← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 116

Sashe 116

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mace mai shekaru ashirin da daya mai tsohon ciki na hango sanye cikin kananun kaya riga iyakar gwuiwa da dogon wando,  kanta nade da mayafi tana bin wani kyakkyawan yaro wanda ya ci riga marar hannu da wando karami na shan iska, yana gudu yana dariya rike da 'yartsana tana binsa da tsinken tsintsiyar kwakwa. Wata kyakkyawar yarinya da aka nade gashinta da ribbon tana biye da ita tana murza idanu baki a ta6e lamun kuka ta yi. 
   "Afreen! Afreen! Ba zaka tsaya ba wai?"
   Saidai kamar k'ara tunzurashi ta ke ya hau zagaye falon, a haka Uban ya fito daga sashensa yana dubansu, ganinsa yasa Afreen rugawa gareshi ya rungume kafafunsa.
  "Papa kaga Maama pho?" Ya fada cikin gur6atacciyar hausarsa. 
  Daidai lokacin da ta karaso a fusace ta daga zata kai mishi bugu, Faruk ya rike hannunta. Ta dubeshi tana huci.
"Allah kuwa FAR HAS karka hanani, tun dazu ya ke ta sanya yarinyarnan kuka don ya ga bata da hayaniya duk ya bi ya takura rayuwarta. Bata yartsanarta tun kan na 6ata ranka."
  Murmushi Faruk ya yi ya daga Afreen cak ya sanya a kafadarsa suna dariya. Ganin haka yasa Ummi ta k'ulu, ta yi kwafa gami da jan hannun Afra su wuce. Faruk ya riko kunnen Afreen har saida ya saki yar kara da dariya. Yaron ba dai wayo ba. 
  "Bigboy meyasa ka ke takurawa Bebina ne? Duk maganar da zanyi ba ka ji ko? Zamu 6ata fa."
"Na daina Papa, ka yi hakuli."
  Ya ja kumatunsa kasancewar Afreen tubarkallah akwai k'iba don har yafi Afra jiki.
  "Oya muje ka bata hakuri."
Suka nufi wajen Ummi wacce ta dannowa Afra game a wayarta ta mik'amata. Ko kallonsu bata yi ba, Faruk ya sauke Afreen, ai kuwa daman jira ya ke a guje ya je ya mikawa Afra 'yartsanarta kafin ya soma raba idanu yana kallon wayar Ummin don a rayuwarsa yana son ya ganshi yana danne-dannen waya duk kuwa da cewar ba iyawa ya yi ba. Abin yaso bawa Ummi dariya sanin halin dannata saidai ta danne. Ya dubeta kamar wanda ya yiwa Sarki k'arya. 
Faruk ya na dariya ya dan sanya yatsa cikin kunnen Ummi ta yi saurin tarewa tana dariya. Bayan sun tsagaita ya ce. "Kinsan fa abinda dannaki ke so ki ke mishi yanga ko?"
  Ta dan tsuke baki.
"Allah kuwa shine abin ban haushi."
"Na daina Maama, ki yi hakuri."
Ya fada yana mai dafa kafafunta. 
"Please Ummina ki yi hakuri bazai k'ara ba ko?"
   Ta yi murmushi kafin ta rungume dannata ta sumbaci goshinsa. 
  "Is ok my son, Maama ta hakura."
  Ya hau tsalle sannan ya dane cinyarta har ta danyi k'ara sakamakon dan bugun cikinta da ya yi, da sauri Faruk ya dagashi cak.
"Afra, tashi ku je dakin Maama ku yi game din amma banda danne-danne kunji?" 
"Toh." A guje suka mike suka yi dakin, ya janyota jikinsa ta kwanta saman kafadarsa. 
  "Ina sonki Ummina."
Ta lumshe idanu tana murmushi, shekarunsu uku da aure amman har gobe tana jin kalmar nan tamkar sabuwa fil a kunne da gangar jikinta. 
  "Kasan me FAR HAS?"
Shima idanunsa lumshe ya amsa.
"Sai kin fada Ummina."
  Ta kara rungume hannunsa.
"Inajin dadi aduk sadda ka cemin I love you."
Ya yi yar dariya.
"Zanyita ce miki har sai zuwa komawarmu ga Allah, ki tayani addua, Allah Ya bani ikon farantamiki har karshen rayuwata."
Ta dago ta dubeshi shima ita ya ke kallo har suna shakar numfashin juna, kai ta girgiza gami da shafar gefen fuskarsa. 
   "Ni kuwa menene ba ka yimin ba ma a yanzun FAR HAS, ka nunawa duniya cewa nima ina cikin yan Adam masu girma da daraja, ka yimin dukkan wani abu na rayuwa, ka barni na samu karatu har gashinan zan zana jarabawar wucewa jami'a, me zanyi gareka banda addua da kyautatamaka. Ni nake ganin ma kamar banyi maka wani abu ba..."
  Ya girgizamata kai cike da jin shaukin sonta da kauna.
"Ke ki ka yimin kuwa Ummina, tunda har ki ka amince da aurena ki ka zauna da ni bisa amana har kika haifamin Afreen da Afra kin biyani Ummina, ga kuma bebina mai zuwa nan gaba,( ya shafi cikinta), kinmin komai kina bin umarnina kina nunamin kauna ta hakika, ai kuwa kin biyani."
  Ta yi murmushi, wayar Faruk ta yi kara ya daga, Abubakar ke sanarmishi haihuwar Ihsan haihuwa ta biyu, farinciki ya cikashi don daman yaronta na fari  Badiyya abokiyar zamanta ta barwa wacce itama cikin ikon Allah yanzun ta ke dauke da juna biyu. 
   Ummi kanta ta yi farinciki don takanas ta kira Ihsan suka shiga hira kafin Abubakar ya kar6e wai ta takurawa matarsa daga haihuwa, don yanzu Abubakar ya nutsu sosai ya bar dukkan mugun dabi'u cikin nufin Allah. 
   Faruk ya mike gami da miko mata hannunsa, ta dubeshi ya kashemata ido daya. Ta bishi da murmushin da ya fi so daga gareta, kafin ta sanya hannunta cikinnasa suka nufi sashensa....!!!!
          Tammat Bi Hamdullah...!!!
     Godiya da Yabo sun tabbata ga Ubangijina da Yaban ikon rubuto muku labarin DAN ADAM, tsira da amincinSa su tabbata ga Annabi sallalahu alaihi wasallam. 
   Godiya gareku fans masu karfafamin gwuiwa, duk inda kuke koda ban sanku ba, wallahi ina kaunarku, Allah Ya hada fuskokinmu duniya da kuma lahira (aljannarSa)..ameen.
   Godiya ta musamman ga yar uwata kuma mai kaunata koyaushe...
  Safiyya Ummu Abdoul..Allah Yabar kaunata...kwarai kin taimaka sosai wajen ganin DAN ADAM ya tafi bisa tsari... Allah Ya barmu tare..ameen...
   Ina mika godiya ga mutan DM, Hdy, rof facebook & whatsapp, khalisat group fb, Matan aure, matan aljanna, meema's novels, classic ladies, taskira da sauransu. 
  Don Allah duk wanda na mance ya yi hakuri..kuna da yawa ne...inda muka kuskuro muna fatan zaayi mana uzuri sannan zaa yi mana... 
DAN ADAM AJIZI NE, DAN ADAM NADA DARAJA, DAN ADAM BA ABIN WULAKANTAWA BANE...Bakasan mai yi maka rana ba cikin DAN ADAM... 
  Allah Yasa mu dace..ameen...!!!

  
Chapter 116 · 0% Book details