← Book details Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 116

Sashe 66

Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

84
    Yaha ta yi furucin cike da tsananin mamaki, ba don Mami da kanta ke sanarmata ba da kai tsaye zata kira hakan da shaci fad'i.
Mami ta cigaba da magana.
"Ba abin mamaki bane, shi DAN ADAM idan ya samu guri fin haka zai iya aikatawa, banda haka ki duba irin yanda na dauki yarinyarnan, tunda nake yin yan aiki ban ta6a yin wacce na kyautatawa ba kamar ita, har wai yar aiki ta samu matsayin da zan zauna na dan yi hira da ita. Anan menene bai faru ba.."
Sai kuma ta yi shiru tana mai jin zafi a ranta.
  Yaha ta yi shiru cikin nazari, to ita fa Saude kudi ta ke nema, ita dai acewarta ko karuwanci yarinyar zata fad'a to ta fad'a matukar zata samu abin duniya sanadin haka, ga kuma yanzu a karshe da suka yi waya ta sanarmata kada ta kuskura yarinyar ta k'ara koda kallon hanyar garinsu ne ballantana wai ta kawota ganin gida. Yanzu ya za ta yi? 
  "Ki ka yi shiru? Idan za ki iya komawa gobe ki dawo to, idan kuwa za ki yi zaman jiran zuwansu daga Abuja yau din to babu laifi."(Ta sani ne ta hanyar Ihsan wacce su ka yi maganar da Ikram.)
    Sai lokacin Yaha ta dawo cikin hayyacinta, lallai kam tana bukatar nazarin.
"Bakomai ranki ya dad'e, zan iya tafiya na dawo goben."
Mami bata ko kara kallonta ba, daga haka itama ta mike ta bar gidan ba tare da ta samu ko na mota daga Hajiyar ba kamar yanda ta saba yi mata duk zuwanta.
   Bata zarce ko'ina ba sai gidan 'yar yayarta Abida wanda anan ne ta saba sauka duk sadda ta shigo garin Kano. Abida ta yi mata kyakkyawar tarba yanda ta saba. Yaha ta sauke mayafinta.
"Su Abu sun wuce makaranta ne?"
  "Eh sun dan jima."
Sai bayan ta ci abinci ta yi sakato tana tunani, Abida da ke gefe tana kokaarin zuba kananzir cikin risho tana mata hira amman shiru hakan yasa ta dubanta.
"To Inna meke faruwa ne haka?"
Yaha ta hau lashe kwana kafin ta tureshi gefe ta dubeta. 
"Bani shawara Abida, kaina ya cushe na rasa ma menene abin yi."
  Abida ta maida risho ta gyara sannan ta karkato tana dubanta.
"Ina jinki Inna."
Ta karanto mata tun kai Ummi aikatau da kuma ire-iren abinda Saude ke sanarmata akan yanda ta ke son ganin Ummi har ma da yanda suka yi da Mami. Ta karashe da fadin.
"Yanzu wallahi gaba daya jikina jinsa nake a sanyaye, ni tunda nake kai yan aiki ban ta6a haduwa da mai hakuri irin Ummin nan ba wallahi, zan iya ce miki tun tashinta a hannun Saude bata huta ba, ga kuma tsangwama da tsanar da ubanta ke nunamata tamkar ba jininsa ba."
  Abida ita kam mamakin Innarta ne ya cikata, ashe daman zata iya mugun abu har irin haka? A haka idan ka ganta tamkar ba zata aikata ba. 
  "Allah Mai Iko!" Ta fada a fili kafin ta cigaba da magana.
"Inna a farko ina mai baki shawara kan ki ji tsoran Allah, ki kuma sani cewar dukkan wani abu da muke aikatawa za'a tashemu gobe kiyama a kuma tambayemu. Wannan sam ba daidai bane a hada baki dake wajen cutar da rayuwar baiwar Allah wacce bata ji ba, kuma bata gani ba, ki sanya Rahma (diyar Yahan) a matsayinta ki auna ki gani, za ki ji dadi ace yau babu ranki Kulu(kishiyarta tun mijinsu na raye) ta aikata hakan agareta? Kada hakkin Ummi ya kamaki anan gaba Inna, don Allah ki yi tunani wannan ba daidai bane ko kadan."
  Daga haka Abida ta juya ta cigaba da aikinta zuciyarta cike da dumbin tausayin Ummi duk kuwa da cewa labarinta kadai ta ji. Yaha wacce ta yo shiru tana nazarin maganganun Abida ne, jikinta ya yi sanyi, babu abinda ke yawo a kwakwalwarta face irin zagi da hantara da ta dunga yiwa Ummi a hanya da kuma zuwansu Kano, harma da zaginta da suka yi zaman yi da su Saude duk akan abim duniya wanda ba wani mai yawan azo a gani bane. 
  Ta sauke ajiyar zuciya kawai.
Chapter 66 · 0% Book details