← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 116

Sashe 42

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Acan kuwa Ummi ta iske Faruk durkushe gaban ruwa yana sanya tafin hannunsa na dama yana wasa da shi, fuskarsa a sake. Jin shigowarta yasa shi kallonta, ta kauda idanunta ta karasa bayan ta rufe k'ofar. 
   Mikewa ya yi ya koma ya zauna, itama ganin haka ne yasa ta zama a dayan kujerar kamar yanda sukayi wancan karon saidai a wannan karon ya sanya kujerun suna kallon juna, hakan yasa shi bawa k'ofa baya ita kuwa tana fuskanta. 
   "Na yi zaton bazaki zo ba ai."
Babu abinda ta ce sai wasa da gefen hijabinta da ta ke. 
   "Ummina."
  Ba ta amsa ba sai kirjinta da ke lugude. 
  "Wai meyasa ne kike kasa sakin jiki da ni? Idan da magana a bakinki ko fad'a."
   Ta ga dama ta samu, hakan yasa ta daurewa ta dubeshi.
"Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri ka kyaleni." Ta sauke idanunta daga kansa kafin ta cigaba da magana a raunane.
"Wannan abu ne da ko a mafarki ban ta6a ganin ya faru ba, 'yar aiki da auren d'an masu gida, kayi hakuri domin Allah, komai dake a ranka game da ni ka ajiyeshi gefe. Ni bazan iya abinda ka ke so ba, banason saka kaina cikin kowace matsala. Ka gafarceni amman idan akwai inda na kuskuro a maganata."

  Tun soma maganarta ya zubamata ido hannayensa biyu dunk'ule wuri guda. Ya lura iyakar gaskiyarta ta ke fad'a ba kuma don bata sonshi ba. Ya girgiza kai.
  "Meyasa ni ban ta6a hangen matsalar da kike yawan ikrari bane Ummi? Kina da tsoro, nasan kuma abinda ke tsorata ki wanda sam bai dace ba. Na farko dai nasan iyayena ba zasu hanani aurenki ba matukar na nuna musu ke ce za6ina, su din sun kasance maso abinda nake so, haka kuma yan uwana na tabbatar ba zasu hanani rayuwa da ke ba Ummi, koda ace kuma basu yi na'am da ke ba, to fa hakan ba zaisa na k'i aurenki ba muddin iyayena sun yarjemin.
Batu na gaba, ni ban daukeki daban da ni ba, Allah ne Ya haliccemu duka, ina yi miki kallo daidai da matsayina, ki ture dukkan wadannan kananun matsalolin Ummi, ki sauk'ak'awa zuk'atanmu, nasan kina jin abinda nake ji duk da cewar ba ki kama koda rabin k'afata ba."
  Shiru ya dan biyu baya, ya rankwafo kadan ya soma magana cikin rad'a.
  "Kin yarda kin amince na sanarwa Hajiya..."
  Bai kai ga karasawa ba ta hau girgiza kai tana dubansa da idanunta wadanda suka ciko da kwalla.
"A'a, a'a, don Allah kada ka fadawa kowa idan ba haka ba zan gudu."
  Ya dan hade gira jin kalmarta na karshe. 
   "Saboda kada ki aureni ne za ki gudu?"
  Ganin yanda muryarsa ta chanja da kuma yanayinsa yasa ta yin shiru gami da duk'ar da kai. Ya lumshe ido.
  "Shikenan, tashi ki tafi."
  Ta kasa motsawa, sai ta ji bata kyauta mishi ba, shi kuwa har lokacin bai bude idanunsa ba, dagaske bai ji dadin furucinta ba, kenan akan ta aureshi, ta za6i guduwa? 
    "Ka yi hakuri don Allah."
  Ya tsinci muryarta, da sauri ya bude ido don kuwa muryar ta nuna alamun kuka takeyi.  Kukan kuwa takeyi, ya girgiza mata kai.
"No Ummi please, banson hawayenki fa. Ni na hakura."
  Faruk ya cigaba da kasheta da dad'ad'an kalamai wadanda nan take suka kashemata jiki suka sukurkuta ta. Allah Ya mishi baiwar iya lafuzza masu dadi da saurin sace zuciya wanda shi kansa bai sani ba sai a yanzun da ya fad'a cikin soyayyar Umminsa. A wannan zaman da sukayi saida Faruk ya ci galaba don kuwa Ummi ta dan saki jikinta sun yi hira mai dadi har da dariya. Kowannensu yana jin zuciyarsa sakayau, gaba daya ji sukeyi tamkar a duniyar babu sauran bil adama sai su biyu tallin tal! A karshe ya duba wayarsa da ta soma k'ara, yayansa Likita ne(Ridwan). Ya dauka. Bayan sallama ya tambayeshi inda ya shiga, ga shi kuma a falon Hajiyarsu bai ganshi ba.
  Ya dubi fuskar Ummi wacce ke dan satar kallonsa, murmushi ylm    a yi ganin ta kauda kanta.
"Hira nake yi da surukarku amma ina nan zuwa."
   Daga haka ya katse kiran ya bar Ummi da sakin baki.
"To sarkin tsoro, rufe bakin."
Yana fadin haka ya mik'e tsaye.
"Bari na wuce Dakta ya zo. Sai mun hadu gobe kuma in sha Allahu ko?"
  Ta girgiza kai alamar aa. Ya ja dan guntun tsaki. "Kinga dadin waya kenan, da sai mu sha hira, amma dai ba wani abu."
  Daga haka ya yi mata sallama ya wuce, itama barin wajen ta yi da saurinta. Tana shiga dakin ta fidda hijabinta ta zauna, a yau ji take dukkan shawararwarin Antinta babu daya da ta iya dauka, ji take kamar ana k'ara rura mata wutar kaunar Faruk. Ta matso da ledar ta bude, ta yi mamakin ganin kayan kwalam har da su meatpie nad'e a jikin tissue guda uku, ga wani kullin leda karami wanda tana budewa ta ci karo da alawoyi kala-kala. Harda su cake da robar ice-cream manya biyu. 
   "Assalamu alaikum." Da bude kofar da sallamar nata duk lokaci guda ne
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  60
"Ya Salam, haba Ihsan, meyasa haka?"
  Ihsan ta mike zaune idanunta jage-jage da ruwan hawaye. Ta ja majina.
"Kinga lokaci ya k'uremin ko Ikram? Da ace na bi shawararki da banga wannan rana ba."
  Ikram tausayinta ya mamayeta, ta dafa kafadarta gami da girgiza mata kai.
"Aa, lokaci har yanzu da sauransa Ihsan. Na fadamiki ki cire kunya ki sanarwa Faruk abindq kike ji game da shi koda ta hanyar  kafar sadarwa (whatsapp)ne. Kada ki karaya da wuri."
   Haka ta yita lallashinta sannan ta fita wajen yan uwanta. Tana fita Ihsan ta dauki waya ta kira Maminta. Ko sallama bata iya yi ba ta fashe mata da kuka gami da labartamata abinda ake ciki. Mami ta shiga damuwa ainun.
  "Ihsan kina kyautatamasa kuwa kamar yanda nace?"
   "Babu abinda bana yi Mami, har gyaran dakinsa hana Ikram nayi na ke yi, amma wannan duk ba ya gani, ni yanzu na yanke shawarar sanarmishi irin illar da sonshi ya yiwa zuciyata."
  Mami ta karya murya.
"Kina ganin hakan zai fi?"
"Eh Mami."
  Mami ta jinjina kai, kwarai kuma tasan Faruk yana da mutunci, bazai so damuwar 'yar uwarsa ba. 
   "Shikenan, ayi hakan. Amma ki san abinda za kice dai."
   Haka ta yita lalla6a diyarta, bata son abinda zai ta6a farincikin 'yar tata ko kadan. A karshe ta sanarmata cewa an soma shirye-shiryen tafiyar Adnan Dubai inda ya za6a. Maganar ta yi mata dadi, hakan ya rage zafin da zuciyarta ke yi ta dan samu nutsuwa. Falon da bata koma kenan ba!
                  ***   ***   ***
                      RINGIM
      TSAFI GASKIYAR MAI SHI...

Kwarai wannan zance haka yake, don a kwana uku kacal! Dija da uwarta sun yi dukkanin k'ulla-k'ullarsu sun dauke hankalin Deen tsaf daga kan matarsa, kacokam zuciyarsa ta koma ga Dija. A yau lahadi ya yi shirin zuwa Ringim, don tun cikin ranakun aiki ya ke son kawomata ziyara tana hanashi. Yau kam ko sanarmata baiyi ba sai ganinsa sukayi. A kofar gidan ya faka motarsa, ya kirata a waya ya sanarmata yana kofa. Ta yi mamaki har da tsalle da ihunta na murna, Baba Habiba itama ranta sakayau. Ta taimakamata ta shirya sannan ta mik'amata turare da kwallin da suka kar6o.
  "Saka 'yar albarka."
  Tana dariya ta soma da kwallin sannan ta feshe jikinta da turaren mai kamshin 'yan bori, wanda aka tabbatarmusu cewar Deen zai ji ba kamshin da ya fi so anan duniya sai shi. 
  Daga haka ta fita ta sameshi, ai kuwa yana ganinta ya budemata kofa ta shiga. Nan take ya ji wutar kaunarta na k'ara ruruwa cikin ransa, sun sha hira inda ya matso dab da ita yana jin kamar ya sanyata jikinsa saidai ganin idanin mutane dake kansu yasa ta tsawatarmishi. Ya sanarmata cewa da zarar ya koma zai turo magabatansa, wannan yafi komai yi mata dadi don ta lura ya shiga hannu ta yanda shi kansa kwata-kwata ya bar shakkar dangin Munira su ji labari. 
    Ya sha hira sannan ya tafi, a daren ya k'ara dawowa, har suka gaisa da Malam Yahuza wanda ya yita mamakin ganinsa kuma da sunan ya zo wurin diyarsa. Koda ya shiga ciki ya tambayi Habiba, ta sanarmishi ai da aure ya ke sonta. Hankalinsa ya tashi da wannan amsa da ya samu, ya so nuna rashin goyon bayansa saidai ba shi da wannan isar a gidansa, sai ma ya tsinci bakinsa da furta kalaman nuna jin dadin al'amarin ba don har cikin zuciyarsa hakan bane.
   Ita kuwa Dija da Deen murzar juna sukayi son ransu, dakyar suka rabu. 
  Washegari Baba Habiba ta nufi wajen aminiyarta ta sanarmata komai, shewa Saude ta yi don abin ba k'aramin dadi ya yi mata ba.
   "Kice lokaci ya yi? Ai karku damu da abinda mutane zasu ce matar mutum fa kabarinsa, atoh."
  Dariya Habiba ta yi tana dan waige-waige.
  "Wai ina Mariya ne ban ganta ba tun zuwana?"
  Saude ta murmusa.
"Mariya kuma da farin jini, tana nan zaune Dauda dan gidan Zinaru ya aiko kiranta."
  Habiba ta dan yi jim.
"Anya Saude? Dauda fa kamar na ta6a ji ya yiwa wata budurwa ciki?" 
  Saude ta girgiza kai.
"Bar mutane da shegen karya Habiba, yaron nan har nan ya ke zuwa mu gaisa, kar kiso kiga irin kyautatawar da ya ke yiwa Mariya. Kuma banda abinki, yarinya da bata fi shekara tara ba?"
  Habiba ta jinjina kai.
"Shikenan, amma gaskiya ki saka idanu."
Saude ta gamsu da zancenta.
Chapter 42 · 0% Book details