Sashe 80
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Washegari Dada da kanta ta yafa mayafi ta shigar da Ummi makwafta suka yita ganinta tana nunamusu jikarta diyar Hasiya. Ummi har ta rasa inda za ta saka kanta don murna, fararen hakorannan nata sun kasa rufuwa, a karshe suka dawo gida. Batun Mariya kuwa, Dada har mancewa ta ke yi da ita don dagaske jininta yafi haduwa da diyar Hasiyarta.
Koda suka dawo anan waje suka tarar da Malam Balarabe da mahaifinsa suna hira. Ta daure fuska tamau kamar bata ta6a dariya ba, ko sannu da zuwan Malam Balarabe bata amsa ba. Ta gaida mijinta ta yi gaba. Haka ya sauke ajiyar zuciya ransa duk ba dadi. Malam ya girgiza kai.
"Kar ka gajiya, ka cigaba da rok'onta gafara, Fatima mace ce mai hakuri saidai tana da zafi idan an ta6ota, ni nasan tana kaunarka matuka, na sha kamata tana kuka duk akanka, yanzun kuma da ka zo sai ta yi fushi? Karka damu zata sauko."
Wannan magana ta karfafawa Malam Balarabe gwuiwa, ya saki fuskarsa sosai.
"Ai ni na yi mata laifi, dole na bita a sannu."
Murmushi kawai Malam ya yi.
"Ina matarka ne?"
Gaban Malam Balarabe saida ya fadi, cike da damuwa ya labartamishi dukkan abinda ya faru tun bayan mutuwar Hasiya kawowa yanzu da Saude ta haukace da irin tone-tonen da ta yiwa kanta.
Malam banda ambaton Innalillahi babu abinda ya ke yi, tausayi matuka na Ummi da dannasa ya mamayeshi.
"Yanzu Hasiya saida ta yi aikatau? Allah Mai Yanda Ya so da bayinSa."
Shima Malam Balarabe da jikinsa ya yi sanyi ya amsa da eh. Kafin ya sanyomishi batun maneman auren Ummin. Da kuma irin taimako da suka yiwa Ummin a rayuwa.
Malam ya danyi jim sannan ya numfasa.
"To, shi lamari na aure ai na Allah ne, kwarai sunyi mana halaccin da suka cancanci mu dauki diyarmu mu basu. Allah Ya za6amata abinda ya fi alheri."
Malam Balarabe ya amsa da amin. Haka sukayita hirarsu abin sha'awa.
Bayan Magriba suna zaune suna hira a tsakar gida har Dada, Ummi na kwance ta yi matashi da cinyarta ita kuwa tana aikin tsefemata kai tana fadan tabar kai kitso ya tsufa.
Ita dai banda murmushi babu abinda ta ke yi, ta lumshe idanunta, gatan kawai ta ke gani tamkar a mafarki. Wayarta ta dauki k'ara, ta bude idanunta da sauri, tun dazu ya ke kiranta a hanya saidai ganin tana cikin mutane ne yasa ta jin kunyar dagawa, ta janyo wayar a sanyaye ta ce.
"Dada tsaya na amsa waya."
Dada ta saki kannata, ta dan dubi Dada, ita din kuwa ta zubawa ido, kawai sai ta mike a guje ta fada daki tana murmushi daidai lokacin da ta ke amsawa da sallama.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya saki wanda ta ji shi har cikin ranta. A sanyaye ya amsa sallamar gami da fad'in.
"Ki yi hakuri kin ji don Allah."
Ta kasa gane inda maganarsa ta dosa, ta yi hakuri fa? Yaya Faruk ke bata hakuri?
"Hakuri kuma? Akan me?"
"Ba ki ji yanda hankalina ya tashi jin shiru ba ki amsa wayata ba Ummi, har ina niyyar biyo bayanki Gombe."
Ta numfasa sannan ta murmusa, duk a zatonta wani abin ne daban ko kuma cewa zai yi ya fasa aurenta.
"Kai zan bawa hakuri Yaya Faruk, wallahi muna tare da su Dada ne ni kuma kunyar daukar wayar na ke yi."
Ya yi murmushi mai sauti.
"Karki damu, ya wuce, saidai dagaske ina jin zan shigo Gombe karshen satinnan, nisan ya na takurani, na soma gajiya da rashin ganinki."
Ta kasa cewa komai sai murmushi, a haka Dada ta shigo daukar damammiyar furarta a kwanon sha ta ganta, duk sai ta diririce, Dada murmushi kawai ta yi ta fice.
"Kin yi shiru, dagaske za ki iya ganina."
"Ba ka kunyar su Daddy?"
Ta fada cikin sanyin muryarta. Ya dan yi dariya.
"Haba Ummi, Daddy fa ki ka ce? Kar ki damu, sunsan irin kaunar da nake miki wacce sai na daure matuka na ke iya 6oyonsa, bansan wace irin addua ki ke min na har kullum kaunarki ke k'aruwa cikin raina."
Ta girgiza kai tana dan dariya kawai.
Sun dan jima suna hira sannan suka yi sallama.
Koda suka kammala sai ta kasa fita ta yi zamanta a dakin ta kwanta saman gadon karfen Dada tana game. Can jimawa kadan Dada ta shigo tana fadin.
"Wai 'yarnan ba ki gama wa..." Ganin da ta yi mata kwance tana wasa da waya yasa ta rike ha6a.
"Au, tsifar kenan? Shi ne ki ka yi kwanciyarki anan? To kin kyauta ai daman dare ya yi nima hannuna ya gaji, taso ki sha fura ga farfesu can Abida ta aikomiki."
Ta mike tana mai kokarin rufe kanta da dankwali don sam bata mance tsifar ake mata ba, kawai nauyinsu ne ya hanata fita.
"Allah Yasa ba sukari sosai a ciki irin na dazu."
Dada ta murmusa.
"Kema bakya son sukari sosai? Allah Ya jik'an Boddo, itama haka ta ke ko kadan bata son sukari. Komai naku dai daya."
Jin haka yasa Ummi zamowa daga gadon bayan ta amsa da amin.
"Ni kuwa Dada wai da wa Ummana ta yi kama tsakanin kakana da kakata."
Jin haka yasa Dada zama gefenta gami da dubanta fuska a sake.
"Mahaifiyarki ta dauko kamannin Kakanki Usmanu Lamido, wanda suke kama sosai shi da yan uwansa, musamman babbar yayarsu Bintu dake aure garin Adamawa da yaranta uku, danta namiji guda ne Allah Ya azurta mata shi, a hannunta Karamar uwarki (Zahra) wacce suke kira da Inno ta girma, ana shirin aurenta ta rasu. Idan da zaki ganta itama marigayiya Zahra, sai ki rantse mahaifiyarki ce don kamannin da kuma jini.
Ta jinjina kai kafin ta k'ara da fadin.
"Wai akwai yan uwanmu ne a Adamawan nan sosai? Naga har kanwar Baba itama can aka ce ta yi aure har ta rasu."
"Dangantaka mai karfi kuwa da Adamawa, duk kuwa da asalinmu Kwami da Jar Kwami, saidai mazajenmu da iyayenmu sun yi tafiye-tafiye, wasu suka yada zango Adamawa har suka tara iyali. Ba acan ne shi Lamido Shuaibun ya auro mahaifiyar Yakubu mijin marigayiya Aishatu kafin kuma su rabu ta koma can, a hannunta Yakubun ya girma ai wani zuwansa nan ya ga Inna Boddo a Jar Kwami ya nuna yana so, sai mutuwa ta rabasu."
Ummi zata k'ara magana saidai bata samu dama ba, don Dada mikewa ta yi.
"Kinga, tashi mu je ki sha fura sai mu zo ki ban mijinnawa a waya mu gaisa don na lura sai kumbiya-kumbiya ki ke kada ya ji muryata ya fasa da ke."
Jin haka Ummi ta yi dariya tana rufe fuskarta, Dada ta fice itama tana yar dariyar.
Washegari....
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
98