← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 116

Sashe 65

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ihsan ta yi tsai tana duban hoton saurayin da Maminta ta bata, babu laifi kyakkyawa ne kuma bak'i, yana da 'yar kiba. Ta numfasa, ba wai ta ji sonsa a ranta ba, kawai dai ya kai yanda zaa iya auren huce haushi da shi.
  "Dan wani babban abokin Abbanku ne dake Adamawa, mahaifinsa babban Injiniya ne, Alhaji Kabir Jimeta."
  Ihsan ta ajiye hoton a gefe.
"Yana da d'a Abubakar?"
Cikin dariyar mamaki Mami ta ce.
   "Ashe kin sanshi ma, ai shine wannan din."
  Ta dan ta6e baki.
"Yana da kirki, muna chatting da shi ai saidai ban sanshi a hoto ba, ya sha gwada yana sona saidai ni ce ban ba shi fuska ba."
     "Ai kuwa ya zama dole ki so shi, kin kuwa san matakin arzikinsa yanzu a Adamawa? To ana sanyashi cikin goman farko na yara matasa masu kudin garin sannan kalleshi da kyau ba shi da makusa a halitta."
  Ihsan ta danyi jim, kafin ta ce.
"Yana da mata fa Mami."
Tsaki Mamin ta ja, ta soma fusata da lamari na diyartata kuma.
"Shikenan sai ki zauna jiran aurenki da Faruk ki yi kishi da wacce bata kai ba, ni wallahi bansan irinki ba, ina ruwanki da matarsa? Matarsa gogaggiyar yar boko ce kuma bata ta6a haihuwa ba da shi, shi kuwa ba shi da burin da ya wuce na ganin ya haihu a duniya. Idan ki ka haihu da shi tabbas mun warke, kada ki bar wannan dama ta wuce mu. A zamanin nan samun matashin da ba shi da aure kuma mai rikon aure sai an tona, gwara ki auri wannan da kowa ya shaida kyawawan dabi'unsa."
   Haka Mamin ta yi ta kod'a Abubakar a wajen 'yarta, ita Ihsan har mamaki ta ke yanda uwar ta sanshi haka, sai kuma ta tuna sunan mahaifiyarsa da ta ambata, wato Hajiya Salma kusan tare suka tashi da Mamin a Kano, aure ya rabasu. Dole Ihsan ta amince da hakan, saidai abinda ta kasa sanar da Mamin shine, Abubakar ya sha janta da hirar da bata dace ba tana k'in ba shi fuska, hakan yasa ma dangantakarsu ta yi tsawo.  Ai kuwa kamar jira Mamin ta ke, Abba na dawowa ta tare shi da zancen, ya ji dadi matuka don kuwa acewarsa daman Alhaji Kabirun ya ta6a neman tayin hakan tun akan Aisha saidai Allah baiyi rabon dannasa bace, yanzu kuwa yasan zai ji dadi idan ya kasance da Ihsan, daman burinsu a k'ulla zumunci. 
   Kwana biyu da yin hakan Alhaji Muhammad ya yi magana da abokinnasa.
"Kamar kuwa kasan ina kan ga6ar nemarwa dan nawa aure, ina burin ganin jikokina, fatana Allah Yasa idan anyi hakan mafarkina ya tabbata."
  Nan suka sasanta magana inda Alhaji Kabiru ya tabbatar mishi cewar cikin(weekend) zai zo tare da dan nasa don su ga juna. Da wannan suka ajiye wayar ran kowa ya yi dadi. 
Bayan Abba ya ajiye ne ya dubi Mami.
"Kinga cikin ikon Allah sai a had'a auren harda na Iklima, itama ta tsaida yaron nan dan gidan tsohon kansila, Mu'azzam. Itama Hussainar ba barinta zan yi ba, lokaci guda zan aurar da su idan Allah Ya yarda, da zarar sun kammala wannan ajin, ba don ma yaron ya ce sai ya gama gini ba, da sai a soma na Iklimar."
  Mami ta gyada kai, ranta baiso ba, ta so ya zamana ba za'a hada auren diyarta ta da na kowa ba, ko don a fi ganin kalar bajintar da zata yi. Amman ta riga ta saba da binshi yanda yaso.
"Hakan ma ya yi, Allah Yasa ayi muna raye."
Ya amsa da amin cikin jin dadin sha'ani na uwargidan tasa wanda ya sha bamban da Hajiya Binta, da ita ce sai sun kai ruwa rana, gwara-gwara Hajiya Luba, itama akan yi abin arziki da ita idan kishinta bai motsa ba.
                   ***   ***   ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
83
                       ABUJA

   "Allah Mai Iko." Shine abinda Gen. Ahmad ya fad'a sa'ilin da ya ajiye waya da Alhaji Atiku inda suka tattauna a mutunce. 
  Hajiya Babba da ke kokarin zuba mishi abinci babi abinda ta ce, tamkar duk bata ji abinda suke tattaunawa akai ba. Shima Daddy ita ya yi shiru yana duba.
  "Meyasa ki ka 6oyemin wannan batu? Na yi tsammanin don shi ki ka je Kanon?"
Hajiya ta ajiye (serving spoon) tana mai duban mijinnata cike da kulawa. 
   "Me fa?"
"Ai shi Alhaji Muhammad ya riga da ya yiwa diyartasa miji, d'an abokinsa, Alhaji Kabir Jimeta."
  Hajiya Babba ta yi wani murmushi.
'Madina kenan.'
Ta fada a zuci, a fili kuwa ta nuna rashin damuwarta.
"Allah Yasa alheri, ni sai yanzu da ka fada na sani daman iyakar tattaunawarmu da ni da Madinar ce, watakil sai bayan ta sanarmishi itama ta ji hakan don da ace ta san da haka ba zata 6oyemin ba."
   Ta fad'i hakan ne don batason ta nunawa mijinta basu dadi da yar uwarta. Ganin fuskarsa ta cika da damuwa ta ce.
"Ba wani abu fa, kasan babu mai aurar matar wani, watakil ba rabo tsakaninsu, idan akwai sai kaga lamarin ya juye."
   Ya jinjina kai cike da gamsuwa da maganganunta.
"Hakane kuma, to Allah Ya za6amusu abinda yafi alheri. Ita wannan ya ake ciki?"
   "Ga dukkan alamu lokacin zuwan matar da ta kawota ya k'arato inaga tunda ga watan saura kwana biyu ya mutu, ( family meeting) din namu shima ina tunanin jibi ne zaayi."
Cewar Hajiya kafin kuma ta cigaba da zubamishi abinci. 

    Kwance a saman lallausan katifa a saman gado, Ummi ce tana faman duba wasu litattafan addini da Hajiya ta had'ata da su, ta ji dadin hakan kwarai, Hajiya ta k'ara da batun sanyata Islamiyyar da Ikram ke zuwa don zuwa lokacin hatta form an kar6omata, hakanan an bada a dinka mata (Uniform). Ga shi kuma gogan ya nuna yana mata sha'awar karatun boko, acewarsa neman ilimi ko gemunka na ja a k'as ba ka yi latti ba. Wannan shine kyakkyawan albishir gareta. 
    Wayarta ta yi k'ara alokacin da ta tsunduma cikin karatu, ta sanya hannu ta janyota. Tsai ta yi da ido tana duban lambar wacce ta ta ganta banbarakwai, har ta katse bata iya ta d'aga ba, sai a karo na biyu ne ta d'aga da sallama. 
  Daga can Adnan ya amsa yana dariya.
"Kaga sabon shiga kin tsoraci kada a gudu da ke ne?"
  Ta so gane muryar saidai bata da tabbacin shi dinne ko aa, ta dan saki fuska.
"Ba haka bane."
"To ina My Best?"
Kalmarnan babu a bakin wanda ta santa sai Adnan, ta washe hakora gami da mikewa zaune.
"Lah, Yaya Adnan?"
Sai kuma ta yi dariya shima darawar ya yi. 
"Ni ne nan kanin Angonki."
"Kai Yaya Adnan."
"Ai gaskiya ne, yanzu ko kin yi tsada karki so ki ji kashedun da aka yimin kafin a bani lambarki."
Ta yi murmushi.
"Ina wuni." Ta fada cikin basar da wancan maganar. 
  "Ba zan amsa ba tunda kin yi waya amma ba ki nemi a ba ki lambata ba."
  "Ka yi hakuri to, ya su Mami?"
  "Suna k'asarku, ni ina nan Dubai."
Ta dan bude ido kadan.
"Au na manta, Yaya Faruk ya gayamin kwanaki wai za ka karatu ko?"
   "Inye! Abu ya yi nisa haka ashe?"
Ya karashe yana dariya, ita kuwa murmushi kawai ta yi, ita sai lokacin ta tuna da ashe fa da yaya Ihsan ta ke magana, sam halinsu ya bambanta.
  Adnan ya sake da ita suka shiga kwasar hira sosai yana bata labarin Dubai tamkar wata abokiyarsa,  duk da tana jin wani dan kara(din-din) ta cikin wayar bata fahimci ko na menene ba. Bayan sun kammala wayar ne ta ajiye, nan ta fahimci Faruk ke kira. Kafin ta kai ga yunkurin kiransa sai ga shi ya kara kira.
  Bai ko amsa sallamarta ba.
"Da wa ki ke waya?"
"Yaya Adnan ne."
Ya sauke ajiyar zuciyar da har ta ji.
"Ok, amman kun jima kuna waya, me ya ke fadamiki haka?"
   Ta yi murmushi kadan.
"Hira ce ta makarantarsu ya ke min."
"Ok, kina da labarin tafiyarmu Kano gobe?"
Gabanta ya fadi.
"Har da ni?"
"Au, Hajiya bata sanarmiki kenan? Watakil sai zuwa anjima, family meeting zaayi, kusan wannan karon ni da ke ne masu muhimmanci a gurin, akwai wani ma albishir din amman ba yanzu zan yi miki shi ba."
  Ita kam duk ta tsorata, ta lura shi gogan ma bai gane hakan ba.
  Suka dan ta6a hira kafin su yi sallama.
   Ai kuwa a daren Hajiya ke sanarmata cewa ta shirya kaya ko kala uku ne. 
      Washegari gaba daya da misalin biyu na rana suka kama hanya har yayyun Faruk da matansu, a motar can lungu ta zauna don gujewa wani abin da zai je ya zo, tana ji Intisar, Baraka da Ikram suka juye harshe zuwa fulatanci suna hirarsu, duk ta bi ta tsargu duk da basu ko kallon inda ta ke. 
                    ***   ***   ***
                         KANO
     Acan kuwa gidan Mami, da misalin karfe uku Yaha ta diro. Mami ta dubeta bayan ta zauna.
"Aa Yaha sai yau ki ke tafe?"
"Wallahi kuwa Hajiya, Minna na je shiyasa na kwan biyu ba ki ganni ba, su ma can gidan su Ummin suna min waya wai sun ji shiru."
   Murmushi Mami ta yi na takaici. 
"Ai kuwa Ummi bata gidannan yanzu."
Yaha ta karkato gami da yin sakato da baki. Mami ta koramata bayani.
  "Jar Uba!" Shine kawai abinda Yaha ta ambata....!

  Don gyara ko shawara a tuntu6en...
[email protected] or through facebook acc. Rufaida Omar
  "Jar Uba!" Shine kawai abinda Yaha ta ambata....!
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 65 · 0% Book details