Sashe 16
Dan Adam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
21
Acan kuwa Ummi kasa shiga ciki tayi haka kawai bata son shiga cikin mutanen gidan, tana jin nauyinsu. Amina ce ta kar6a ta mik'awa Hajiya Babba sannan suka koma inda suke. Sai misalin karfe bakwai kowa ya soma shirin tafiya wajen (Party) wanda Ango ya shirya na musamman da iyayensu da yanmata da samari. Abin har ya bawa Ummi mamaki, aganinta wannan kawai rashin sanin abinda za'ayi da kudin ne, ko kuma dai kudin ne suka yawaita garesu. Tana gani Amina tayi mata sallama suka wuce sakamakon yara da zata kula dasu a gida kafin dawowar Hajiya Maman. Ummi ta dubeta.
"Nima na tabbatar yanzu zamu wuce ko don Ramma."
"Wace Ramma? Ramma ai ta tafi gida tun dazu tare da su Hajiyar Iklima. Baki ga su Iklima sunzo dazu ba?"
Ummi ta zaro ido.
"Aa banma gansu ba wallahi, na tabbatar Mami ta manta ne da ta had'a tafiyata da su. Toh yanzu wa zan bi?"
Amina ta jinjina kai.
"Mamin ce zata barki ki tafi da kishiyoyinta? Wasa kike ma. Na..."
"Ummi, kizo inji Mami." Suka tsinci muryar Fahad wanda yayi sanadin katse Amina daga maganarta. Ta dubeta.
"To saida safe, nasan kuma mu da kara haduwa ba yanzu ba." Sukayi sallama Amina ta wuce.
Ummi tana d'ari-d'ari haka ta daure ta shiga falon, Mami na daga zaune wata tana d'aura mata d'ankwali.
Ta gaida mutanen falon sannan ta koma gefen Mami.
"Gani Mami." Mami ta dan dubeta.
"Ramma ta riga ta tafi, nikuma da wuya idan zan dawo ta nan gaskiya don gaba d'aya zamu tafi can wajen party, ki zauna a inda zan ganki idan mu fito."
"Toh Mami."
Daga haka tayi gaba, tana ji wata tana zolayar Mami wai da alama ita bata iya rayuwa saida 'yar aiki, har sauran suna dariya. Suna tsokanarta wai sai kace itace autar innartasu.
Ummi ba haka taso ba, don alal hakika ita zuwa wajen wani party ko waje mai hayaniya baya burgeta, da ace Mami zata barta anan da ta zauna har zuwa lokacin da zasu ci su cinye su dawo su tafi. Ta dubi jikjnta bayan wucewar wasu yanmata da suka dauki ado cikin wani leshi yellow da nadin kai ja, ta yaya ma zata shiga taron jama'a da kayan nan? Ta tabbatar ita kadai zata bambanta acikinsu. Ta langa6ar da kanta, kodayake daman ita din ba kowa bace face 'yar aiki. Bata da wani daraja, babu wani wanda zai ra6eta da sunan kauna ta jini ta yan uwantaka, shiyasa take matukar kaunar Amina, ta tabbatar su Amina suna kaunarta saidai bata da sa'ar 'yan uwa. Batasan halin da suke ciki ba a yanzu, da ace ma zatasan dangin mahaifiyarta, lallai da ta kai kanta garesu komin nisan dake tsakaninsu. Ta sauke ajiyar zuciya kafin kuma da saurinta ta share hawayen da suka zubomata.
Ko mintuna biyar batayi ba awajen, Mami ta aiko kiranta, kaya ta dunga kwasa tana kaiwa boot din motarsu, sannan ta zauna a motar tare da Fahad da wasu iyaye matan, Mami na fitowa suka wuce wajen party.
Tun a farfajiyar otel din Ummi tayi bala'in raina kanta. Ta sauke ajiyar zuciya gami da sakin baki galala tana kallon yanda wajen ya k'ayatu, anyiwa wajen adon fulawoyi wadanda sai buso sanyi sukeyi, hakanan kuma wajen sai kamshi yakeyi. Daga can ciki kana jiyo tashin kid'a. Wadanda basu shiga ba suna tsaitsaye a farfajiyar wajen. Haka suka dunguma zuwa ciki. Sanyi ba bak'on Ummi bane don tun bata saba shan sa ba a falon Mami, har ya zamana yanzu ta saba. Wajen kowa ya dauki kwalliya. Matasa masu ji da ilimi da gayu sai kuma iyaye wadanda kallo daya zakayi musu ka tabbatar cewa kud'i sun riga sun gama jik'asu. Zugwui-zugwui take bin bayansu Mami, gaba dayanta a d'arare take, gani takeyi kamar kowa awajen ita ya zubawa ido. Idanunta suka cika da kwalla, bata saba da irin haka ba. Tunaninta ya katse sadda ta ji an damki hannunta. Ta juya da sauri, Ihsan ta gani ta ci ado har ta gaji da haduwa, saidai fuskarta a murtuke. Bata ce mata uffan ba ta soma janta, gaban Ummi na faduwa haka ta bi bayanta har zuwa d'an (Corridor) na shiga dakin taron.
"Uban wa yace ki shigo? Kalleki kiganki, typical 'yar kauye, wallahi kika yi kuskuren shigowa wajennan sai na miki wulakancin da baki ta6a zato da tsammani ba. Shegiya kawai marar galihu!" Daga haka ta ja tsaki tayi gaba ganin mutane sun nufo hanyar shigowa. Ummi kuka ya taho mata, da saurinta ta juya zata fita, ta bawa mutanen hanya suka wuce ta bi ta gefe ta fita da gudu-gudu. Kai tsaye ta wuce bayan motoci inda babu mai ganinta ta durkushe ta soma kuka mai shiga rai. Kuka sosai takeyi, lallai ta k'ara gaskata cewar halayen DAN ADAM sun bambanta. Ta gaskata cewar ita din ba wata bace face marar galihun kamar yanda Ihsan ta jaddada mata. Kaiconta! Kaicon rayuwarta! Ace mahaifinka ya bude baki yayi furucin cewa ko bangon duniya za'a kaika, ba matsalarsa bace, baka da wani makusanci mai kaunarka, daga dangin mahaifin harma da shi kansa mahaifin. Takan rasa abinda ta yiwa mutane, wai meyasa dangin mahaifiyarta bazasu nemeta ba? Ta tabbatar koda duniya ta k'i ta, su bazasu ta6a gudunta ba, ta tabbatar zasu bambanta da sauran 'yan adam din da ta sani kuma ta rayu da su. Tana fatan su zamto irin Amina da su Anti Hauwa, tana fatan su zamto masu nunamata so da kauna ta gaskiya.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
22
K'arar rufe motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa a firgice. Ido hud'u sukayi, kallonta yake cike da tsantsar mamaki, yayinda ita kuwa take mishi kallo tamkar wacce ta ga wani dodo. Gaba d'aya tsoro takeji kada ya bud'emata wuta akan me takeyi anan. Ta sunkuyar da kanta tana duban motar, sai lokacin ta lura cewa motar da suka ganshi dazu a ciki ce.
Kamar yayi mata magana, saidai ya fasa ya juya ya soma tafiya. Ta mike ta bar wajen ta soma tafiya kai tsaye ta nufi k'ofar fita daga Otel din. Kamar ance ya juyo, ya ganta.
"Ke!"
Ya fad'a a sannu yanda yasan zata ji don ba wani nisa tayi ba. Ta juya gabanta na fad'uwa. Sai lokacin ta lura da shigarsa, ya had'u karshen haduwa, a yanzun yana sanye da shadda ruwan kasa mai duhu wacce aka yiwa dinkin da ya zauna daidai a jikinsa. Takalmi da hular da ya dora ma su kansu abin a kalla a k'ara kalla ne. A haka har ta karasa wajensa ta durkusa. Ya bata umarnin ta mik'e. Bayan ta mike ya kare mata kallo sannan ya jefota da tambaya.
"Ina zaki?"
Ta soma rawar murya.
"Gi..da." Ya yamutse fuska.
"Ke kika kawo kanki?"
Ta girgiza kai.
"To shiga ciki."
Tunanowa da maganar Ihsan yasa ta soma zubar hawaye ta dubeshi da jajayen idanunta wadanda kuka ya maidasu hakan, sai lokacin shima ya lura da su.
"Kayi hakuri Yalla6ai, bazan iya shiga ba."
Shiru ya biyo baya ayayinda ya kafeta da ido yana kallon fuskarta. Haka kawai sai ya ja guntun tsaki.
"Akan wane dalili?"
"Ih..ih.san tace kada na shiga zata wulakantani."
Ya ji wani abu a ransa, sai kuma ya cije le66ansa na kasa.
"Ko menene ku kuke jawowa rayuwarku, da ace kun hakura da yanayin rayuwa, kun godewa kad'an din da kuke samu a gidajenku, da babu abinda zaisa kuzo ana wulakantaku ana baku tamkar wasu karnuka."
Batasan sadda ta cigaba da 6ul6ulo da ruwan hawaye ba. Ta so tayi shiru ta barwa zuciyarta amsa, saidsi ta tsinci kanta da kasa aikata hakan.
"Ka gafarceni Yalla6ai, saidai akwai lokutan da ba'ason ran mutum yajr aikata abinda ya aikata ba. Akwai tilastawar rayuwa, wani ba shi da yanda zaiyi ne, sai yaga da yaje ya aikata abin turr gwara ya gwammace ya rufawa iyayensa da kansa asiri ta hanyar nema ta halal. Wani kuwa, rashin gata da rashin samun kulawar yan uwa ke sanyashi tsintar kai a halin da yake ciki. Kowane bawa da yanda Allah Ya tsaro rayuwarsa, ba mu muka za6awa kanmu wannan rayuwar ba. Akwai KADDARA."
Daga haka ta juya da sauri-sauri ta bar wajen gami da nufar get, batayi wata-wata ba ta fice daga wajen batare da tasan inda ta nufa ba, burinta kawai tabar wajen ko ranta zaiyi sanyi....!