← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 116

Sashe 12

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba musu ta ja Ihsan suka tafi. Hajiya Binta suka soma gani a falo tare da Usman, Jabir da Hanif, gaba daya kallo ya daukemusu hankali. Sallamarsu ce ta sanyasu maido hankali garesu. Ta soma shan kamshi yayinda ta amsa ciki-ciki.
Suka karasa suka gaisheta. Saida ta k'arewa suturar dake jikin Baraka kallo sannan ta numfasa, ta riga tasani iyalan Hajiya Fatima ba su ta6a zama a baya wajen suturu da sauran kayan more rayuwar duniya.
"Baraka ko?"
Baraka fuska a sake ta amsa.
"Eh ni ce Umma."
"Sannu, yanzu kuka zo?"
"Za mu tafi ne dai, ina Iklima?"
Hajiya Binta ta nunamusu hanya.
"Ku shiga tana d'akinta."
Suka shige ta bi bayansu da kallo cike da jin wani tuk'uk'i a ranta, dole Madina ta dunga yi musu wani gani-gani kasancewar daga ita har Lubna, ba wasu 'ya'yan masu kudin azo a gani bane, a komai dangin Hajiya Madina sun k'ere musu, yana daga dalilin da yasa suke matukar kishinta. A gefe kuma tana tak'ama da cewar ita din fa jinin Alhajinsu ce, shi kansa Alhajin koda hira akeyi da ya shafi danginsu, sau da yawa yakan yabawa bajintar mahaifin Madina, da irin yanda ya iya rik'e iyali da sauransu. Wannan yasa ko kad'an acikinsu babu mai kaunar suyi wata doguwar hirar da ta shafi dangin Alhaji Modibbo. Babban burinta yanzu, bai wuce yaranta su kasance wasu shahararru ba a fannin kudi, ta ci buri akan Iklima wannan yasa ta haneta abota da dukkan wani jinin talaka, dukkan abokan Iklima 'ya'yan wasu ne. Koyaushe tana hanyar biki da party. Babu laifi takan samu samarin masu ji da kudi saidai da yawansu ba da aure suke sonta ba, saidai wata manufarsu ta daban. Idanunta sunyi masifar budewa wanda hakan nai ta6a damun Hajiya Binta ba, acewarta, idan bata kasance wayayyiyar ba, a ina har zata samarwa kanta miji dan zamani.
Acan kuwa su Baraka suna shiga Iklima ta rungume Baraka tana ihun murna don sosai kawarta ce, kusan halinsu yazo d'aya na son gayu da samari.
"Shegiyar gari, daman kinzo shine ko ki nemeni?"
Baraka tana dariya tace "Afuwan tawan, kinsan tun dazu na so shigowa Allah baiyiba, ina su Yaks?"
Fad'in haka yasa ita da Ikliman suka tuntsire da dariya ita dai Ihsan ta zama 'yar kallo, ko ita da suke tare da Ikliman basu hira mai tsayi har haka, lallai ba karamin sabo Baraka da Iklima sukayi ba.
"Yana inda yake, kwana biyu munyi fad'a ma, zan baki labari kedai. Ina mijina?"
Cewar Iklima tana mai kashe mata ido d'aya, Baraka ta ja guntun tsaki tana dariya. Ta fahimci Faruk take nufi, tun daga sau daya da ta ga ta dora hotonsa a dp lokacin shi kuwa yana gani ya shigo har dakinsu ya hauta da fad'a har yakai ga mangarinta, yace tayi gaggawar goge dukkan hotunansa a wayarta. Daga ranar bata kara dora hotonsa. Daga ranar Iklima ta makale akan lallai ita fa sai ta hadata da shi, hakuri kawai ta bata ta gwadamata Faruk sam ba irin nasu bane don ba shi da wannan rawar kan akan mata.
"Kedai ki kama kanki baruwana na gayamaki."
Cewar Baraka. Iklima tayi dariya.
"Ina ruwanki? Bazan kama ba sai randa kika bani lambarsa."
Ihsan duk bata fahimci komai ba saida ta ji Baraka na fadin.
"Kizo muje da kanki ki tambayeshi, ga shi can a waje." Ai sai Iklima ta zaro ido.
"Dagaske?"
"Wallahi." Cewar Baraka cikin dariya, tuni ta ja dankwalinta ta rufe kanta, daman riga 'yar kanti ce a jikinta sai siket ruwan madara na leshi da dankwalinsa.
"Muje wallahi na gaisheshi na tambaya."
Suka kamo hanya Baraka cikin dariya ta na fad'in.
"Kamar gaske, bakisan wanene Yaya Faruk ba wallahi."
Gaban Ihsan ya fad'i, me Baraka ke nufi? Wato Iklima batun Faruk take? Aikuwa ba zata sa6u ba, saidai su yi BIYU BABU. Muddin ita bata samu soyayyarsa ba, to babu wata ta jininta da zata samu, ta gwammace ya je ya auri bare akan tana ji tana gani ya auri wata jininsu. A ganinta, itama fa tana da aji, ba zai yiwu ta zauna wani namiji na sha mata kamshi ba, ta tsani dukkan wani namiji mai ji da kansa, baruwanta da kyansa, idan kyau ne, akwai wadanda suka fishi da suka nuna suna sonta tana sha musu kamshi.
Anan kofar shiga sashen Alhaji Modibbo suka ga takalman Mami da Hajiya Babba, wannan ya tabbatar musu suna ciki. Da rawar jiki Iklima take tafiya, Allah-Allah takeyi ta had'u da Faruk ko don shima yasan da zamanta. Ta tabbatar ba kowane namiji ne zai iya dauke idanu daga kanta ba. Haka suka karasa bakin motar, alokacin Haidar da Adnan ne kawai tsaye sai Ikram wacce ta jingina jikin mota tana danne-dannen waya. Iklima suka gaisa da Haidar, Adnan sai dauke kai yakeyi. Itama bata bi ta kansa ba ta dan lek'a motar, kasancewar akwai wadatar haske a farfajiyar gidan hakan yasa ta hangi Faruk dake zaune a mazaunin direba ya d'ora tafin kafarsa akan kujera, kansa jingine jikin kujerar yayinda kunnensa ya sanya (Earpiece) yana shan sauti. Idanunsa a lumshe. Wani wawan ajiyar zuciyar Iklima ta saki, ta ko'ina Faruk ya had'u. Ta gaida su Yaya Usman suka amsa mata fuska a sake kafin tayi ta wajen Faruk tana gaisheshi. Ko kusa baisan ma tana yi ba saida Usman ya cire mishi kunne d'aya na (Earpiece) sannan ya juyo da rinannun idanunsa, da alamu ma bacci ya soma.
"Au bacci kakeyi ma? Ana gaisheka."
"Ina wuni." Ta k'ara fad'a. Ya juyo ya zubamata idanu, ai ji tayi kamar ta saki fitsari tsabar yanda kallon ya kad'ata, duk inda take zaton Faruk a kyau da komai, ya wuce nan. Kansa kawai ya gyad'a mata sannan ya dauke kai. Ji tayi ta kasa koda kwakkwarar magana, to ta ina ma zata iya furta mishi wani abun har ya kai ga tambayar lambarsa? Ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ga su Baraka wadanda ke yi mata dariya har Ihsan wacce ba karamin dadi abin ya yi mata ba.
"Wace ne?"
Faruk ya tambaya ba tare da ya bud'e idanunsa ba.
"Iklima, step-sister dinmu." Cewar Adnan. Ya yamutse fuska.
"Har yanzu Hajiya bata fito ba? Wallahi na soma bacci."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

16
Kafin waninsu yayi magana, sai ga Mami da Hajiya tafe suna hira, Yaya Ridwan ne yayi magana.
"Ai idan iyayenmu mata suka had'u wallahi har mamaki suke ban, ko kusa basu kaunar rabuwa da juna."
Faruk da Usman suka d'an dara, kamar ba zasu karaso ba haka suke tafe suna hira. Ganin dai da gaske basu da niyyar tahowa ya sanya Faruk dannan hon, wannan ya maido hankalinsu wajensu. Ya koma can gefen mazaunin direba yana fad'in.
"I can't drive wallahi, bacci ya soma kama idona."
Haidar ya bude mazaunin direba ya shiga yana fad'in.
"Ai nayi mamaki ma da ka iya kaiwa war haka, kodayake na dole ne. Mutumin da wani sa'in takwas ma yayi bacci."
Murmushi kawai Faruk yayi ya kara lumshe idanunsa sannan ya budesu. Hajiya Babba ta karaso ta shiga, ganin haka yasa yanmatan sallama da juna, bayan shigarsu Iklima ta zubawa Faruk ido kamar ta had'iyeshi, tsaf ya lura da kallon da take jifansa da shi, wannan yasa a sannu ya zuge gilas wanda ya kasance mai duhu, shi ya yi mata katanga daga dubansa. Ta sauke ajiyar zuciya, ta juya ta kama hanyar ciki bayan ta gaishe da Hajiya Babba, sun kara sallama da Baraka.

"Maganar banza ce kikeyi, wacce ba zata ta6a kasantuwa ba matukar Binta na raye wallahi. Da kinsan yanda nake kishin Madina da danginta, da baki soma tunanin son Faruk ba Iklima."
Cewar Hajiya Binta tana faman hura hanci fuska a murtuke kamar bata ta6a bud'a hakoranta ba don dariya. Iklima ta tur6une fuska tana kunkuni ta mik'e ta barta tana faman bud'e wuta.
"Eh lallai, gwara tun wuri na tashi tsaye kafin kema ki rikita lamurana, shawarar Luba zan bi."
Ta karashe tana daukar wayarta, H
Luba ta dannawa kira sannan ta mike ta fad'a d'aki. Suka gama kulla-kullarsu akan yanda Alhaji zai shigo hannunta sai yanda tayi da shi, da kuma irin nau'ikan muguntar da za'a yiwa Madina a lalata rayuwar 'ya'yanta, itama a dusasar da tauraronta dake haskawa a idanun Maigidan da surukarsu. Haka suka ajiye wayar cike da jin wani nishad'i ko babu komai itama tana dab da samun matsayi babba.

☆☆☆

Haka rayuwa tayita tafiyarwa Ummi, yau dadi gobe babu dadi. Yawanci matsalarta bai wuce Ihsan ba don Mami matukar zata yi abinda ta sanyata to fa babu ruwanta da harkarta. A wannan halin ne wata ranar Asabar ta tashi da ciwon mara marar misali, tun tana dauriya har ta kasa, ko tashi ta kasa yi balle ta kai ga aikace-aikacenta. A wannan hali Ramma tayi sallama ta shigo bisa umarnin Mami da ta dubo ko lafiya bata fito ba har ga Ramma ta rigata zuwa.
Ganinta ba lafiya yasa ta fita ta sanarwa Mami. Kafin su dawo ta soma jin ta da lema, saida Ramma ta d'agata ne suka fahimci abinda ke faruwa. Ramma ta taimaka mata bayan ta kar6o (Always) wajen Mami, ta gwada mata yanda zatayi, saida ta kimtsa sannan suka rankaya kemis da Ramma.
Tun daga wannan ranar Ummi ta fahimci girma ya hau ta, Ramma ta k'ara jaddada mata hakkokin da suke akanta yanzun wadanda ta riga ta sani don a makaranta duk ana koyardasu.
Mami bata yarda da kazantar kunzugu ba, hakan yasa ta bata (pads) cikin na Ihsan wacce ta rigata somawa tuni. Saida tayi kwanaki hud'u sannan tayi wankan tsarki. Daga wannan lokacin ta k'ara kame kanta ta zama mai kula sosai da takatsantsan musamman ma ga sallolinta.
☆☆☆

A KWANA A TASHI...!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
Chapter 12 · 0% Book details