Sashe 63
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hajiya Mama na zaune a falonta tana kallo, yayinda Amina ke gefe daga kicin tana 6arar tafarnuwar girkin rana, yaran gaba daya sun wuce makaranta. Lokacin karfe sha daya na rana. Wayarta ta dauki kara, Hajiya Babba ce, gabanta ya fadi, to har yaushe ne za ta yi ta 6oyon wannan lamari ga yayartasu? Ta rage k'arar talabijin ta dauka. Bayan sun gaisa Hajiya Babba ta jefomata tambaya.
"Sadiya ya za ki 6oyen gaskiyar yanda ku ka yi da Madina?"
Hajiya Mama ta gyara zama, shikenan fa ranar da ta ke gudu ya zo don jin muryar Hajiya Babba ta yi duk a sanyaye. Kafin ta nemo abin fadi Hajiya Babba ta zayyane mata yanda suka yi da Madina ta waya. Ran Hajiya Mama ya 6aci.
"Bata isa ba wallahi ta yi kadan, auren Faruk da Ummi saidai ikon Allah ne kadai zai sa a fasa shi, Madina ta raina mutane. Hajiya kada ki soma yarda da wannan banzan maganarnata, itace sama da mu ne?"
Cikin damuwa Hajiya Babba ta ce.
"Sadiya zumunci nake dubawa, da dai Madina za ta yarda da tsarina da nafi kowa jin dadi."
"To Hajiya tunda ta nuna mana iyakarmu ba sai mu fita hanyarta ba? Ko ita ce ta haifemu?"
"Hannunka bai ru6ewa ka yanke ka yarr Sadiya. Bari dai zan duba na gani, idan na samu zuwa Kano a satinnan zan zo mu hadu a tattauna."
Hajiya Mama bata so hakan ba sai don dai Hajiya Babbar ta dage akan hakan ne, dole ta amince suka yi sallama akan hakan.
Amina dake kicin mutuwar tsaye ta yi jin an ambaci wata kamar Ummi kuam wai da Yaya Faruk aure. Anya kumnuwanta sun jiyemata daidai? Sai kuma ta ji Hajiya Mama na faman surutai tana fadin.
"Ai ba ita ta haifemu ba, a da Ummi ke yar aiki amma yanzu yarinya ta tashi anan, sai ta hada diyartata kishi da yayan masu da shi, shegantaka kawai."
Batasan lokacin da ta bar abinda ta ke ba tana salati, ta dafe kai don tsananin kaduwa, ji ta ke kamar ta saki fitsari anan, haka Ummi ta yi? Ina shawarar da ta bata? Shikenan ta kawo rarrabuwar kai acikin zuri'ar nan. Hawaye ta ji ya soma zubomata, inama tana da hanyar da zata bi ta samu Ummi koda ta waya ne su yi magana, anan kam babu abinda za ta ji sosai.
'Ba ki yiwa kanki dabara ba Ummi, ba ki kyautawa rayuwarki ba.' Ta fad'a a ranta cike da tausayin Ummin, kokisa bata son abinda zai ta6ata, ita mamakin ma karfin halinta ta ke yi na yanda ta iya bari suka kai ga haka da Faruk wai magana har kunnen iyaye? Sai kuma ta tuna abin na Allah ne, idan Ya yi babu mai iya hanawa. Ta sauke ajiyar zuciya.
'Allah Ya kauda dukkan fitinu. Ya yi miki za6i na alheri a rayuwa.'
Daga nan ta cigaba da aikinta bayan ta je ta rage marar, yinin ranar cikin sanyin jiki ta yishi, tunaninta ko wane yanayi Ummin ke ciki a Abuja? Tasan dai ba kowa ne zai so aurennan ba.
*** *** ***
BAYAN SATI DAYA
ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
81
BAYAN SATI DAYA
ABUJA
Ummi an soma gogewa, fatarta fara ta kara haskawa sai sheki da wani sul6i da jikinta ke k'arawa, hakanan har wata 'yar k'iba ta yi, Ikram kadai ce matsalarta sai kuwa Baraka da matar Babban Yaya(Fadila) da Jidda idan sun zo. Su dinma a fili suke nuna rashin goyon bayansu. Wannan abu na yi mata zafi saidai fad'an da ya fi karfinka....!
Hajiya Babba ta bi jirgi zuwa Kano ita kadai tun ran alhamis, gidan ya rage daga Ikram sai kuwa su din. Ranar Asabar misalin biyar na yamma Ummi zaune acikin (garden) tana sauraron wakokin hausa a waya wadanda Binta ta aikamata su da yawa, sanye take cikin wata atamfa ruwan madara mai adon fulawoyi, fuskarta fayau sai hoda da kwalli da ta sanya, kadan-kadan ta ke motsa lilon ta kwantar da kanta saman lilon idanunta a lumshe tana mai jin dadin wakar da ta ke bi na Alan waka na (Ummina). A hankali kuma hawaye suka soma zuba saman fuskarta, ta k'ara gyara zaman (earpiece) din kunnenta. Daidai lokacin da Faruk ya shigo gidan, dawowarsa kenan daga nan makwaftansu wajen wani dan makocinnasu mai mutunci da bai ji dadin jikinsa ba, kasancewar sun saba haduwa duk weekend yawanci anan kofar gidan su gaisa yasa koda ya ji ba shi da lafiya ya yi yunkurin zuwa dubashi. Yana sanye da riga koriya da wandon jeans bak'i, kai tsaye hanyar cikin gidan ya yi saidai idanunsa ya hangomasa sanyin idaniyartasa zaune saman lilo, ya dan kuramata ido duk a zatonsa ma bacci ta ke yi a hakan ganin yanda ta lumshe ido, ya taka a sannu ya karasa gareta, sai lokacin ya lura da(earpiece) dake a kunnenta ga kuma hawaye da ta ke zubarwa. Zama ya yi gefenta kamshi na turarensa ya ankarar da ita zuwansa. Da sauri ta bude idanunta gami da sa hannu ta share hawayenta, duk yana kallo saidai baice komai ba hannu yasa ya ciro kunne daya yasa a kunnensa, ya yi shiru yana nazarin wak'ar kafin kuma ya cire daga kunnensa yana mai dubanta, ta maida hankali ga wayar don kashe wakar.
"Kina tunawa da Ummarmu ne?"
Ta kasa magana sai gyada kai. Ya sauke numfashi.
"Hakan yana da kyau, saidai ba kukanki ne abin so awajenta ba, addua ya kamata ki yi mata idan har kina son ta yi farinciki da ke. Duk wanda ya mutu yafi bukatar adduarmu sama da komai."
Ta gyada kai.
"Hakane."
"Allah Ya jikanta."
"Amin."
Shiru ya dan biyo baya.
"Ni kuwa Ummi kin ta6a ganin hoton Ummanki?"
Ta girgiza kai, wannan ma na daya daga cikin abinda ke sosa ranta muddin ta tuno.
"Ko a hoto bansanta ba, nasan dai muna kama ta bakin matar babana shima sai tana zagina ta dunga hada yanayina da ita sai ko makwafta da zan ji suna fadin kamarmu da ita."
Ya jinjina kai.
"Allah Sarki. Kenan babu wani nata da ki ka ta6a gani?"
Ta amsa da eh.
Shiru ya biyo baya kafin kuma ya ce.
"Bayan wuya sai dadi in sha Allah, wataran za ki zama abin so da alfahari wajensu."
Ta yi murmushi don har cikin ranta ta ji dadin maganar.
"Allah Yasa."
"Amin."
Sun jima suna yar hira tana amsawa a kunyace kafin su mike su shiga ciki.
*** *** ***
KANO
Hajja ta dubi Fatima babbar diyartata da kulawa.
"Ke kam menene haka mai muhimmanci da ya taso ki daga Abuja zuwa Kano, maimakon ki bari tunda sati na sama ne zaayi taron zuri'a (family meeting) ku taho gaba daya da yara?"
Hajiya Babba ta murmusa, kwananta biyu kenan da zuwa amman kullum sai Hajja ta yi mata korafin zuwannata don gani ta ke yi kamar wata matsalar diyartata ta samu da maigidannata.
"Ke kam Hajja ba wani abin bane ba fa, daga zuwa ganinku duk kin bi kin damu kanki da tunani."
"A'a to, gani na yi ba ki saba wannan zuwan haka ba."
"To ke tunda kinsan bata saba ba, ai kinsan banza bazai kawota ba, akwai wani abun, bari yan uwannata su zo ko menene sai mu ji."
Cewar Dattijo Modibbo mahaifinsu.