← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 116

Sashe 48

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

64
Washegari Ummi ta kammala aikinta, tana shirin barin wajen Hajiya ta shigo, bayan ta gaisheta ta dakatar da ita da fad'in.
  "Ina jin zuwa Asabar zaki koma fa, ba don naso hakan ba sai don Madina da ta takura da zama ba mai tayata wasu hidindimun, ta ce yanzu ba wata matsala. Zuwa gobe za'a kawomin wata."
   Gaban Ummi ya fad'i, jikinta ya yi sanyi matuk'a. Shikenan ta kusa rabuwa da ganin sanyin idanunta. A fili ta k'irk'iro murmushi wanda ya yi kama da na yak'e. 
  "To Hajiya, Allah Ya kaimu."
"Amin."
  Daga haka ta bar wajen da saurinta, tana zuwa (garden) ta zauna a kujerar da ta saba zaman wanki, ta ajiye bokitin mai dauke da tsummokarai, shiru ta yi tana tunani kafin ta daga kanta tana duban barandar dakin Faruk, shikenan ta kusa daina sakashi a ido koyaushe? Hawaye suka zubomata, ta jima tana shararsu kafin ta daurewa zuciyarta ta cigaba da aikinta. A ranar haka ta wuni jiki babu kwari, daidai da Binta ta lura da hakan, tambayar duniya ta yi mata saidai amsar daya ce.
"Babu komai."
Koda dare ya yi, ta taimakawa Binta da shirya tebur har lokacin bata da wani kuzari, abincin ma kasa ci ta yi sosai. Binta sai kai loma take yi, can ta dubeta.
"Wai menene matsalarki ne?"
Ta numfasa.
"Na fadamaki babu komai, kaina ke ciwo."
  Daga haka ta dan ja guntun tsaki ta mike.
  "Ni na k'oshi ma."
. Binta na kallonta ta wanke hannu ta bar kicin din zuwa daki. 
"Um, ai shikenan idan ta yi wari ma ji."
  Daga haka ta cigaba da cin tuwonta. Ummi na tafe a sanyaye, wasa takeyi da jelar dankwalinta, yayinda ta fad'a duniyar tunani, ko kadan bata san inda take jefa kafarta ba, tasan dai hanyar dakinsu ta nufa. Babban damuwarta bai wuce Faruk ba, da kuma irin yanda take tunanin ko aurensu mai yiwuwa ne ko kuwa dai kawai iyakar soyayyar ce?
    Bata ankara ba ta ji ta yi karo da mutum har goshinta na ta6a kirjinsa, ta yi saurin ja baya a tsorace, sai kuma ta yi ido hud'u da hasken rayuwarta. Wani hadadden murmushi na gefen kumatu ya sakarmata. Sanye yake da riga marar hannu mai hula da wando(3quarter). 
   Ta sauke idanunta kasa sannan ta russuna cikin rawar murya ta gaisheshi ya amsa sannan ya dubeta.
"Zo, ke na fito nema daman, na lek'a daki ban ganki ba."
  'Gwara da Allah Yasa ka ganni a hanya.' Ta ayyana a zuciyarta.
Ya soma tafiya zuwa samansa.
"Biyoni."
Ta yi sakato tana dubansa. Har ya taka matattakala uku, ya juyo yana dubanta. Tana tsaye cak, ya dan yi jim yana karemata kallo, ita dinma shi ta ke kallo a sace, can kuma sai ta daga kafafunta da sukayi mata nauyi ta soma bin bayansa. Ganin haka ya murmusa ya cigaba da tafiya tana biye da shi tana waige, cikin sa'a Binta ta zo wucewa da sauri ta sauka ta nufeta.
  "Ina zuwa don Allah, Yaya Faruk ke kirana, ki rufamin asiri."
Ta yi maganar cikin rad'a, Binta ta gyada kai tana dariya ciki-ciki don wannan soyayya tasu burgeta take yi, daga haka Ummi ta juya. Tuni gogan ya shige, a falo ta iske baya nan, tun da take bata ta6a yiwa sashensa kallon tsanaki ba, ko sadda Sa'a ta yaudareta ta kawota wajen KB, sam ba'a cikin nutsuwa ta ke ba. Falon adon fari da bulu ne, ya tsaru iya tsaruwa. Anan kasan (tiles) ta durk'ushe kamar yanda kowace yar aiki ta saba a gaban masu gida. A haka ya fito rike da kan waya da kwalinsa ya iso ya zauna saman kujera. Da hannu ya yi mata nuni da gefensa.
"Dawo nan Malama, saikace ba dakinki ba?"
    Ta saci kallonsa kawai ta dan yi murmushi kafin ta mike cikin tausayawa rayuwarsu, shikenan sun kusa yin nisa da juna duk da hausawa kance garin masoyi ba ya nisa. A kasa ta zauna saman kafet, shima ya zamo ya zauna a k'asan ta dubeshi saidai babu abinda ta ce.
  "Kamar kina cikin damuwa Ummina, sanardani abinda ya faru."
  Mamaki ya kamata yanda har ya fahimci yanayinta. Ta girgiza kai.
  "Bakomai."
Ba don ya yarda ba ya gyada kai sannan ya mik'amata wayar. 
   "Rik'e."
Ta bude tafin hannu ya dora mata a kai.
   "Naki ne."
  Ga mamaki ta dubeshi. 
"Ai..ai ni ban iya amfani da waya ba."
  Ya gyada kai da murmushi saman fuskarsa.
  "Nasan da hakan shiyasa na kiraki don koyamiki."
    Ji ta yi ranta ya yi wani mugun sanyi, saidai fa haduwar wayar ya tsoratata, bata ta6a ganin irinta ba. 
   Jin kamshin turarensa ta yi daf da ita, hakan yasa ta dagowa a razane ta dubeshi, ya matso gefenta hankalinsa naga wayar, ya kar6a daga hannunta ya soma nunamata da yacce zata cire (pattern) wanda ya sakamata saboda tsaro. Sannan ya shiga ya soma da gwada mata budo sak'onni, da amsa waya, har gwada kiranta ya yi ta ga sunan "Hubbyna." Ya fito, bata san dai yanda zata fadi sunan a baki ba. Amma tasan wani abun ya ke nufi na soyayya. 
   Sun dauki kusan mintuna fiye da talatin a haka har saida ya tabbatar ta iya yanda yake so, har (whatsapp) saida ya nunamata yanda zata amsa sak'onshi da mayarmishi da amsa, lambarsa kadai ce a wayar na gaba daya layukansu hudu masu tsada da ba wata diya mace da ta ta6a mallakarsu haka. 
    Bayan ya kammala ya mik'amata kwalin.
  "Mun gama da wannan Ummina, yanzu maganar aurenmu ce ya ragemana."
Ta lumshe ido tana mai jin kamar ta saki ihun kuka, ya matsa yana fuskantarta. 
   "Gobe juma'a nakeson bayyana ki ga su Hajiya matsayin wacce nakeso da aure."
     Ido waje ta ke dubanshi, hawayen da ta ke dannewa tuni ya fito ya soma sauka saman fuskarta.
    Ji ya yi wata iriyar kasala ta saukar masa, ya runtse ido cikin kasalalliyar murya ya ce. "Please stop it mana, na tsani ganin hawayenki ya zuba Ummi akan kuma dalilin da bai taka kara ya karya ba. Idan ke kin kasa jarumtar jure koma menene zai zo wanda bana fatansa ma, ni ya kikeson nayi ne? A'a Ummi, wallahi Faruk bazai iya daukar wani tsawon lokaci batare da Hasiya ba. Na soma gajiya, ni ban iya wannan rayuwar ta 6oye abinda zuciya da gangar jikina ke muradi ba. Bazan iya ba, gobe ki shirya, ina zuwa."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

66
Chapter 48 · 0% Book details