanka. (DAN ADAM MAI WUYAR GANE HALI KENAN...!)

   Hajiya Mama ranta duk a 6ace, Amina da yaran Hajiya Maman, Rukayya, Maryam, Na'im da autarsu mai shekaru goma, Mufida. Intisar ce babbat diyarta don Hajiya Mama bata samu haihuwa da wuri ba.
  "Lafiya kuwa yau?"
Cewar Rukayya tana duban yan uwanta. Amina wacce suka zama kamar yan uwa ta jinjina kai.
  "Nifa na lura tun dawowar Hajiya Mama daga gidan Mami bata cikin hayyacinta, Allah Yasa ba wani abun ne ya faru ba." 
   "Amin, ni duk jikina ya yi sanyi ma wallahi, bakuga wainar fulawar nan ta dazu ba gaba daya fita daga raina ta yi wallahi."
  Rukayya ke maganar tana yamutse fuska cike da damuwa, duk da ita ce ma karfin cewa suyi wainar fulawa har ana rabon aiki, wannan ce zatayi suya a farko idan ta gaji waccan ta yi, wancan mai daka yaji.
  "Allah Ya jishshemu alheri." Fadin Amina kenan.
Suka amsa da amin, ita kam Amina ko aka bata ta6a kawowa wani batun Ummi ne ya tashi da Faruk ba? To wa zai kawo hakan ma?
    Suna nan zaune Adnan ya shigo da sallamarsa. Suka amsa, Maryam ta saki baki tana dariya.
"Ikon Allah, kodai mafarki nakeyi, ku mintsileni mugani."
  Ai kuwa Amina da Rukayya harma da Mufida suka hau rige-rige, ganin dagaske suke ta yi tsalle ta ja baya suka sanya dariya gaba daya. Adnan ma cikin dariyar ya zauna, hankalinsa ya dan kwanta da yanda suka tarbeshi, ko babu komai ya ji dadin ganin Hajiya Mama bata sanarwa yaranta ba. Bayan an gaisa yake sanarmusu batun tafiyarsa gobe, Rukayya harda ihun murna, Maryam ta zaro ido.
  "Dagaske?"
Adnan ya jefeta da kallon kauna don kuwa sun had'a kansu saidai a 6oye suke soyewa ta kafar sadarwa harda yiwa juna alkwarin rikon amana.
"Kamar baki sani ba?"
Sai kuma ta yi murmushi. Maryam ta ta6e baki.
  "Ato, ai munsan komai saidai mu yi shiru."
Ya yi dariya da mamaki kafin ya dubeta.
"Ke kika sani malama, ina uwata?"
"Au, daman baku hadu ba? Daga gidanku fa take."
  "Eh, ni na dan fita ne."
  "Ayya, bari ayi mata magana."
"Kamar ba gidanmu ba?"
Ya fad'a yana hararar Rukayyar, sukayi dariya kafin ya wuce.
  Sallama ya yi, Hajiya Mama ta amsa don ta ji maganarsu da yaranta. Fuska a sake tana mai kokarin danne damuwarta ta ce.
"Aa Adnan? Karaso mana."
Ya karasa jiki a sanyaye ga kuma kunyar abinda Maminsa ta aikata gareta ya russuna ya gaisheta. Ta amsa. Shiru ya biyo baya kafin ya soma bata hakuri kan abinda ya faru.
"Kayya, dama baka shiga ciki ba don kuwa wannan tsakaninmu ne. Karka damu, ka yiwa mahaifiyarka uzuri kasan ance mai d'a wawa, watakil son nata ne ya rufemata ido har haka. Amma nasan Madina ba lallai har zuciyarta hakan bane."
Ta fad'a ne kawai ba don har zuciyarta tana ganin hakan bane, saidai bata kaunar yaransu su shigo cikin maganar wanda dai da kamar wuya. Bazata so ya shafi zumunci yaransu ba da mazajensu.
    Adnan shi kansa yasan Hajiya Mama ta fad'a ne kawai.
  Ta share maganar.
"Ashe kuma gobe zaka wuce ko?"
"Eh." Ya fada yana mai shafar sumarsa.
  Ta shiga yi mishi nasiha tamkar dan cikinta, da nunamishi sanya Allah a rai da kuma gujewa mugayen dabi'u da abokan huld'a. Adnan ya ji dadi matuk'a na shawarwarinta, ya ji dukkan damuwarsa ta warware daman ya dauka shikenan Hajiya Mama ta barsu kenan, sai ya ga ba haka ba. Koda ya ce zai wuce, dakatar da shi ta yi don saida ya ci abincin dare sannan ta kaishi har wajen Alhaji Haruna mahaifin su Intisar suka gaisa shima ya bishi da kyawawan nasihu da kuma addu'o'i kafin suyi sallama ya tafi bayan su Maryam sun tabbatar mishi zasu zo rakiyarsa zuwa(Airport) goben.
                    ***  ***  ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  77
                      RINGIM
Chapter 58 · 0% Book details