Sashe 82
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kasa kwakkwarar motsi Ummi ta yi, ya hade cikin farin yadi wanda ake ganin farar singiletinsa ya dora bak'ar hula hakanan takalminsa bak'i ne. Ya yi kyau kwarai duk ya chanjamata. Abu ke tambayar Gidado abinda ya faru. Daidai lokacin da suka karaso wajensu ya kasa dauke idanunsa daga Ummi.
"Bak'o ki ka yi, tare da Mai sunan Baffa(Usman kanin Malam Balarabe) ya zo, bayan an gaisa kuma ya ce bazai jira ku dawo ba na yi mishi rakiya." Duk wannan dogon bayanin da Gidado ke yi gareta ita gaba daya jikinta ya yi sanyi, Yaya Faruk? Ina ya baro aikinnasa? Yanzu babu kunya ya cewa su Daddy zai zo wajenta? Wayyo, wannan abu akwai kunya. Saida ta ji Abu ta gaisheshi da hausa ne ya amsamata da fulatanci har Abu na dariyar mamaki, itama ta dawo hankalinta, ta tuna ashe fa shima bafulatanin ne.
Ta durkusa ta gaisheshi da girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa, Gidado ya dubesu.
"To, za ku juya ne ko mu wuce tare?"
Faruk ya dubeshi har lokacin fuskarsa da walwala.
"No ku karasa, ta nan za ku biyo ko?"
"Eh." Abu ta amsa.
"Idan kun zo nan sai mu koma tare."
Suka amsa da to kafin su soma tafiya, shi kuwa baice uffan ba ya soma tafiya ya nufi wajen wani dutse ya sanya hankicif gami da zama. Garin babu rana sai ma hadari da ke haduwa. Ya dubeta, ta sunkuyar da kanta ta soma takowa don ta fahimci manufar kallon, gefe ta dan zauna.
"Sai ki ka ga Faruk ko?"
Ta murmusa.
"Ai na yi mamaki, naga kuma yau ranar aiki."
Yana binta da kallo ya amsa.
"Kar ki yi mamaki, kina da daraja da matsayi babba awajena wannan yasa ni daukar hutun sati kawai don na zo na ganki. Na horu da yawa fa Ummina, ji yanda na ajiye k'ashin wuya sadda ke ki ke mulmula k'iba har wani tumbi ki ka ajiye."
Ya karashe a shagwa6ance kamar yana gaban Hajiyarsa. Kunya da dariya ta kamata lokaci guda. Ta dan ja mayafinta da ya zamo har ana ganin kwantaccen gashin goshinta wanda ya kusan haduwa da gira. Tabbas tasan ta yi k'iba saidai bata hango tumbin da ya hanga ba. Ya dan daga gira.
"Dagaske nake."
"Um, ya akayi ka zo nan?"
"Garin masoyi yana nisa ne?"
Bai saurari amsarta ba ya cigaba.
"Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa, rashin ganin mahadinta kwana biyunnan ya jefata cikin tarin damuwar da ba za ki gane ba. Da naga ina neman mutuwa kawai na yanke shawarar biyo jirgi na taho Gombe. Ina isa kai tsaye na kira Babana, shi kansa ya yi mamakin jin wai ina Gombe, ya fadamin sunan unguwar ya ce idan na shiga tasi na hadashi da direban. Ya mishi kwatance, Alhamdulillah, don kuwa Ummina yan uwanmu sun min kyakkyawan tarba sannan sun ji daga bakin Baba cewa ni ke son aurenki. Jiya na iso Gombe, sai yau na taho nan. Kin gane dagaske Faruk bai iyawa babu Hasiya?"
Ta rufe idanunta tana murmushi, har cikin ranta wani wutar kaunarsa ke kara ruruwa. Bata ji tashinsa ba sai bude ido da ta yi ta ganshi durkushe gabanta ya kuramata idanu yana murmushi, yayinda ya tokare hannun damansa saman dutsen. Sunkuyar da kanta ta yi.
"Mu godewa Allah da Ya amsa mana addu'armu ya sadaki da farincikinki, na tayaki murna ainun Ummina. Abu daya ya rage mana."
Ta ji sarai abinda ya ce sai ta basar.
"Nagode Yaya Faruk."
"Dayan fa? Ba za ki yi tambaya akansa ba?"
Ta dan saci kallonsa yanda ya ke maganar cikin rad'a-rad'a. Ya kashemata ido daya, ta yi kasa da kanta da sauri.
"Ko bakyaso ki ganki a gidana matsayin matata?"
Da sauri ta karkata ta kauce daga saitinsa tana mai ambaton Innalillahi a fili don ji ta ke kamar ta dora hannu a kanta don kunya. Dariya sosai Faruk ya shiga yi adaidai lokacin da iska ta yi awon gaba da mayafinta, ta rike kannata tana mai da na sanin fitowa ba dankwali, tunda suke da Faruk bai ta6a ganin gashinta tsirara har haka ba, ya yi mata kallo daya yana mai kauda kansa da sauri alokaci guda ya na mai tsintar yanayinsa da chanjawa, ita kuwa da sauri ta janyo mayafin ta rufe gashinta sannan ta mike tsaye, muryarta ba rawa ta ce.
"Yaya Faruk mu tafi kada ruwa ya riskemu anan kaga har yanzu ba su tahowa."
Ya sanya hannuwansa cikin aljihun wando, yana mai shakar daddad'ar iskar da ke kadawa, kafin ya juyo ya dubeta sannan ya yi kasa da kansa.
"Muje." Ya fada cikin yanayi na mutuwar jiki. Ta fahimci kamar yana niyyar barin hankicif dinnasa anan, shi kuwa yana sane ya yi hakan, ta dan saci kallonsa, ganin ba ya kallonta yasa ta dauka da sauri ta cusa a riga, ya yi kamar bai gani ba sai ma juyar da kan da ya yi yana murmushi ya soma tafiya. Suna cikin tafiya suka ji yo muryar su Abu da Gidado, hakan yasa suka tsaya suka jera tare suna tafiya da dan sauri-sauri ganin yanda ake iskar sosai, don ma a dazun ba wani nisa Ummi da Abu su ka yi ba ya taddosu.
Suna dab da karasawa aka soma yayyafi, cikin taimakon Ubangiji ruwa bai tsuge ba sai bayan isarsu gidan. Suka yita godiya ga Allah.
Faruk bisa jagorancin Gidado ya koma dakin Dattijo Manu, wanda a yan kwana biyunnan ne ya dan ji saukin jikinsa don yana fama da hawan jini.
Bayan sunyi sallar Magriba, Faruk ya sanya (jacket) sakamakon sanyin da garin ya yi, sannan suka shiga hira da harshen fulatanci, Faruk ya daukeshi tamkar Modibbo, Dattijo Manu na watso mishi tambaya game da ko su fulanin ina ne yana amsawa dalla-dalla. Kafin shima ya labartamishi nasu, ya ji dadin hira sosai da Faruk din, shima Faruk din ya sake da shi ainun don bai ji nauyin sanarmishi yanda ya ke kaunar Ummi ba wanda hakan ba karamin dadi ya yi masa ba. Cikin tsokana ya ce.
"Saidai fa banason kara yin nisa da amaryata."
Dariya Faruk ya yi.
"Karka damu, akai-akai za ka dunga ganinta, idan ta kama ma ai sai mu daukeka mu maidaka Abuja."
"Kayya, barni inda nafi wayo, nan Buba ma ya yi da ni akan na koma can birni Gombe wajensa na k'i." Duk suna maganar da fulatanci suna dariya.
"Nima inaga mun kusa zuwa Adamawa, amma fa da Amaryata."
Cewar Faruk cikin wasa da dariya har ya bawa Dattijon dariya. Saida ruwa ya tsagaita sannan Inna Boddo ta umarci Ummi da kai musu abinci, ta yi tsuru da ido saidai ganin ba yanda ta iya ta ja Abu suka wuce tarr kowanne dauke da kwano bibbiyu don har kaza aka soyawa Faruk, gaba daya dattijan ke haduwa su ci abinci tare saidai ruwa yanzu ya hana hakan ita kuwa tunani ta ke yi Faruk dan gayu dan hutu da shi anya zai iya cin cimarsu? Haka dai suka karasa da sallama, bata kallesu ba, kai a kasa ta gaida Dattijo Manu, ya amsa yana fadin.
"Amaryata ki yi zamanki anan kinji? Sai kin iya fillanci."
Murmushi kawai ta yi, duk yanda Faruk ya so su hada ido ta k'i, saida suka kawo musu komai har ruwan wanke hannu da na sha na randa mai sanyi sannan suka fita.
Ummi kuwa kowa a gidan cewa ya ke ta yi sa'a ga shi mutumin kirki ga shi kuma bafulatani shima, murmushi kawai ta ke yi ba ta cewa komai.
Tana kwance a dakin Inna Boddo, Innar na cikin sange(mosquito net) an lullu6eta da bargo mai kauri sosai saboda sanyi. Bayan ta tabbatar Innar ta yi nisa a bacci ta fiddo hankicif din ta rufa a fuskarta tana mai shak'ar kamshin idanunta a lumshe, murmushi saman fuskarta. Wayarta ta soma k'ara da sauri ta zarota daga k'asan filo ta danna kada Inna ta farka, Faruk dinne kuwa. Ta dafe kirji kadan, a hankali ta sauka daga gadon ta fito waje ta zauna.
"Ummina."
"Um."
"Na yi mantuwa fa a wajen dazu." Ta zaro ido gami da hadiye miyau na fargaba.
"Mantuwar me?"
Ya danne dariyarsa yana duban Dattijo wanda munsharinsa ya hanashi runtsawa kwata-kwata.
"Hankicif dina, ko kin ganshi?"
Idanunta ya yi kwal-kwal, to ta ce me? Ta ganshi yana wurinta? Me zata yi da shi da bata mayarmishi ba?
"Kinyi shiru."
((Afuwan..ni kaina na qagara na kammala muku saidai haka Allah Ya nufa labarin zai fi yanda na zata a tsawo...not much..lol))
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
100