← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 116

Sashe 105

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

   Tun daga wannan ranar sai ta ja shi da hira, abinda ya burge Gidado bai wuce ganin yanda koda wasa bata sanarmishi cewar tana sonsa ba, hakazalika babu ranar da bata tambayar Hafsa, har Anti ta lak'aba a farkon sunanta. Ya yi mamaki matuk'a don ya yi zaton zata dunga kishinta ko don ma yanda ya ke yawan yi mata zancenta, abin daure kan ma ita da kanta ta nemi ya bata tarihin farkon haduwarsa da Hafsa inda ya kirata suka dan ta6a hira kafin ya bata.
  Kishi fal ya cika kirjinta jin yanda ya ke kod'a Hafsa a zuciyarsa, saidai ya zata yi tunda ita ta nemi da ya bata labarin.
  "Ya ki ka yi shiru?"
Ta yi murmushin yak'e.
"Bakomai, kwarai soyayyarku ta burgeni, ina fatan nima Allah Ya bani miji wanda zai yimin irin wannan son da ka ke yiwa Anti Hafsa, ko fiye da hakan ma."
Ransa ya sosu, ta kuma ba shi tausayi, anya yana kyautawa yarinyarnan? Ya tuna ya cewa Abubakar suna hira sosai da ita, saidai ya 6oyemishi cewar bai yi mata wata magana da ta danganci soyayya ba.  
   "Hello." Ta fada muryarta a sanyaye. Sai lokacin ya tuna ashe waya ya ke yi.  Ya numfasa. 
  "Allah Sarki, Allah Ya ba ki fiye da ni."
   Ta gyada kai idanunta cike taf da kwalla, shakka babu Gidado fa ba sonta ya ke yi ba. 
  "Um, da wuya na samu hakan, koda zan samun ma bana bukata, nafison daidai kai din a komai da komai."
  "Kamar ya?"
Sai alokacin ta fahimci lallai su6utar baki ta yi. Ta yi saurin gyara furucinta.
"Eh idan na samu fiye da kai ai inajin mata ba zasu barni na huta ba, inada kishi kuma, banajin zan iya jure waccan ta kiraka waccan ta zo."
  Cikin dariya da muryar zolaya ya ce.
"Kuma gashinan kina shiga lokacin wata ko?"
  Itama dariyar ta yi.
"To ai ni kanwa nake wajenka."
Ya yi murmushi mai sauti.
"Hakane."
  Suka kara ta6a hira kafin su yi sallama. 
   Ta k'urawa wayar idanu kafin ta hau ambaton 'Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun', wannan ba karaalmar musiba bace ace kana son wanda ba ya sonka. 
   Ta k'ara daukar alkawarin zage damtsenta wajen kyautata mishi da yawan hira da shi da kuma danne soyayyarta, watakil a haka Allah Ya taimaketa ta ci galaba ya soma sonta.

      ***    BAYAN SATI UKU   ***

                GIDAN FAR HAS
Faruk ya jima da komawa bakin aikinsa, yayinda ya cikawa Ummi alkawari inda ya daukomata matar da zata koyar da ita karatu kafin zuwan lokacin da zata soma shiga aji. 
   Koyaushe soyayya suke zubawa, a wannan lokacin har Hajiya sun kaiwa ziyara, hakanan ya dauketa zuwa gidan yayyunsa, nan ma ta yi mamakin ganin chanji daga su Jidda duk kuwa da cewar bata iya ta saki jiki da su ba tunda basu saba da hakan ba.  
   A ranar wata laraba Faruk na tsaka da aiki ya tsinci kiran Ummi, a take ya ajiye biron hannunsa ya daga.
  "Assalamu alaikum Ummina."
Ta amsa da fara'arta kafin ta tambayi lafiyarsa. Ya yi murmushi. 
"Ganinan sai afkin tunaninki kuma ga ayyuka sunmin ca."
Ta yi murmushi mai sauti kan ta dora da fadin.
"Allah Sarki, Ummi ma ta kasa rabuwa da tunanin Faruk dinta."
Ya lumshe ido gami da jinginar da kansa jikin kujera yana murmushi.
"Kasan meyasa na kiraka?"
"Saikin fad'a tawan."
  Cikin shagwa6e murya ta ce.
"Fura nakeson sha."
  Ya yi dariya.
"Yau kuma gida ki ka tuno?" 
Itama ta dara.
"Dagaske wallahi, na kasa cin komai, shi kawai nakeson sha."
  Ya mike zaune.
"Ya Salam, meyasa tun dazu ba ki gayamin ba kuma ki ka zauna da yunwa? Bari nasa a kawomiki."
   "Yauwa FAR HAS."
  Tunda ya ke bai ta6a jin ta ce hakan ba, ya yi saurin jefamata tambaya.
"Me kenan?"
  Dariya ta yi ta katse kiran ta barshi sakato da waya a hannunsa ba tare da yasan tak'amaiman manufarta ba.
Tunawa da ya yi da furucinta na bata ci komai ba yasa shi saurin katse wannan gami da kiran Ado direban gidansu da zummar ya bashi aike. 
  Cikin mintuna da basu gaza ashirin ba ya je ya siyo damammiyar fura mai dadi ta cikin roba har guda biyar bayan ya kar6i kudin a hannun Hajiya daga nan bisa umarnin Faruk ya zarce ya kaiwa Ummi. Ai kuwa shi ta wuni a wannan ranar tana sha. 
Koda ya dawo suna zaune, yayinda ya ke cin abinci ita kuwa tana faman sha fura tana kallon talabijin, ya k'uramata idanu yana k'aremata kallo cikin lura. Ta tsargu, hakan yasa ta dubansa.....!
   DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

124

"Meyafaru?"
Ta fada cikin sanyin muryarta, ya dagamata gira yana mata murmushi. 
"Zo nan."
Ba musu ta ajiye robar furarta ta mike ta nufi inda ya ke gami da zama a gefensa, sanye take cikin riga iyaka gwuiwa da dogon wando(tight).  Ya janyota jikinsa. 
"Gaba daya kin chanja, anya babu ajiyata anan?" Ya karashe yana mai kai hannu cikinta gami da shafa. 
  Ta yi shiru, ita daman wata nada sati daya ta tare a gidan yanzu gashinan har watan ya cinye bata ga komai ba. 
Ya zungureta.
"Answer me."
Ta shagwa6e fuska.
"Nidai bani da komai."
Ya yi murmushi.
"Anya kuwa? Ji fa yanda ki ka k'ara girma a komai." 
Ta lumshe idanu jin yanda ya kasa tsayar da hannunsa wuri guda, da sauri ta zame ta koma gefe tana fadin.
"Kai FAR HAS abinci fa ka ke ci."
Ya yi mata duban rashin fahimta.
"Af, kinga na manta ko? Inason tambayarki ma'anar wannan FAR HAS din na manta."
  Dariya ta yi wacce ke burgeshi, bai iya 6oyewa ba saida ya furta, don Faruk sam bai iya 6oye abinda ya yi mishi, ko girki ta yi sai ya yaba balle idan idan ta ci ado, hakazalika duk sadda ya shigo gidan sai ya yaba da gyaranta, wannan ba karamin kara mata sonsa ya ke ba, babu macen da batason a yabawa kokarinta, wasu mazan nasu tunanin su kadai zasuyi ana yabawa, su ba zasu yaba naka ba, basusan cewa yabo na kara soyayya tsakanin maaurata ba,  koda ta yi ba daidai ba idan ka fada bazata ji haushinka ba saboda tasan ka yabawa kokarinta kafin haka. 
  "Har kullum bana gajiya da ganin dariyarki."
Ta rage dariyar tana murmushin jin dadin kalamansa.
  "Nagode FAR HAS."
Ta fada cike da zolaya, ya basar gami da maida kansa ga faranti yana murmushi. 
   Bai kara magana ba hakanan itama kowanne na bawa cikinsa, ita kuwa saida ta shanye robar fura tas. Lokacin shima ya kammala cin abincin ta dauke kwanukan sannan ta dawo ta zauna kusa da shi kamar yanda ya nunamata yafi bukata idan suna zaune. 
   Ya ja yatsun hannunta.
"Fadamin ma'anar FAR HAS."
Ta saki k'ara kad'an kafin ta turo baki.
"A kyauta?"
Ya na murmushi ya girgiza kai.
"Fad'i bukatarki."
  Ta kanne ido daya.
"Gobe a karomin fura."
Ya janyota ta yi filo da cinyarsa.
"Mai sauki kenan daga abinda za ki samu, just tell me."
   Ta lumshe ido tana murmushi.
"Faruk da Hasiya nake nufi."
Sai lokacin ya dan tsaya nazari kafin ya dubeta da mamaki ya na murmushi.
"Sunan ya burgeni ya kuma ban mamaki ta yanda har ki ka yi tunanin hadawa."
  Ta rufe ido da hannu tana murmushi. Ya sunkuyo da fuskarsa zuwa nata....!
Chapter 105 · 0% Book details