Sashe 31
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Adnan ya kama hannun Maminsa tamkar ya rungumeta don murna.
Baraka da Ikram a guje suma suka fito har Hajiya Babba wacce ta kasa hakurin k'arasowar yan uwannata ciki. Ta rungume Innarta, su Amina da Ummi suka zagaya domin kwasar kaya.
Tana janye da katuwar jaka, idanunta ya sauka akan Faruk, yana gefe ya hard'e hannuwansa yana zabga murmushinsa mai burgewa. Sanye ya ke cikin kananun kaya, riga bak'a anyi rubutu da farin abu, wandonsa ma bak'in ne, ya yi kyau har ya gaji da had'uwa. Cikin sa'a idanunsa ya kai kanta sa'ilin tuni sauran sun kama hanyar cikin gidan. Murmushi ya sakarmata, itama ta tsinci kanta da mayarmasa da martani har(dimple) dinta na dama na bayyana. Ya ji wani abu da bai ta6a ji ba na tsirgashi, ya kauda kansa gami da soma tafiya zuwa ciki. Tana jan akwatin tamkar bata so sanadin kallonsa da take yi, namiji mai aji kenan, ina ita ina shi? Ta sauke ajiyar zuciya ta dubi gefenta jin alamun mutum. Amina ce itama rik'e da katuwar jakar Hajiya Mama tana dubanta cikin nazari, sai kuma bayan sun hada ido ta sakarmata murmushin yak'e.
"Muje mana naga bakya daga kafa ne."
Ummi ta gyada kai ta k'ara sauri. Amina mamaki kwarai takeyi na irin kallo da murmushin da ta ga Faruk na jifan Ummi da shi, da kuma kallon da Ummi ke bin bayan Faruk din da shi har ya illata tafiyarta. Ta numfasa, 'Idan ma akwai wani abun ya zama dole nasa ido na gano, bazan bari Ummi ta jefa kanta cikin matsala babba ba, ina mata kallon kanwata kamar ta jini.' Ta ayyana a ranta. Da taimakon yan aikin Hajiya Babba aka shishshigar da kayan gaba daya ciki.
Tsarin gidan Hajiya Babba wane sauran gidajen yan uwanta, iyakar haduwa ya had'u. Kayan duk ansaka a inda ya dace, Ummi da Amina daki guda aka hadasu wanda duk na yan aiki ne, yana daga can bayan(garden) din gidan.
Hira ta k'i ci ta k'i cinyewa tsakanin yan uwan, dakyar sukayi wanka suka chanja kaya sannan aka gabatar da sallar la'asar akayi zaman cin abinci. Alokacin kuma Haidar da Intisar suka shigo. Da gudu suka rungume juna ita da Ihsan sannan ta koma ga iyayen kowanne ta hau rungumarsa don dadi.
"Wai ke bakya girma ne?" Cewar Hajiya Mama kenan alokacin da ta rungumota.
"Kema dai kya fad'a Sadiya, yau kam dole kiban mijina tunda na iso." Cewar Inna kenan.
"Ahaf, mai zuwa gidanmu sai ya shirya fa." Fadin Haidar kenan, akayi dariya gaba daya. Su Faruk na daga falo suna jiyo caftarsu, shima Haidar bayan gama gaisuwa ya komo wajensu ana hira. Faruk kusan hankalinsa ya kasu biyu, hakanan ya ji yana d'okin ganin daga inda Ummi zata 6ullo, fatansa ya k'ara cin karo da kyakkyawar fuskarta. Da zarar ya soma tunaninta, sai ya yu saurin kwa6ar zuciyarsa, aganinsa babu wani dalili da ya ke da shi da zai dunga tunanin wata can. Abu ne da tun da ya ke a rayuwa bai ta6a faruwa gareshi ba.
Ita kuwa baiwar Allah, suna can tare da Amina suna cin abinci, saida suka kammala suka kai komai kicin. Alokacin ta fita wanka, bayan dawowarta itama Amina ta tafi wanko jikinta. Doyuwar riga ta sanya na kanti marar nauyi na yawon gida, itama Amina doguwar rigar ce jallabiya. Ummi ta dubeta taba daga rigingine saman katifa
"Anti ashe duk tsaruwar gidajen su Mami bai kama rabin k'afar na Hajiya Babba ba?"
Amina ta murmusa yayinda ta zauna gefenta.
"Haduwa ma ba daya ba kedai, na ji ance fa har wajen wanka akwai(swimming pool)."
Ummi ta zaro ido.
"Haba?"
"Wallahi a bakin su Anti Intisar na ta6a ji, ba don ma kada muyi laifi ba da mun zagaya gidan."
Ummi ta amsa.
"Wallahi kam, zanso ganin wajen wankan kuwa."
Haka sukayita hirarrakinsu, Amina na son yi mata magana akan abinda ke gudana tsakaninta da Faruk, tana kuma tsoron kada ya kasance zarginta ne kawai, wannan yasa ta barwa zuciyarta.
Sun sakankance suna hira har Ummi ta soma lumshe ido na jin bacci, ganin haka Amina ta kyaleta. Cikin baccin kuma ta ji ana tashinta, ta mike zaune tana murza idanu. Ta yi mamakin ganin lokacin Magriba ya taho.
"Ki tashi magriba fa ta yi, an turo a kiramu ma sai ni na je nayi aikin." Cewar Amina wacce ke kokarin gyara hijabinta bayan dauro alwala da ta yi. Da sauri ta mik'e ta fita zuwa bandaki domin dai bandakin yan aiki mata guda daya ne kuma ba cikin dakuna ya ke ba, yana daga dan lungun dakunan. Ta iske yan aiki biyu na alwala, ta gaishesu.
"Kece Ummi?"
"Eh." Ta amsa da murmushi. Suka saki baki.
"Kema kuma yar aiki ce?"
Ta gyada kai don ta soma mamakin tambayar.
Daga haka ta wucesu ta shiga bandaki. Tana jiyo hirarsu, daya na fadin. "Kinsan Allah Binta, da ace ni na samu kyawun wannan ba zan bautawa wasu a aikatau ba, na gwammace na ci duniyata da tsinke."
Bintar ta ja tsaki.
"Kedai matsalarki Sa'a kina da son maza kamar wata karya wallahi. Nayi zaton ma batun aure zakiyi."
Sa'a ta ta6e baki.
"Aurena biyu ban ji da dadi ba, don haka ko marmarin k'ara yi bana yi."
Lokacin Ummi ta fito sukayi shiru, ta isa ga famfon dake a gefen garden din inda suke tsaye ta soma alwala suna kallonta, suka saki baki ganin har wata suma take da a goshinta ga gashi daidai misali, ita dai ta samu ta kammala a gaggauce, ta yi musu sallama ta tafi da tunani hali irin na wasu mutanen da suke da karancin godiya ga Allah, wasu suna can ma basu samu koda rabin yanda su suka samu ba.
A haka ta shiga ta tarar har Amina ta idar da sallar tana addu'o'in da ta saba. Itama ta zura hijab ta tayar, bayan idarwarsu suka yi zaman hira anan take ji daga bakin Amina cewa su Haidar ma sunzo.
"Mai yiwuwa suma sauran ki gansu." Amina ta karasa.
Ummi ta bata labarin hirarsu Sa'a akanta, Amina ta dara.
"Mata kenan, muna da matsala wallahi. Mudai mu kama kanmu babu ruwanmu da harkarsu idan ba gaisuwa ba da hirar da bata shafi kowa ba.
Suna nan Sa'a ta lek'o.
"Ummi, Anti Aisha na kira."
"Toh."
Ta mike cikin sauri ta gyara zaman hular kanta.
Ta fito tana waige-waige don har ga Allah ta mance yanda tsarin gidan yake. Ta karasa wajen doguwar baranda wacce akwai bene daga wani loko, ta yi shiru, ta cigaba da tafiya, wata kofa ta gani makamanciyar wacce suka shigo, hakan yasa ta bude kofar, kawai sai ganinta ta yi a wajen (pool). Daga tsakiya ya ke, a gefensa rumfa ce aka sanya kujerun zama, wani murmushi ta yi don sosai wajen ya burgeta.
Ta rufe jin kamar motsi ana saukowa daga bene. Tana shirin barin wajen suka yi kici6us da Adnan. Kowannensu ya saki fuska.
"Lah, daman dake aka zo?" Ta yi dariya.
"Eh, kana murnar ganin Mami baka lura ba."
Ya dara shima. "Bari kawai, ai nayi kewarku wallahi. Ina za ki ne?"
"Kaga hanyar na rasa, Anti Aisha ce ke nemana."
Yana dariya ya soma tafiya.
"Ke kam ba dai saurin mantuwa ba, biyoni ki gani."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR