← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 116

Sashe 29

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Washegari Iklima tana ji tana gani su Mami nata shiryen-shiryen tafiya. Rahila da Aisha suma nan suka zo, dan Aisha, Tahir ya yi wayo sosai. Rahila da yaranta biyu itama, Bintu da Samir wanda shine karami yana da wayo sosai, cikin ikon Allah bai mance fuskar Ummi ba, hakanan ya yarda ya je hannunta. Ko kusa Ummi bata da matsala da Rahila da Aisha, babu ruwansa, sannan basu fiye zuwa gidan ba face da babban dalili. Wannan ne dalilin da yasa basu san wainar da ake toyawa ba, a wannan zuwannasu ne ma ta tsincesu a dakin Ihsan tana faman labartamusu komai harda tafiyar Adnan Abuja. Aisha da mamaki tace "Haba, shiyasa kwana biyu banga keyarsa a gidana ba, ashe baya garin. Bakomai, komai zai wuce."
  Abinda ta tsinkaya kenan ta dauki kayan Fahad da Mami ta aiko ta dauka ta fice daga dakin. 
  Nan su kuma sukayita jajantawa har saida Mami ta gaji ta soma fadan zata tafi ta barsu sannan suka fito. 
   Kai tsaye gidan kakansu suka nufa wato Alhaji Atiku Modibbo inda anan zasu hadu har Hajiya Mama da iyalanta su wuce Abujan. Tafiyar har da Innarsu. Suka yi sallama suka bar dan tsoho daga shi sai yan aiki da wani dan uwansa na Adamawa suka kama hanya. Ummi na rike da Samir a gefen Antinta Amina suna shan hira, kowa a Bus din abinda ya shafeshi yakeyi, Mami kuwa su uku ne a mazauninsu, ita da Hajiya Mama da Innarsu sai hira sukeyi. Nan ma Ummin ke labartawa Amina kazafin da akayimata, Amina abin ya yi mata ciwo saidai fadan da yafi karfinka... 
Har dai suka isa kowa da abinda yasa gaba kafin a karshe a gaji ayi shiru.
   Amina da Ummi wadanda basu ta6a takowa Abuja ba, suka saki baki suna kalle-kalle. Har suka isa gidan Gen. Ahmad Danzaki inda anan kallo ya koma sabo dal. Suka saki baki suna k'arewa haduwar gidan kallo. Wannan ko a Turai ne sai hakan.
"Aljannar Duniya." Abinda Amina ta fada kenan cikin rada yanda Ummi kadai ce zata ji. Sukayi 'yar dariya.
"Bari Anti, basu da matsala a fannin kudi."
  Amina ta jinjina kai. "Tabbas."
Direban ya hau hon, maigadin da sauri ya budemusu kofa yana washe baki gami da dago hannu yana musu lale marhabin. 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

43
   Yana daga samansa yana dubansu da murmushi, ya karasa ga Adnan wanda bayan karin safe ya yi wanka ya cigaba da bacci ya kai mishi duka.
"Tashi kaga wani abu." Adnan ya mike da sauri yana dubansa ido waje.
"Sun iso?"
  Faruk na murmushi ya ja hannunsa zuwa barandar. Ihu ya saki wandq har saida su Mami da suka riga suka fito suka kallo shi, dariya suka sanya. Da gudu ya fira ya sauka garesu. Shima Faruk ba shi da za6in da ya wuce na bin bayansa. 

Adnan ya kama hannun Maminsa tamkar ya rungumeta don murna. 
   Baraka da Ikram a guje suma suka fito har Hajiya Babba wacce ta kasa hakurin k'arasowar yan uwannata ciki. Ta rungume Innarta, su Amina da Ummi suka zagaya domin kwasar kaya. 
  Tana janye da katuwar jaka, idanunta ya sauka akan Faruk, yana gefe ya hard'e hannuwansa yana zabga murmushinsa mai burgewa. Sanye ya ke cikin kananun kaya, riga bak'a anyi rubutu da farin abu, wandonsa ma bak'in ne, ya yi kyau har ya gaji da had'uwa. Cikin sa'a idanunsa ya kai kanta sa'ilin tuni sauran sun kama hanyar cikin gidan. Murmushi ya sakarmata, itama ta tsinci kanta da mayarmasa da martani har(dimple) dinta na dama  na bayyana. Ya ji wani abu da bai ta6a ji ba na tsirgashi, ya kauda kansa gami da soma tafiya zuwa ciki. Tana jan akwatin tamkar bata so sanadin kallonsa da take yi, namiji mai aji kenan, ina ita ina shi? Ta sauke ajiyar zuciya ta dubi gefenta jin alamun mutum. Amina ce itama rik'e da katuwar jakar Hajiya Mama tana dubanta cikin nazari, sai kuma bayan sun hada ido ta sakarmata murmushin yak'e.
"Muje mana naga bakya daga kafa ne."
Ummi ta gyada kai ta k'ara sauri. Amina mamaki kwarai takeyi na irin kallo da murmushin da ta ga Faruk na jifan Ummi da shi, da kuma kallon da Ummi ke bin bayan Faruk din da shi har ya illata tafiyarta. Ta numfasa, 'Idan ma akwai wani abun ya zama dole nasa ido na gano, bazan bari Ummi ta jefa kanta cikin matsala babba ba, ina mata kallon kanwata kamar ta jini.' Ta ayyana a ranta. Da taimakon yan aikin Hajiya Babba aka shishshigar da kayan gaba daya ciki. 
  Tsarin gidan Hajiya Babba wane sauran gidajen yan uwanta, iyakar haduwa ya had'u. Kayan duk ansaka a inda ya dace, Ummi da Amina daki guda aka hadasu wanda duk na yan aiki ne, yana daga can bayan(garden) din gidan. 
    Hira ta k'i ci ta k'i cinyewa tsakanin yan uwan, dakyar sukayi wanka suka chanja kaya sannan aka gabatar da sallar la'asar akayi zaman cin abinci. Alokacin kuma Haidar da Intisar suka shigo. Da gudu suka rungume juna ita da Ihsan sannan ta koma ga iyayen kowanne ta hau rungumarsa don dadi. 
  "Wai ke bakya girma ne?" Cewar Hajiya Mama kenan alokacin da ta rungumota. 
  "Kema dai kya fad'a Sadiya, yau kam dole kiban mijina tunda na iso." Cewar Inna kenan.
  "Ahaf, mai zuwa gidanmu sai ya shirya fa." Fadin Haidar kenan, akayi dariya gaba daya. Su Faruk na daga falo suna jiyo caftarsu, shima Haidar bayan gama gaisuwa ya komo wajensu ana hira. Faruk kusan hankalinsa ya kasu biyu, hakanan ya ji yana d'okin ganin daga inda Ummi zata 6ullo, fatansa ya k'ara cin karo da kyakkyawar fuskarta. Da zarar ya soma tunaninta, sai ya yu saurin kwa6ar zuciyarsa, aganinsa babu wani dalili da ya ke da shi da zai dunga tunanin wata can. Abu ne da tun da ya ke a rayuwa bai ta6a faruwa gareshi ba. 
    Ita kuwa baiwar Allah, suna can tare da Amina suna cin abinci, saida suka kammala suka kai komai kicin. Alokacin ta fita wanka, bayan dawowarta itama Amina ta tafi wanko jikinta. Doyuwar riga ta sanya na kanti marar nauyi na yawon gida, itama Amina doguwar rigar ce jallabiya. Ummi ta dubeta taba daga rigingine saman katifa 
"Anti ashe duk tsaruwar gidajen su Mami bai kama rabin k'afar na Hajiya Babba ba?"
  Amina ta murmusa yayinda ta zauna gefenta.
"Haduwa ma ba daya ba kedai, na ji ance fa har wajen wanka akwai(swimming pool)."
  Ummi ta zaro ido.
"Haba?"
"Wallahi a bakin su Anti Intisar na ta6a ji, ba don ma kada muyi laifi ba da mun zagaya gidan."
Ummi ta amsa.
"Wallahi kam, zanso ganin wajen wankan kuwa."
  Haka sukayita hirarrakinsu, Amina na son yi mata magana akan abinda ke gudana tsakaninta da Faruk, tana kuma tsoron kada ya kasance zarginta ne kawai, wannan yasa ta barwa zuciyarta. 
    Sun sakankance suna hira har Ummi ta soma lumshe ido na jin bacci, ganin haka Amina ta kyaleta. Cikin baccin kuma ta ji ana tashinta, ta mike zaune tana murza idanu. Ta yi mamakin ganin lokacin Magriba ya taho.
"Ki tashi magriba fa ta yi, an turo a kiramu ma sai ni na je nayi aikin." Cewar Amina wacce ke kokarin gyara hijabinta bayan dauro alwala da ta yi. Da sauri ta mik'e ta fita zuwa bandaki domin dai bandakin yan aiki mata guda daya ne kuma ba cikin dakuna ya ke ba, yana daga dan lungun dakunan. Ta iske yan aiki biyu na alwala, ta gaishesu.
"Kece Ummi?"
"Eh." Ta amsa da murmushi. Suka saki baki.
"Kema kuma yar aiki ce?"
Ta gyada kai don ta soma mamakin tambayar. 
  Daga haka ta wucesu ta shiga bandaki. Tana jiyo hirarsu, daya na fadin. "Kinsan Allah Binta, da ace ni na samu kyawun wannan ba zan bautawa wasu a aikatau ba, na gwammace na ci duniyata da tsinke."
  Bintar ta ja tsaki.
"Kedai matsalarki Sa'a kina da son maza kamar wata karya wallahi. Nayi zaton ma batun aure zakiyi."
  Sa'a ta ta6e baki.
"Aurena biyu ban ji da dadi ba, don haka ko marmarin k'ara yi bana yi."
  Lokacin Ummi ta fito sukayi shiru, ta isa ga famfon dake a gefen garden din inda suke tsaye ta soma alwala suna kallonta, suka saki baki ganin har wata suma take da a goshinta ga gashi daidai misali, ita dai ta samu ta kammala a gaggauce, ta yi musu sallama ta tafi da tunani hali irin na wasu mutanen da suke da karancin godiya ga Allah, wasu suna can ma basu samu koda rabin yanda su suka samu ba.
  A haka ta shiga ta tarar har Amina ta idar da sallar tana addu'o'in da ta saba. Itama ta zura hijab ta tayar, bayan idarwarsu suka yi zaman hira anan take ji daga bakin Amina cewa su Haidar ma sunzo.
"Mai yiwuwa suma sauran ki gansu." Amina ta karasa.
  Ummi ta bata labarin hirarsu Sa'a akanta, Amina ta dara.
"Mata kenan, muna da matsala wallahi. Mudai mu kama kanmu babu ruwanmu da harkarsu idan ba gaisuwa ba da hirar da bata shafi kowa ba. 
    Suna nan Sa'a ta lek'o.
"Ummi, Anti Aisha na kira."
"Toh."
Ta mike cikin sauri ta gyara zaman hular kanta. 
   Ta fito tana waige-waige don har ga Allah ta mance yanda tsarin gidan yake. Ta karasa wajen doguwar baranda wacce akwai bene daga wani loko, ta yi shiru, ta cigaba da tafiya, wata kofa ta gani makamanciyar wacce suka shigo, hakan yasa ta bude kofar, kawai sai ganinta ta yi a wajen (pool). Daga tsakiya ya ke, a gefensa rumfa ce aka sanya kujerun zama, wani murmushi ta yi don sosai wajen ya burgeta.
Ta rufe jin kamar motsi ana saukowa daga bene. Tana shirin barin wajen suka yi kici6us da Adnan. Kowannensu ya saki fuska. 
  "Lah, daman dake aka zo?" Ta yi dariya.
"Eh, kana murnar ganin Mami baka lura ba."
  Ya dara shima. "Bari kawai, ai nayi kewarku wallahi. Ina za ki ne?"
   "Kaga hanyar na rasa, Anti Aisha ce ke nemana."
  Yana dariya ya soma tafiya.
"Ke kam ba dai saurin mantuwa ba, biyoni ki gani."
 DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 29 · 0% Book details