← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 116

Sashe 83

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ta runtse ido gami da dan mak'e wuya kamar wacce ake shirin kaiwa mari, ba ta ce komai ba.
  Ya kasa rike dariyarsa saida ya dara kadan.
"Ummina kenan, ki rikeshi na bar miki."
  Ta zaro ido kawai saita kashe wayar don kunya, ashe daman ya ganta? Ya k'ara kira bata daga ba, karshe ma ta kashe wayar.
    Washegari misalin takwas na safe, tana zaune tana shirin karyawa suna waya da Amina wacce ke labartamata cewar itama za su je Nijar dangin mahaifinsu su dawo, ta tayata murna a karshe ta sanarmata Faruk yana nan. Amina ta yi dariya kwarai.
"Oh wannan soyayya ta ku? Kedai ki yi ta godiya ga Allah da wannan babbar kyautar."
Murmushi kawai Ummi ta yi mai bayyana hakora. 
   Sun sha hira sannan su ka yi sallama. 
   Kwanan Faruk biyu ya soma shirin komawa bayan zuwan Malam Balarabe garin an zauna an tattauna inda ya yi musu bayanin karatun da Ummin ta soma a Abuja, sun ji dadi matuka saidai basu aminta da komawarta gidan surukai ba, haka dai ba don ya so ba ya hakura da raayinsa, yasan idan ya turo su Daddy to watakil su amince ta koma can. 
  A zaure suka tsaya suna sallama, Faruk ya dubi Ummi gaba daya ji ya ke kamar ya zubda hawaye, ita kuwa kanta a k'asa, ya fiddo wayarsa ya kara daukarta hoto, sautin camera yasa ta fahimci abinda ya ke. Ta ja hijabinta tana fadin.
"Kai Yaya Faruk na kusan goma kenan fa."
  "Ke an fadamiki ina gajiya da kallon hotunanki?"
   Murmushi kawai ta yi mai bayyana hakora kafin su yi sallama, a sanyaye ta mishi adduar isa lafiya suka yi sallama ran kowannensu cike da jin kewa. 
   Saida Ummi ta yi sati biyu a Jar Kwami, kawarta ta islamiyya, Husna A Rashid har ta gaji da tambayar ranar dawowarta makaranta ganin lokaci ya ja bata dawo ba. A wannan sati biyun har Kwami ta je ta ga dangin kakarta wadanda wasu da yawa sun rasu, kwananta biyu ta dawo sannan ta wuce birnin Gombe gidan su mahaifinta. 
    Kwanakinta uku da zuwa ta lura da sauyin da aka samu tsakanin mahaifinta da Dada don zuwa yanzun ta sake da shi ta nunamishi komai ya wuce abin ya bata mamaki ya kuma yi mata dadi don har hira sosai suna yi. 
  Kamar yau juma'a da yamma, sun hadu gaba daya tsakar gida ana hira, wayar Malam ta yi kara. Ya saki fuska sosai ganin Malam Yahuza ne. Fadi ya ke. "Yau Yahuza ne ya tuna da ni?"
  Ya dauka da sallama, bayan gaishe-gaishe Malam Yahuza ya soma ba shi labarin bayan rabuwa, ya sanarmishi ya samu ya shirya da yan uwansa ya nemi gafararsu, ya gangara kan labarin da ya ba shi mamaki da al'ajabi har saida ya tashi ya bar wajen yana fadin.
"Innalillahi." Suka bishi da kallo musamman Ummi da ta ji wata irin faduwar gaba don tsoronta ya kasance ko Habiba ce ta gudu daga gidan yari. 
   Bayan ya gama wayar ne ya dawo, anan Haruna ke tambayarshi ko lafiya. Ya dubesu.
"Diyar Malam Yahuza, Dije, 'yar Baba kin santa ko?"
Ta gyada kai don hankalinta ya dan kwanta.
"To itace mijin ya turowa mahaifinta takardar sakinta, aciki ya ke shaidawa mahaifin ya kamata tana mu'amala da yar uwarta mace, ya yi mata duka ya korota tun washegarin faruwar lamarin saidai an tabbatar mishi bata zo wannan yasa yanke turomishi takarda. Bayan haka kuma da kwana biyu labari ya riskeshi cewar an ganta can gidan wata Bokanya ta je tare da abokiyar shaidancinnata har an samu wasu sun k'ona gidan kurmus. Dakyar ita Dijen ta samu arcewa, fitarta kuma ta hau titi da zummar tsallakawa mota ta bi ta kanta."
  Kowa a wajen ya dauki salati.
"Duniya abar tsoro, wannan masifa da me ta yi kama?"
Cewar Baffa kenan, Dada ta ca6e.
"Karshen duk wani mai aikata mummunan aiki kenan matukar bai tuba ba, Allah Ya karemu da al'ummar musulmi ga fadawa halaka irin wannan."
Ummi girgiza kai kawai ta ke yi tana salati, lamarin mutane abin tsoro, wani abin kamar a mafarki, ba don na kusa da kai bane idan ka ji a wani wajen kana iya cewa ba gaskiya bane. 
"Allah Ka sa mu cika da imani." Cewar Malam Balarabe, suka amsa da amin.
      Washegari misalin karfe uku na rana, Ummi kwance a dakin Antinta Abida matar Baffa tana karanta wani littafi na Ahlari da ta taho da shi, ta tsinci muryar Baffa na tambayar Abida ta ba shi tabarma anyi bak'i daga Abuja. Batasan sadda ta mike tsaye ba tana lek'ensu ta windo. 
  "Su waye?" Cewar Abida tana mai mik'amishi tabarmar.
"Maneman auren Ummi."
Ai batasan sadda ta dafe kirji ba gami da komawa saman kujera ta zauna. 
"Su Daddy ne?" Shine tambayar da ta jefi kanta da shi a fili.
"Ina ki ke 'yar nema? Fito nan ki ji labari mai dadi." Cewar Abida tana kokarin shigowa dakin, a guje Ummi ta mike ta 6uya bayan labule tana dariya ciki-ciki. 
   "Au 6uya ki ka yi? Kya ma fito, ai ni tun ganin da na yi wannan saurayin ya kasa hakuri ya biyoki har nan, nasan ba lallai ya iya hakurin barinki ba."
   Ta daga labulen da Ummi ke 6oye, ganin haka ta durkusa tana mai rufe fuskarta da hannu tana dariya.
"Kai don Allah Anti."
Abida ta dara.
"Za ki san Anti, bari mu zo mu soma gyaraki yarinya."
Daga haka ta saki labulen ta koma duba sanwarta. 
  Ummi ta fito ta zauna da saman kujera tana dariya, karatun dai bai samu shiga ba.

   Gen. Ahmad Danzaki ne, sai kaninsa Alhaji Aminu Danzaki da babban Abokin Gen. Ahmad Danzaki, wato Major Yusuf Bashir mahaifi ga Sa'ad miji ga Baraka. Sai ko Babban Yaya wanda shi ne ya tuk'osu daga Abuja, bayan shigowarsu da tambaya suka iso unguwar sannan suka yi kiran Malam Balarabe kamar yanda suka tsara ya tura aka taho da su. 
  ((Thanks for your votes on wattpad.... Love you all..))

 DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

101
Chapter 83 · 0% Book details