← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 116

Sashe 44

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

61
  Zaune ta ke a (Garden) tana wanke kayanta kala daya, tana yi tana dan wak'e-wak'enta. Bata da masaniyar cewa Faruk na daga barandarsa yana kallonta, a gabansa abin zane ne. Ya jima yana dubanta da murmushi dauke a saman fuskarsa kafin daga bisani ya hau zanata. Iyakar fuskar kawai ya zana, bayan kammalawarsa ya mike ya sauka.
  Ba zato ta ji shi zaune a gefenta saman kujera. Ta dubeshi gabanta na dukan uku-uku sannan ta dubi hanya.
   "Kar6i wannan kiga, hoton matar da zan aura ce."
   Gabanta ya fadi, ta dubi takardar da ya kanannad'e sannan ta dubeshi, shi dinma ita ya ke kallo da son lura da yanayinta. Murmushin yak'e ta yi.
"Hannuna da ruwa, kada na jik'a maka."
   "Kar6i ba komai."
Ta sa hannunta wanda ya soma rawa ta kar6a. Koda ta bude, kallon tsoro ta yiwa zanen don kuwa wani kishi ta ke ji yana sukar zuciyarta. 
   "Ta yi kyau, Allah Yasa alheri."

"Ameen, nagode." Ya fada yana dubanta, ya tabbatar bata kalli zanen sosai ba, wannan alamu ne na tana sonshi kuma tana kishinsa hakan kuma ya mishi dadi. 
   Ya dan lek'a fuskarta.
"Za ki halarci bikin?"
Ji ta yi kamar ta kai mishi bugu, ashe komai da ya ke fadamata a baki ya tsaya? Daman itama ta yi wautar daukar zantukansa ta saka a rai. Yaudarar kai kenan. Ta kauda fuskarta gefe.
"Um."
Ya yi wani murmushi.
"Mungode."
Daga haka ya bar wajen, ta bi bayansa da kallo, daidai da fatarsa fara k'al kalar 'ya'yan hutu ne, ina ita ina shi ne? Bata kyautawa kanta da rayuwarta ba da har ta bari kaunarsa ta shiga ranta. 
  Ta k'ara duban takardar cike ba tayi wata-wata ba ta d'aga da zummar yagawa saidai me? Karo ta ci da wata mai kama da ita, ta zaro ido tana k'ara duba sosai, shakka babu ita ce, har  dan lotsawar kumatunta. Kunya ta kamata, shikenan Faruk ya gane tana kishinsa tunda har ta kasa 6oyewa. Kamar ance ta daga kanta, sukayi ido hudu da shi daga barandarsa. Ya kashemata ido daya, ta yi saurin mikewa ta bar wajen tana murmushi tare da mamakin yanda akayi har ya isa ga dakinsa, kodayake ba wani nisa ne daga nan ba.  Ta adana takardar cikin kayanta, saida ta tabbatar ya bar wajen sannan ta koma ga aikinta.

  Ihsan ta dubi Ihsan fuska a washe.
"Kina ganin hakan yafi?"
  Ikram tana murmushi ta gyada kai.
"Kwarai kuwa, ke kanki kusan komai zai fi zuwar miki da sauki, kinga cikin kyautar da za ki ba shi sai ki isar da sak'onki ta nan."
Ihsan harda tsalle ta yi ta rungume Ikram.
"Yaushe ya kama ranar haihuwar tasa?"
  Ikram na dariya ta amsa.
"Jibi ne, sha shida ga watan (March), kada mu sanarmishi batun fatin, ya kasance mun bashi mamaki, saidai ya dawo gida ya tarar da komai."
  Sukayi dariya.
"Daidai kenan." Cewar Ihsan.
"Naji, taso muje mu yi shawara da Hajiya."
  Koda suka je, batun fatin kawai suka sanarmata, nan kuwa ta basu goyon baya dari bisa dari don Faruk tun yana da shekaru ashirin rabon da ayimishi wani birthday party. Ta taimaka musu da kudade suka soma shiri da sanin Daddy da yayyunsa maza har ma da matansu. Duk uban gayyar ma baida labari, asalima ya mance da wani batun ranar haihuwarsa da ta kusan zagayowa.
                    ***   ***   ***
                        RINGIM 
   Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba don kuwa a ranar litinin Deen ya iso da wani baffansa wanda shi kadai ya samu dakyar ya lalla6a akan zai nema mishi auren Dija, iyayensa dai sunce babu hannunsu hakanan basu yarje mishi ba don wannan cin amana ne, saidai adalilin makancewa da ya riga ya yi a son Dija ko kusa bai dauki maganarsu da girma ba, haka ya samu wani kanin mahaifinsa ya shige mishi gaba. Koda suka zo ga Malam Yahuza, ba yanda ya iya hakanan ya kar6i kudin auren shi da wani makwafcinsa, a karshe aka tsaida maganar aure nan da wata daya kamar yanda Deen ya nema, Malam Yahuza ya zo mishi da korafin cewar sai ya shirya amma Deen ya tabbatar mishi matukar saboda kayan d'aki ne, to fa ya dauke mishi komai. Sun cika da mamaki kwarai, shi kuwa Deen ji ya ke yi idan har baayi auren nan ba, to kuwa so da shaawar Dija zasu iya mishi lahani.
   Kafin kace me, gari ya dauka cewar Malam Yahuza ya kar6i kudin auren Dija daga Zahraddeen miji ga'yar uwarta. Ai kuwa magana har gidan iyayen Munira. Sai ga mahaifiyar Munira da kanta, Bilkisu ta zo har gidan. 
  A tsakar gidan ta iske Malam Yahuza da Habiba, da sallama ta shiga suka amsa. Habiba ta saki fuska.
"Aa, Bilkisu kece tafe? Karaso mana."
  Bilkisu ta zauna saman kujera yar tsugunno sannan ta dubi dan uwanta dake cin magani kamar ya ga kashi.
  "Yaya ina wuni."
"Lafiya." Ya amsa dakyar, ta gyada kai, bata wani damu sosai ba tunda daman haka ya saba amsa gaisuwarsu a wasu lokutan idan Habiba ta murda kambunta.
  "Wani labari na ji a gari shine na zo don tabbatar da gaskiyarsa."
  Habiba murmushi kawai ta ke, Malam Yahuza ya kara tamke fuska, acan kasan zuciyarsa ko kadan bai jin dadin abinda ke faruwa saidai ba halin nunawa tunda yana gaban sarauniyartasa.
   "Wane magana kuma?"
"Wai Zahraddeen zai auri Khadija?"
Kafin ya yi magana Habiba ta amshe.
"Gaskiyar maganar kenan Bilkisu, yanzu nake shirin aikamuku cewar ku zo amsar kayan saka rana da lefe jibi, sai kuma ga ki da kanki don Allah ki aika a gayawa sauran dangi na kusa da ke."
    Bilkisu ta rasa me za ta ce, tsananin mamaki da tsoron hali na DAN ADAM su ne suka fi cikata. Ganin abin ta ke yi kamar almara, kamar dai a ire-iren litattafan da ta ke sauraro a shirin Rai Dangin Goro, ashe da gaske yana zama gaske?
   Ta mik'e tsaye sakamakon ruwan hawaye da ya soma kwaranyo mata a saman fuska. Ta dubi dan uwanta.
"To madallah, nagode kwarai da wannan cin amanar zamantakewar, babu abinda zance muku saidai duk wanda ya yi mai kyau kansa, akwai ranar k'in dillanci. Tabbas kun nuna hali irin na DAN ADAM na butulci, amma bakomai, Allah Yana nan."
  Daga haka ta sanya kai ta fice tana share fuskarta da mayafi. Tana jin sababin da Habiba ta ke yiwa yayanta akan yana ji ta ci zarafinsu bai dauki wani kwakkwarar mataki ba. 
   Koda Bilki ta isa gida saida ta sha fadan mijinta Malam Amadu akan dalilin da yasa bata bi maganarsa ba ta je gidan, ya kuma gargadeta akan kada ta sanarwa diyartasu tukunna har sai anga abinda hali ya yi. Daga wannan suka rufe maganar sai jimami da tunane-tunane. 
                  ***   ***   ***
                      ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 44 · 0% Book details