Sashe 76
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Da ni da mahaifiyarki duk yan gari daya ne, wato Gombe. Saidai ita din ta yi rayuwa ne a kauyen Jar Kwami dake Gombe. Da mahaifinta, Malam Manu(Usman) da kuma mahaifina Malam Buba(Abubakar) aminan juna ne wanda amintarsu ta samo asali tun kan iyayensu wanda tarihi ya nuna suma haka suka taso kansu a hade.
Malam Buba bayan aure ya koma cikin birnin Gombe da zama Unguwar Tudun wada tare da mahaifiyata Fatima wacce muke kiranta Dada. Yaransu bakwai, uku sun rasu, ya yi saura daga Haruna, Baffa(wanda ya ci sunan Usman baban Hasiya) sannan ni Abdullah wanda hasken fatata yasa suke kirana da Balarabe sannan kuma kanwarmu Aisha.
Gaba daya danginmu bamu da yawa sosai don bamu kai yawan dangin mahaifiyarki. Mahaifinta d'a ne ga Muhammadu Lamido, tsohon Sarkinmu na kauyen Jar Kwami, kafin ya mutu yana da mata har hudu banda uku da suka ta6a rabuwa duk kuma sun ajiye mishi yara, mata sunfi yawa cikin yaransa, bayan mutuwarsa aka dora wani kan karagar mulkin don alokacin yaransa maza su uku duk basu kai minzalin rike mulki ba.
Koda lokacin ya yi, babban yayansa ne kawai ke shaawar mulkin sam kakanki Malam Manu(dansa na biyu) ba ya so.
Gaba daya a gidan sarautar su ke zaune, manyansu da yaransu. Sai kuwa matan da aure ke rabasu da gidan, wasu cikinsu ma auren gida ake musu da yaran yan uwa.
Duk cikin yaran Malam Manu, mahaifiyarki ce k'aramarsu, babban dansa namiji ne, Ado sai Bilkisu, Safiya, Asma'u sannan Mahaifiyarki Hasiya saidai Boddo suke kiranta, wato mai kyau. Don Masha Allah duk cikin yaran Malam Manu babu mai kyawunta. Innarsu Aisha da suke kira da Inna tun bayan haihuwar Hasiya suka koma kiranta da Inna Boddo.
Tun farko anso yi mana auren zumunci da mahaifiyarki tun ma bata isa aure ba, amma fir na k'i sakamakon soyayyar da muke yi da Saude diya a wajen wata mai siyar da abinci a tsohuwar kasuwa inda nan nake zuwa siye da siyarwa. Asalinsu yan Kano ne can kauyen Ringim, saidai aure ne yasa Atine uwa ga Saude baro garinsu zuwa nan Gomben, bayan rasuwar mijinta ne ta fad'a harkar siyarda abinci. Saude kadai ce diyarta, nakan yawaita zuwa shagonnasu daga shagon yayana dake zuwa Kano saro yadikan maza, haka har muka saba da Saude kafin kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninmu. Kullum kwanon abincina na rana anan ya ke.
Ranar da na zo wa mahaifinmu da maganar auren Saude, sam bai aminta ba don kuwa ya ce shi fa ba ni da mata sai Hasiya, lokacin idanuna sun rufe na ce bana sonta, nan duniya Saude kadai ce abar sona.
Akan wannan saida ran Malam ya 6aci ainun, ya budemin wuta sosai. Har ya yanke shawarar zuwa Jar Kwami don ayi wacce zaayi, hankalina ya tashi, ina gani babu wanda ya goyi bayan na auri Saude. Karshe kuwa da ni aka je Jar Kwami, koda Malam ya gama magana akan aurena da Hasiya, Malam Manu ya aminta kuma ya ji dadi sosai, saidai ya bawa Mahaifina hakuri inda ya nunamishi har lokacin Hasiya bata kai munzalin aure ba saidai ko ta zo a ta biyu. Malam fir ya k'i amincewa, ya jajirce akan lallai a daura aurenmu da Hasiya.
Koda na sanarwa Saude halin da ake ciki, ta shiga tashin hankali matsananci ga shi a wannan lokacin mahaifiyarta na shirin zuwa ganin gida can Ringim. Ana gobe za'a daura aurena da Hasiya na bi Saude da babarta zuwa Ringim don kuwa a wannan lokacin ji mu ke yi idan ba mu auri juna ba to fa za mu iya rasa ranmu. A hanyarmu muka yi hatsari mahaifiyar Saude ta rasa ranta, har suma saida Saude ta yi don tashin hankali, inda ma aka ci sa'a Sauden tasan garin tana zuwa. Da taimakon jamaar gari da kuma kwatancen Saude, Allah Ya yi isarmu gidan Kawunta Isah, anan aka yiwa mahaifiyarta jana'iza bayan nan Saude ta gabatar da ni matsayin wanda za'a auramata, ta sanarmusu wannan ne musabbabin zuwanmu garin. Koda aka nemi sanin tarihina, muka rufe komai muka nuna cewar ni din maraya ne, dangi kuwa sun sakoni gaba, babu mai kaunar ya ra6eni. Kawu Isah bai so aurennan ba don yana ganin kamar mun 6oye wani abu bayan wannan, saidai ganin yanda Saude ta tada hankali ga kuma maraicinta da ya duba hakanan itama bata samu wani sukuni daga dangin ubanta ba, ya amince ya daura aurenmu, gidannan da ki ke gani nawa ne, a farkon zuwanmu gidan Kawu Isah muka zauna har na tsawon shekaru biyu kafin na samu abin hannuna ta hanyar sana'o'i daban-daban na gina wannan gidan ginin k'asa. Wannan na sumuntin duk na yanzu ne. (Ya yi nuni da bangon gidan sannan ya dora). Tun zamanmu tsawon shekarun nan Yahuza mijin Habiba makwatanmu ne, yanda na saba da Yahuza haka Saude ta saba da unguwar zoma Habiba kusan ma da ya ke su mata ne shakuwarsu ta fi namu.
Ashe su kuwa acan da na tafi sun daura aurena da Hasiya, saida watarana tunanin gida ya addabeni tashi guda na ji inason komawa Gombe. Zuwana na ji labarin rasuwar mahaifiyarmu da kuma auren kanwata Aisha. Na yi kuka kwarai, Malam kuwa ko kallon inda nake baiyi ba. Gwara ma yayyuna sun saurareni, Haruna da kansa ya bani shawarar zuwa ga Malam Manu don shi kadai ne zai iya shawomin kan mahaifina ya yafemin. Banyi kasa a gwuiwa ba washegari na wuce Jar Kwami. Malam Manu kusan ya yi murna kwarai da ganina, yanda ya kar6eni har kunya na ji don ban ta6a daukar an daura aurena da diyarsa Boddo ba. Ya bini doguwar nasiha, karshe washegari muka wuce cikin Gombe.
Malam ya tabbatar ya hakura muddin zan ba shi takardar Hasiya, ashe ma tun bayan auren aka kawota gidanmu saboda gudun maganar mutan gari.
Malam Manu kuwa ya ce bai isa ba, babu mai kunce aurennan, ni kaina ba zanso hakan ba. Dakyar da sidin goshi Malam ya hakura saidai ya ce nan zan zauna da Hasiya. Nan ma ansha artabu kan ya amince da tafiyarmu Ringim da ita. Saida na yi sati uku kafin na taho da Hasiya da yayyunta da wasu cikin dangi duk don a ga waje.
Ina cike da tsoron irin kallon da Saude za ta yiwa lamarin, saidai ga mamakina ta nuna ta fini farin ciki, har da durkusawa ta yi ta nemi gafarar yan uwana acewarta itama ta yi musu laifi na rabasu da ni. Wannan abu ya k'aramata k'ima a wajena, haka suma yan uwana suka cika da farinciki fad'i su ke, "Balarabe ka yi dacen mace ta gari." Har suna kwatantawa Hasiya da ta yi koyi da Saude. Ko bayan tafiyarsu na barwa Hasiya dakina, daman dakuna uku ne a baya, daya a zaure sai biyun nan kafin yanzu da aka yi ciki da falo.
Zaman lafiya suka gudanar, hakurin Hasiya da kyawawan dabi'unta su suka sanya ni cikin shaukin so da kaunarta ainun, abin Allah sai Ya doromin so da kaunarta fiye da irin wanda na yiwa Saude. Dakyar nake kokarin kwatanta adalci atsakaninsu.
Alokacin ne kuma Saude ta soma nunamin damuwarta kwarai akan rashin samun ciki. Kullum cikin yi mata nasiha nake, saidai takan yawaita tambayata kudi na zuwa wajen wata mai maganin gargajiya da aminiyarta Habiba ta bata labari na wai tana bada maganin samun ciki. Duk yanda na so fahimtar da ita cewar haihuwa lokaci gareshi, bata fahimta ba.
Haka har Hasiya ta samu ciki, kusan Saude ta fimu nuna murnarta, har kuma ta raineshi Saude har ayyuka ta ke kar6amata, magungunan gargajiya duk da tasan zai amfaneta takan kawo, haka itama Habiba ta kyautatawa Mahafiyarki, Allah kadai yasan zuciyoyinsu, ko tun wancan lokacin da gaske suke nunawa Hasiya kauna, ko kuwa dai da biyu su ke yi? Ba zan ce komai akai ba don bani da tabbas.
Cikin ikon Allah cikin Hasiya ya kai wata tara, tana haihuwarki kuma sai Allah Ya dauki ranta."
Malam Balarabe yana kaiwa nan ya dubi Ummi ya na mai haska wayarsa sakamakon wutar da tuni aka dauketa. Ummi hawaye ta ke yi don ita tasan duk ba don Allah suka yi ba, ta sha ji suna hirar, Allah ne kadai ya yi itama za'a haifeta don tun tana ciki aka so cikin ya zube, cewar Saude kenan duk sadda ta ke goranta mata da zaginta a baya.
"Hasiya ki gafarceni, bansan dukkan abinda ya biyo baya ba bayan mutuwar mahaifiyarki, don lokacin gaba daya tsanarki ce ta dirar min, su kansu yan uwana sai suka fita hanyata haka kema daga dangin mahaifiyarki babu mai zuwa su ganki. Sun aminta da Saude fiye da zatonki, kamar yanda nima na aminta da ita ta yimin halin DAN ADAM na butulci."
Ya karashe yana mai share hawaye. Murmushi Ummi ta yi gami da kamo hannun mahaifinta....
((Inda gyara kofa a bude ta ke [email protected] ko fcbk.. Rufaida Omar))
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
94