← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 116

Sashe 28

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

                  ***   ***   ***
   Bikin Baraka ya iso, komai na shirye-shiryen Mami, ita da kanta ta yi bata saurari Abba ba balle ta tambayi wani abu a aljihunsa har ya samu damar cin zarafinta. Ta yiwa Ihsan anko, hakan ta siyawa Fahad shadda tare da Adnan aka dinka musu. Ummi kuwa ta yi mamaki da Mamin ta bata kudi suka je da Amina bayan isarsu gidan Hajiya Mama ta siyo 'yar kanti da kuma wani abin idan tana so. Ta yi murna matuka duk da tasan ba da ita zasu je ba.
   Hajiya Mama ta jajantawa yar uwarta kwarai na abinda ke faruwa da ita. Ta kuma yi mata fada sosai akan dalilinta na rashin sanar da ita tun wuri. A karshe tace zata sanya ayi rokon Allah, suma kuma ba kwanciya zasuyi ba, su dage sosai da addua da sadaka har Allah Ya kawo makarin koma menene. 
    Bayan Amina da Ummi sun dawo daga shago suka biya gidan Innar Aminar. Mace mai mutunci kwarai, ta yi murna da ganin Ummin da duk sadda Amina ta zo saitq bata labarinta. Sun jima anan sannan suka lek'a gidan Anti Hauwa yayar Amina daga nan suka kamo hanyar gida. A hanyar ne ma Ummi ke labartawa Amina yanda suka ta6a yi da Hajiya Binta. Amina sosai ta tsorata, hankalinta ya dan kwanta jin Ummi bata bi turbar shaidan ba ta aikata. Ta k'ara fahimtar da ita lallai mai yiwuwa yanzun ma da sa hannunsu cikin lamarin Abba da Mami. A karshe ta kara shawartarta akan ta dage da addu'a akan Allah Ya kareta daga sharrinsu. 
    Ashe kuwa dai sharrin na tafe, domin a daren da suka koma gida daga gidan Hajiya Mama, Abba ya kira Mami ya ke fadamata ta gaggauta korar Ummi daga gidansa don labari ya iso mishi cewar tana biye-biyen maza tana fakewa da zuwa makaranta. Acewarsa, yaransa basu jawomasa abin kunya ba, to babu 'yar wata can da zata janyomasa. Mami ranta ya 6aci, cike da mugun 6acin rai ta dubeshi.
"Wannan kuma ba halin Ummi bane, da ace Ummi na yi kasan kafin ka gane ka koreta, da tuni na yi hakan don bana zama da maci amana. To Ummi babu inda zata je, zamanta daram a gidan nan!"
  Ta yi maganar cikin daga murya har kirjinta na bugu da sauri-sauri saboda tsananin 6acin rai, ba wai don kwatarwa Ummi yanci kadai bane, aa, har ma da gajiyawa da jin zafin yanda ya ke bayar da ita gaban kishiyoyinta, don a wannan karon ma har hadasu ya yi gaba daya a falon yana mata korafi akan Ummin. Abin ya soma isarta.
  A fusace ya ce. "Sai mu gani idan gidan ke kika ginashi Madina! Amma wallahi kinji rantsuwa ta musulunci babu yar iskar da zata zauna a gidana, saidai ko ki bita."
  Hankalin Mami ya tashi, su kansu matan sun razana da furucin Abba, Anti Amarya wacce bil hakki ta tausayawa Mamin, ta saka baki.
"Haba Alhaji, ya kake..."
"Kiyimin shiru Malama, bansaka dake ba, daman na taraku ne don na gargadeku da ku jawa yan aikinku kunne, banaso and iskancin banza da wofi. Ke kuma ki tattara taki ki maida inda kika amso ta, bazan lamunci iskanci ba."
  Takaici ya sa Mami jan tsaki batare da tasan sadda ya fito ba.
"Sai kayi, na gayamaka babu inda Ummi zata je, sa'arka d'aya zan je Abuja da na soma gwadamaka gaskiyar abinda nake fad'a tun yanzun. Naga ai wasu ma nasu cikin suka ta6a yo wa aka zubar aka cigaba da zama da su a gidan."
  Hajiya Binta ta fahimci da yar aikinta Sa'ade take wacce ta ta6a yo ciki suka zubarmata. Ta fusata ta yi kwafa batace uffan ba.
   Kafin Abba yace wani abu, Mami ta zura silifas dinta ta fice cikin kunar rai.
  "Ummi! Ummi!!"
Ummi dake daki ta ji Mami na kwalamata kira cikin daga murya. Ta fito a kidime ta russuna.
"Naam."
  Ta tamke fuska.
"Ki shirya kayanki, dake zan tafi."
  Ummi gabanta ya fadi don bata ta6a zato ba,  ta mike ta wuce bayan ta amsa da toh kawai. 
   Shigarta da mintuna biyar Fahad yazo ya kara kiranta wai inji Mami. Ta mike ta isa gareta a can daki. Mamin na zaune gefen gado ta yi jugum tana tunani, bayan Ummi ta durkusa ta dubeta fuska daure.
  "Ki gayamin tsakani da Allah akqn dukkan abinda zan tambayeki Ummi."
  Ummi a tsorace ta ce. "Toh."
Mami ta zubamata ido, ita tasan sharri aka yiwa Ummi, saidai dole ne ta tambayeta don amana ce ita a hannunta. 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

42
"Dagaske ne kina...."
Sai kuma ta yi shiru, haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyin maganar, ta daure ta karasa.
  "Labari ya iso ga Abba na kina bibiyar maza, ki gayamin gaskiya Ummi."
  "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"
  Abinda Ummi ta furta kenan a fili kafin wani kuka ya tahomata, kuka sosai harda sheshshek'a. Mami na kallonta bata katseta ba, bata ta6a jin tausayin Ummi ba aduk zaman da suke sai a yau, k'azafi abu ne mai matukar cin rai, tasan yanda Ummi ke ji irinsa Adnan ya ji a sadda aka mishi sharrin sata, hakanan itama irinsa ta ji alokacin. Maganar Ummi ta katse tunaninta.
  "Wallahil Azim ban aikata abinda ake zargina akai ba Mami, ban ta6a koda tsayuwa na saurari wani d'a namiji  ballantana har ya kai da ta6a jikina ba, ki yarda da ni wallahi Allah ban aikata komai ba. Na shiga uku."
Ta k'ara fashewa da wani kuka wanda ke k'arawa Mami jin wani mugun tausayinta. Ta numfasa muryarta a sanyaye.
  "Ya isa, nasan ba ki aikata ba daman, kawai don kiyaye amanar da aka ban naki ne yasa ni tambayar. Na riga nasan kazafi ne na mahassada amma babu komai wataran sai labari. Kiyi hakuri, kina iya tafiya ki soma shiri, dole dake zamu wuce."
  Ummi ta mik'e ta fita, a hanya suka ci karo da Ihsan ta bita da kallon mamaki ganin ta fito daga dakin mahaifiyarsu kuma tana kuka, da sauri ta karasa dakin don duba Mami. Sai ta tarar ta yi shiru ta zuba tagumi. Ta karasa gareta. "Mami lafiya? Naga fitar Ummi daga nan ta na kuka."
  Mami ta murmusa.
"Bakomai, kin gama shirye kayanki?"
Fuskarta cike da damuwa ta amsa da eh. Bata kaunar ganin Maminsu a wannan yanayin, Allah-Allah takeyi su bar garin su shiga cikin yan uwansu ko zuciyarsu zata sanyaya. Ta kasa hakuri saida ta k'ara tambayar Mamin dalilin da yasa Ummi ke kuka. Haka dai ta sanarmata don ta k'i jinin 6acin ran yarannata. Ihsan duk da tana k'in Ummin itama ta ji babu dadi musamman jin cewa a gaban kishiyoyin Maminnata Abba ya gasawa Mamin magana. Ta yi kwafa.
"Ai Allah Ya fisu, munanan mugun abinsu zai juye kansu."
Mami ta jinjina kai. Tabbas ayanzun ta soma zarginsu duk da zato zunubi, tana yi musu kallon munafukai masu fuska biyu. 
    Ummi ji ta yi duniya ta mata zafi sosai, ta riga tasan makircin Umma ne, ita kadai ce matar da ta ci alwashi akan lalata rayuwarta, ta barta da Allah domin bata da karfin yin fad'a da ita, koda tana da shi, bata jin zata iya ramuwar gayya. Allah zai mata sakayya, saukinta ma Mami bata gaskata hakan ba.

                  ***   ***   ***
Ta dubi 'yarta tana mai zaro ido.
"Me kike nufi ne? To wallahi babu inda zakije. Na rabaki da wannan shegen yaron ba kiji, idan ba kiyi a sannu ba zan mugun sa6amaki."
   Iklima ta turo baki ta mike daga saman kujera.
"Wai don Allah inace ni zan zauna da shi? To ni gaskiya ina sonshi kada ki yi yunkurin rabani da shi. Kuma meye idan naje Abujan? Baraka fa k'awata ce, ana bikinta don kawai wani kishi naki kice..."
  Bugun le66anta da ta yi ne yasa ta yin shirun dole tana sosawa don zafi. 
A fusace Umma ke magana.
"Kinyi kadan! Wallahi iklima kinyi kadan, ban haifi 'yar  da zata fi k'arfina ba nan duniya. Biki ne kuma babu inda za ki taka kije, mu zuba ko ni ko ke a gidannan."
  Daga haka Umma ta nufi dakinta a fusace kasancewar ranar ba aikinta bane. Kai tsaye layin bokonsu ta nema ta sanarmishi akan tana so ya raba zuciyar 'yarta da soyayyar Faruk. Ya sanarmata abu ne mai sauki amman sai ta zo ta amshi wasu magunguna. Ranta ya yi sanyi ta bishi da godiya gami da tabbatar mishi da zuwanta a goben da kuma kudin aikinsa. Daga haka suka rabu.
Chapter 28 · 0% Book details