Sashe 21
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** *** ***
UMARUL FARUK DANZAKI
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
29
UMARUL FARUK DANZAKI
Kwance yake saman doguwar kujera dake a tsararren falon mahaifiyarsu. Idanunsa a lumshe kai ka rantse bacci ya ke, a can d'aya 6angaren na falon kuwa wanda nan ma komai ya ji, Hajiya Babba ce da bak'uwarta suna lissafin kayayyaki. Rabin hankalinsa na garesu, rabin kuwa kan jefashi duniyar tunani wanda kokusa baya kaunar hakan. Ya ja guntun tsaki gami da mik'ewa zaune, wayarsa ya d'auka ya bud'e (data), nan take sak'onni suka shiga tururuwar shigowa wayarsa, duk daga (Whatsapp). Ba sabon abu ne awajensa ba, yana da tabbacin kusan maza abokan aikinsa da yan uwansa sunfi yawa, mata masu turomasa sak'o k'alilan ne don bai basu damar mallakar lambarsa ba, saidai har mamaki yakeyi na yacce mafi yawa na 'yanmatan suka samu. Babban dalilin kenan da ya yiwa kannensa gargad'i akan kada su yarda su k'ara bawa kowace yarinya lambarsa. Sun ji gargad'in kuwa don sun kiyaye.
Kai tsaye ya soma bud'e sak'onnin yana karantawa. Ga mamakinsa ya tsinceshi a wani group na Zumunta. Koda ya shiga yan uwansu ne burtik, mata da matasan. A sunayen (Admins) ya hangi wacce ta tsundumoshi ciki.
"Iklima?" Ya fad'a a fili fuskarsa cike da mamaki, ya koma cikin group inda ya ji tana mishi marhabin da shigowa. Ayayinda wani dan baffansu dake Adamawa ya sanyo alamun dariya. Guntun tsaki ya ja gami da ficewa batare da yace uffan ba.
Yana fita kuwa suka hau kyakyata mata dariya harda masu turo sak'on murya wanda hakan ba k'aramin k'ular da ita ya yi ba. Daman sun san halinsa, ba yau ya soma arcewa daga groups ba, da dai zaka mishi magana ta akwatin sirri, anan kam zai iya baka amsa, harma idan ka ci sa'arsa kuyi hira mai tsayi da dariya.
"To sai anjimanku."
Muryar Bak'uwar Hajiyarsa ce ya katseshi daga danne-dannen da ya ke a waya. Ya dubeta ya gyad'a kai cikin dan murmushi ya amsa
"Allah Ya kiyaye hanya."
Daga haka ta yi gaba tana mai amsawa da Amin. Mik'ewa ya yi ya koma wajen da Hajiyarsa ke zaune. Ta maida lesussukan gabanta gefe ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi.
"Miskili kafi mahaukaci ban haushi, Sadauki nawa ya akayi ne?"
Ya d'an turo baki kamar mace, abin ya bawa Hajiya dariya ta girgiza kai.
"To shagwa6arce ta motsa?"
Ya shafi sumarsa yana 'yar dariya, itama tana tayashi, aduk yaranta tafi so da tausayinsa kasancewarshi mutum marar son hayaniya ga kuma hak'uri da rauni. Kullum addu'arta bai wuce na Allah Ya had'ashi da mace ta gari ba, ba wacce zatayi amfani da rauninsa da hakurinsa ta cuceshi ba. Ya katse tunaninta ta hanyar sanarmata batun group da aka sanyashi ya fice. Da murmushi dauke saman fuskarta tace.
"Toh banda abinka Sadaukina, ai k'ara dank'on zumunta ne, ina zaka so ku had'u da d'an uwanka a hanya ayi abin kunya ba ka san da zamansa ba? Kaga mu ma duk muna da group na zumunci, na yan Adamawa daban, namu na dangin mahaifinku daban."
Ya dauki filo ya sanya agefenta ya kwanta yana mai juya mata baya. Ya lumshe ido.
"Hajiya duk wannan takura rayuwa ce, nafi ganewa mu gaisa ta private ko kuma na kira mutum ko ya kirani. Surutu ne zalla sukeyi."
Ta dafa kansa.
"Zumuncin kenan Sadauki, wani ma hakan ya nema ya rasa. Wasu na can basu da dangin ma da zasuyi musu hakan."
Bud'e idanu ya yi, tabbas Hajiya ta fad'i gaskiya, babu wacce ya tuna sai Ummi. Yana ji ajikinsa, akwai wani babban lamari a rayuwarta, har yau ya kasa cire kwad'ayi akan sanin tak'amaiman tarihinta.
"Hakane Hajiya."
Daga haka ya basar da zancen.
"Wai yaushe yarannan zasu dawo?"
"Af, su Baraka ai ansamu gidan zuwa, suna can nasan suna zuba da Intisar."
Ya girgiza kai gami da ta6e baki.
"Ai Yaya Haidar shi ya barsu."
Hajiya ta rik'e ha6a.
"Au kai kace babu mai zuwa gidanka?"
Ya mik'e zaune ya rungume filon yana dariya kad'an-kad'an.
"Bance ba, amma kada a yawaita."
"Eh lallai Sadaukina, ga shi har yau ni banga surukar tawa ba, Alhajinku ma na fama."
Ya yamutsa fuska.
"Ni wai..." Sai kuma ya yi shiru gami da mik'ewa da daukar wayarsa.
"Aifa, daga ansoma maganar gaskiya saika gudu."
Ya yi murmushi mai bayyana hak'ora.
"Kai Hajiyata, ya dace dai ku d'an huta, ga na Baraka nan fa tafe, abin sai ya yi muku yawa."
Hajiya ta harareshi.
"Wane irin yawa? Ai hutunmu yana bayan aurar da ku lafiya."
Ya gyada kai.
"Hakane, bari na d'an fita."
Ya fice da sauri kada ta cigaba da magana d'aya wanda shi amsarsa har zuwa lokacin bai wuce A'a ba, don kuwa ba zaice ya ta6a soyayya ba balle har ya ji yana son auren wata mace.
*** *** ***
Ahmad Bashir Danzaki, haifaffen garin Kano. Ya kwashi tsawon shekaru sittin a rundunar sojoji yana aiki kafin ya yi ritaya. Matarsa d'aya tun lalle, Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiya Babba.
Yaransu shida cif, Usman shine wanda ya yi karatunsa kacokam akan kasuwanci. Ridwan ke bi mishi, shi din ya kasance kwararren likita a fannin mata, sai Haidar wanda ya ke lauya, sannan Faruk wanda yake ma'aikacin banki. Baraka wacce suke sa'anni da Adnan da Iklima, tana aji na karshe a sakandare wanda tare suke tafiya. Sai auta Ikram, wacce sa'ar Ihsan ce, itama tare suke tafiya da ihsan, suna aji na biyu a babbar sakandire.
Umarul Faruk ya kasance ma'abocin son zane, daidai da dakinsa idan ka shiga haka zakayita cin karo da takardu masu dauke da zane kala-kala. Sau da yawa haka mai gyara sashensa, Bala, zaiyita kwasarsu yana zubarwa. Son zanensa bai ragu ba saida ya soma aiki ka'in da na'in, alokacin ya zamana babu kwakkwarar lokacin zane, wani sa'in kuwa sai ranar da babu aiki yakan ta6a. Idan kuwa ka ganshi a falo, to fa hira ce ta motsa. Kokuma yan uwansa sunzo nan zasu had'u suyita kwasar hira suna dariya har mahaifinsu.
Rayuwarsu tana tafiya cike da sha'awa, ga ilimin addinin da na boko. Babu mai takurawa wani, hakan bai hanasu kiyaye dokokin Ubangiji ba.
WANNAN KENAN..
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
30
Alhaji Muhammad zaune a k'ayataccen falonsa bayan ya kammala cin abinci. Ya kai duba ga sanyin idaniyarsa da ta fito daga d'akinnasa bayan kammala feshe d'akin da maganin sauro, murmushi suka sakarwa juna, ya rik'o hannunta ya zaunar da ita a gefensa.
"Bakya tsufa Madina, menene sirrin?"
Mami tayi dariya gami da yin farr da ido.
"Oh Abban Ihsan, kai dai kullu yaumin baka rabo da zolaya."
Ya yi dariya.
"Ina zolaya anan? Babu sai tsagwaron gaskiya."
Sukayi dariya. Ya rik'o yatsunta yana murzawa.
"Kiramin d'ana."
Ta cire yatsunta, zata mik'e ya dakatar da ita.
"Ina wayarki? Kiyi amfani da ita mana."
Ta sa hannu ta dauki wayar a saman tebur kafin ta hau laluben lambar Adnan.
Lokacin yana zaune a falo suna kallon Dadin Kowa suna kyakyata dariya har Ummi dake gefe zaune.
Bayan ya d'aga ta sanarmishi kiran Abba, a take ya mik'e ya fita.
Da sallama ya shiga falon bayan sun amsa. Ya k'arasa ga Abbansa ya zauna agefen kafafunsa.
"Abba gani."
Da murmushi saman fuskarsa ya dubi d'annasa.
"D'an Abba, ya makaranta? Naji kun soma jarabawar karshe ko?"
Adnan ya sosa kai yana murmushi.
"Eh Abba, komai yazo karshe in sha Allah."
Abba ya jinjina kai.
"To haka akeso, Allah Ya taimaka."
Mami da Adnan suka amsa. Ya cigaba da magana.
"Kaje kayi nazari dakyau, saika zo ka sanarmin makarantar da kakeson zuwa k'aro karatu a k'asar waje. Kada kayi gaggawa ka bi sannu, idan ka sanarmin sai mu bincika mu ga yanayin ingancinsa. Allah Ya yi maka za6i na alheri."
Wani dad'i ya daki zuciyar Adnan, ya yita nanata ambaton Allah a zuci, a k'arshe cikin tsananin murna da d'oki ya hau yin godiya ga mahaifinsa. Haka ya tashi ya koma falon Mami cikin tsananin murna.
Yana shiga ya saki k'ara don tsabar farinciki har yana doka tsalle. Tunda suke basu ta6a tsallaka Nijeriya ba, sai a wannan karon da yake fatan burinsa ya cika.
Gaba daya suka zubamishi ido. Ihsan a guje ta taso.
"Yadai broda?"
Nan ya sanarmata, ai don dadi itama ihun ta sanya gami da rungumeshi, shima Fahad agefe yana tsalle. Ummi kanta itama saita tsinci kanta cikin farinciki matuk'a, domin burinta ta ga duk wani masoyinta cikin farinciki.
Ya yi dakinsa a guje, Ihsan ta mara mishi baya tana mai cewa.
"Yi browsing mu dudduba makarantun."
Bayan shigewarsu ta numfasa, babu jimawa da shigarsu wayar Adnan ta dauki k'ara. Da sauri Ummi ta mik'e ta dauka da zummar kai mishi.
Hoton Faruk ta ci karo da shi 6aro-6aro akan screen din wanda Haidar ke rik'e da hannunsa shi kuma yana dubansa da murmushi mai bayyana hak'ora. Gaba d'aya sai ta tsinci kirjinta na bugu.
"BRO FARUK." Sunan dake saman screen din kenan, ta ajiye wayar da sauri, ta kama hanyar d'aki har lokacin wayar na k'ara, haka ta juya ta koma ta dauka. Haka kawai ta tsinci kanta da d'agawa batare da tasan dalili ba. Ta gwada (sliding) wajen koren kamar yanda ta sha ganin Adnan ya yi idan zai d'aga waya. Cikin sa'a kuwa ta soma jin maganarsa yana sallama.
Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata, jin maganar Adnan kawai ta yi a kanta.
"An kirani ko?"
A razane ta juyo ta mik'amai. Kasa magana tayi sai kai data gyad'a. Allah Ya taimaketa batare da Ihsan suka fito ba.
Ta juya da sauri ta nufi dakinta. Tana ji sadda yake fad'in.
"Afuwan dan uwa wallahi Ummi ta d'aga, fitowata kenan daga d'aki."
Daga haka ta shige ciki da sauri.