← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 116

Sashe 112

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna daga dakin suka ji falon ya dauka ga Ango ga Ango, da mamaki Baraka ta ce. "Eh lallai yar gatan yayanta, kiga har ya shigo." Ihsan wacce bata jima da shigowa dakin ba batasan me akeyi ba, sai ganin Abubakar ta yi ya shigo. Tana zaune saidai ban ma lura da ita ba ya yi wajen kanwarsa. Itama tana ganinsa ta kara turo baki tana murmurza idanuwa. "Ya Salam, meyafaru ne wai kanwata? Hankalina ya tashi wallahi." Ganin yanda duk ya rude yasa ta dan sassauta fuskarta, fuska ba walwala ta ce. "Ba shine ya ce wai bazan je dinner party ba." Ya dan runtse ido gami da numfasawa, hankalinsa ya dan kwanta. "Inji wa? Ai ya zama dole ku je don kafarki kafata. Barni da shi, kedai ki tabbatar kin shirya kinji ko?" "Yanzu bayanta za ka goya? Da wannan tulelan cikin ina ita ina wata dinner?" Cewar Rahila yayar Ihsan. Ya dan harareta don sun saba wasa da dariya. "Ina ruwanki to? Zuwa kuma ai ta yishi ta gama, atoh." Dariya sukayi banda Ihsan da ta k'ulu ganin kamar baisan da ita wajen ba. "Idan kaine mijinta ma ji ma gani." Ta kara fadi cikin dariya. "Shima a tafin hannuna ya ke, surukai muke." Daga haka ya fice suna mishi tsiya. Ihsan jikinta ya yi sanyi, wane irin Ango ne mai fifita wata akan matarsa? Haushi ya cika zuciyarta saidai dole ta danne ta mike bisa umarnin Aisha wacce ta shigo kiranta zuwa kwalliya don Magriba ta gabato kuma ana sallar Isha zaa wuce. Ya murza karan hancinsa gami da dora kafa daya kan daya kamar wani basarake yana dubansa. "Ka ce me?" Abubakar ya harareshi. "Na ce idan Inno ba zata je ba to fa nima babu inda zanje, kafarta k'afata." Wani murmushi mai burgewa Faruk ya yi kafin ya dubeshi. "Shikenan, ai ba kai kadai ne Angon ba, sai muje mu sha shagalinmu." Dariya su Haidar da Kb su ka yi don duk gaba daya suna zaune a babban falon na bak'i. Abubakar cikin dariyar ya amsa. "Kafata kafarta fa Malam, ai ba yawo za ta yi ba, wuri daya zata zauna." Baki Faruk ya ta6e baice uffan ba, yana ji Abubakar ya dauki waya ya kira Ummi gami da kara jaddadamata cewa ta shirya zuwa babu fashi don ya amince. Ya kalleshi kawai ya kauda kai kawai. Haka har aka tashi tafiya, idan kaga Amarennan saika k'ara kallonsu tsabar haduwar da sukayi domin kuwa wani arnen leshi suka sanya fari da silver ya zauna das a jikinsu., su kuwa Angwayen farin shadda k'al mai surfani ruwan toka suka sanya. Saura kuwa suka yi ankon bulun french lace mai ratsin ruwan toka sai silver head, yayinda tawagar samarin suka hade cikin (Sky blue)shadda, sunyi kyau har sun gaji da haduwa. Kowa ya shirya tsaf harda Ummi, ita buba ta yi na zani sannan ta dora mayafi ruwan toka-toka, ta yi kyau duk da cewa ta ajiye kumatu ga chanjin fuska da jiki sakamakon ciki. Aka soma fita itama ta fito, Mami ta kama ha6a. "Harda ke Ummi?" Hakan yasa sauran iyayen suka dubeta. Ta yi murmushi. "Eh Mami." "To ki bi a hankali banda tsalle-tsalle don Allah ki zauna wuri daya." Fadin Hajiya Mama kenan don wannan karon banda manyan iyaye a zuwa. Da haka Ummi ta fita ta na cigaba da gwada kiran Faruk wanda ya kashe wayoyinsa kaf. Takaici ya isheta, a waje ta tsaya tana waige-waige, motoci masu tsada sun cika farfajiyar gidan wasu kuwa da basu samu shigowa ba suna daga waje, to biki ne bana mutum daya ba, Hajiya Lubna itama yan uwanta na Maiduguri sunzo da yawa don bata ta6a aurar da diya ba, hakanan Hajiya Binta wacce rabin yan uwanta a Kano suke, su dinma duk hallara. Tana nan tsaye anata tafiya ta hango Gidado na kokarin shiga mota da sauri ta karasa gareshi. "Yaya Gidado." Ya waigi, yana ganinta ya karaso ya cimmata ganin yanda ta ke tafiya da sauri. "Yi a hankali mana Ummi, za ki je dinne?" Ta gyada kai gami da yin narai-narai da fuska. "Eh, ina Yaya Faruk?" Ya yi murmushi. "Yana kofar gida amma nasan yanzu sun wuce, taho mu tafi kawai." Ba musu ta bi bayansa, kafin ta kai ga shiga wayarta ta dauki k'ara, Abubakar ne. Ya tambayeta ko tana ina, ta sanarmishi gatanan za ta bi Gidado, ya ce ta jira tare zasu wuce. Ta amsa da toh gabanta na faduwa, kada fa ya zamana Faruk bai yi na'am da zuwannata bane, to amman ai Abubakar bazai mata karya ba tunda ya ce ya amince ta je. Aikuwa motar Ango da Amarya ta hau, gidan gaba ta zauna, Kb ne matuk'in Abubakar da Ihsan. Ihsan ta ci magani ganin Ummi k'ame a gaban mota, har akaje ba ta ce uffan ba sai kuwa Abubakar da Kb ke kwasar hirarsu, jefi-jefi sukan sanyo Ummi da Ihsan, motocin Amare a jere haja suka isa. Gaban Ummi ya fadi ganin Faruk zaune saman mota a farfajiyar wajen tare da Jafar abokin aikinsa suna hira. Ya yi kyau har ya gaji da haduwa. Tun shigowar motocin idanunsa suka hangomishi matarsa a gefen mutumin da har gobe bai mance abinda ya so aikatawa ga iyalinsa ba, wato Kb. Wani abu ya soki kirjinsa, kishi mai tsanani ya turnuk'eshi x ya dauke kai fuskarsa kamar an aikomishi sak'on mutuwa, wannan ba karamin firgita yan hanjin cikin Ummi ya yi ba, ta hau karanto adduo'i cikin ranta har motar ta daidaita fakin, har Amarya da Ango saida suka rigata fita, sannan a karshe ta daure ta bude mota ta fito, nan masu hoto suka yi musu ca, da sauri ta samu ta bar wajen ta nufi wajen mijinta, saidai babu shi babu dalilinsa, can ta hangeshi wajen Angwaye suna gaisawa da Abokai, jiki a sanyaye ta koma ta shiga ciki, saidai me? Zaman namiji da mace ne, ga mai aure da matarsa, marar aure kuwa budurwarsa. Intisar ana k'ame gefen Haidar, hakanan su Jidda, ta yi shiru ta kasa karasawa ciki dole ta juya da zummar fita saidai ta ji an riko hannunta. Da sauri ta dago kanta, Faruk ne saidai fuskarnan tasa babu digon walwala ya ja hannunta zuwa ciki, ta kasa cewa uffan ga uban tsoro da ya cikata kamar ta saki fitsari a wando, ya dan saki fuska gudun kada a dagosu, itama ganin haka ta saki nata. Haka suka karasa mazauninsu kusa da su Ridwan. "Madam daga nan sai Asibiti ko?" Cewar Ridwan cikin zolaya. Murmushi kawai ta yi. "Kema dai Ummi, ai da kin hakura kin zauna gida." Fadila wacce ta sauko yanzu ta fada da murmushi saman fuskarta. "Ina zata zauna wata ta yi mata kwace? Da gaskiyarta ai." Haidar ya fada yana yar dariya, hakan yasa Ummi fadada fara'arta wanda duk yak'e ne ganin gogannata bai wani sakarmata ba, sai murmushi da ya ke wanda ya zamto yak'e. "Au Madam ashe kinga ogannaki ina can ina nemanki naga kamar ba ki shigo ba." Suka tsinci muryar Kb daga gefe, ta yi yar dariyar yak'e tana fargabar abinda zai biyo bayan amsawarta. "Um, na shigo yanzu." "Yauwa." Daga haka ya maida akalar hirar da Haidar dake tambayarsa ko da wa zai zauna. Ya nunamishi wata cikin kawayen Ihsan wacce a ganin farko ta kwantamishi. Can kuwa Gidado na tare da Ikram kamar su hadiye juna don so. Party ne na yan boko, komai bisa tsari aka yishi, ba'ayi wani raye-raye sosai ba, sai ko (step-dance) da dangin Ango Abdullatif suka shirya suka yi wanda ya k'ayatar sosai. Anci an sha, an kuma yiwa Angwaye da Amare lik'i kwarai. Kafin akai ga tashi ta soma buga uban hamma don ta gaji ga bacci dake cinta, ta dubi Faruk da hankali kwance ya ke kur6ar lemu abinsa, lokacin su kadai ne saman tebur su Babban Yaya da sauransu an tafi daukar hoto. "FAR HAS na gaji wallahi bacci nake ji." Ko kallo bata isheshi ba, kamar ba da shi ta ke magana ba haka ya nuna. Jikinta ya kara sanyi, ta lalubo hannunsa na dama ta matse cikin nata. "Don Allah ka yi hakuri na yi maka lai..." Kallon da ya watsamata ne yasa ta hadiye maganarta babu shiri, har lokacin hangota ya ke zaune kusa da Kb a mota. Ya zare hannunsa cikin nata. "Ai ba ni na kawoki ba, ki nemi wanda ya yi miki iznin zuwa da wanda ya kwasoki a motarsa har ku ke hira da dariya su yafi dacewa ki je su maidaki." Hawayen da ta ke rikewa suka zubo. "Amma Yaya Abubakar cemin ya yi ka amince." "Tunda shi ki ke aure ai ya miki izni kin zo, shikenan kuma, komawa kuma ni ba yanzu zan tafi ba sai na gama abinda ya kawoni." Daga haka ya mike ya soma tafiya a kasaitance, tafiya mai cike da aji, babu budurwa da bata kyasa ba, ya wuce gurin Angwaye, yana zuwa ya fiddo rafar yan dubu-dubu ya hau lik'i. Nan wuri ya chanja, kida ya chanja, Mai wak'a ya tambayi sunansa aka sanarmishi habawa tuni ya hau wak'eshi yana mishi kirari da yayan Amare kuma Abokin Angwaye. Ummi hawaye ta ke na bakinciki da tsananin kishin yanda yan mata ke faman zubamishi lik'i shima, ji ta ke kamar ta dora hannu akai ta kwara ihu, ga bakincikin fushin da ya ke da ita, ga kuma na kishin mijinta. Mamaki ta ke na yanda yau bai damu da zubar hawayenta ba. Mikewa ta yi jiki a sanyaye, ji ta yi fatin ya fice a ranta, ita kuwa ko tasi ne zata hau ya maidata gida da dai ta zauna ta shak'i wannan kayan takaici. Tana jinta wani iri, Faruk bai kamata ace ta bak'anta mishi rai haka ba, idan da alk'awari sam Faruk bai kyautu ta musgunawa zuciyarsa ba, ya cancanci komai daga gareta. Haka ta ke faman tunani har ta fito farfajiyar dakin taron. Nan kuma ta shiga rarraba idanu, to ina zata nufa? Waya ta ciro da zummar kiran Abubakar sai ta tuna abinda Faruk ya ce kawai ta fasa, ta maida wayar jaka ta soma tafiya tana fatan ganin direban gidan su Mami ko Hajiya Mama don ya maidata gida, saidai akwai mutane da motoci
Chapter 112 · 0% Book details