← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 146

Sashe 98

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ta tattara kayanta ta fice ta bamu waje.
Ya matso ya zauna a gefen gadon da nake kai. Ya zuba mini ido tare da ce wa "Sannu little. Ban zaci zaki iya haihuwa da kanki ba. Mussaman da na ga Ubaida da Nasiba masu garin jiki sun gaza haihuwar da kansu".
A hankali na ce "Haihuwa ikon Allah ke sawa a yi ta lafiya ban da haka kam da iyayenmu basu taramu da yawa haka ba".
Ummi da take gefe ta murmusa ta ce "Yabi an je kusa da lahira an dawo."
Ya ce "Ummi ai ni da kaina na tausaya mata, haihuwar yara biyu tashi guda, sannan ki gansu manya tamkar ba tagwaye ba? Wani ikon Allah bamu yi zaton yan biyu ba ne, Ubangiji ya boye su ko sikanin din da aka yi bai nuna ba."
"Ikon Allah ya fi ga hakan ai" Yaya Ummi ta fa'da a hankali.
Ya sake kallona ya ce "Asiya kin ga yaran nan kuwa, kina ganin yadda Ubangiji ya mana kyautar da ba kowa yake yiwa irinta tashi guda ba?"
A hankali na ce "Ai ban gansu ba, ba'a bani na ga ni ba, kunya kuma ta hana ni na tambaya".
Ya yi hanzarin sake matso wa kusa da ni tare da d'ora mini yaron akan cinya a hankali. Cikin nutsuwa yake ce wa "kalle shi da kyau Asiyata. Kalli ki ga yadda suke kama da ni. Kalle shi, ki masa addu'a, ki kuma gode wa Ubangiji bisa d'inbin baiwar da ya yi mana".
Na zuba wa yaron ido. Ina son ga ne kammannin da Tijjani yake fa'da. Amma na kasa tantance wa, domin ni kam bana ga ne kammannin jarirai. Na tsananta kallonsa, ina jin wata irin nutsuwa da kaunar yaron na shigata sannu a hankali. Na saka hannu ina duba yatsun hannunsa da na tabbatar irin nawa ne.
A hankali Tijjani ya ce "Yusuf ke nan (Baban Bulkachuwa) ki masa addu'a, shi ne babban".
A fili na furta "Allah ya raya shi, ya saka shi cikin bayinsa da yake sonsu. Allah ya masa kyakkawar rayuwa. Allah ya bashi basira da azanci, ya saukaka al'amarinsa, ya kuma ba shi kyakkawan rabo a lahira".
"Ameen ameen" Tijjani yake fa'da cikin wani irin yanayi.
Da azama ya ce "Ummilolo kawo shi, shi ma ya samu tabararakin addu'ar uwa."
Ya dauke wanda ya kira da Yusuf. Yaya Ummi ta d'ora mini na hannunta ta koma gefe. Ya gyara rikon na hannunsa ya ce "Kin ga yadda suke kama da juna ko? Tagwaye ne masu kama da juna kwabo da kwabo(Identical twins)".
Na gasgata shi, domin ni kaina idan aka jere mini su bazan iya banbanta su ba a yanzu.
Na zuba masa ido tamkar yadda na yiwa d'anuwan sa. A hankali Tijjani ya ce "Muhammad Sani ne wannan(Baban Marina)."
Haka kawai na ji tausayi yaron ya shige ni. Kaunar sa ta shiga mamayata.
Cikin rauni na ce "Allah ya raya shi, ya sanya shi cikin bayinsa da yake kar'ba daga garesu. Allah ya saukaka al'amarinsa, ya kimsa masa ilimi da azancin sarrafa harshe. Ubangiji ya sa ya dace da kyakkawan rabo a lahira".
Shi da Yaya Ummi suna ta fa'din "ameen".
Ya sake kusantowa gare ni. Ya ha'demu gaba'daya ya rungume. A fili ya ce "Allah ga ahalina, ka so su, ka taya ni kula da al'amarinsu, ka tsarkake mini su. Ubangiji ka basu kariyar da ni ba zan iya basu ba. Ka zame mini jagoran wajen sauke nauyinsu da ka d'ora mini. Allah ka bawa uwarsu lafiya da juriyar raino da tarbiya. Ina ro'kon ka saukar da albarka a cikin gidanmu da rayuwarmu gaba'daya".
Ya dinga kaiwa kuncina da goshina sumba.
Jaririn da yake hannuna ya fara mutsu mutsu da k'ananun kuka tabbacin an takure shi. Da azama Tijjani ya janye daga gare ni.
Yaya Ummi ta matso da nufin d'aukar yaron. Ya ce "Ashe ba ki fita rarashin Dada ba Ummilolo? Da kika ga sun fice ai sai ke ma ki bi bayansu ki bamu waje".
Ta ce "ka gama borin kunyar ka dai".
Ya matse ya ce "To ba daukarsa zaki yi ba. Taimaka wa zaki yi ya sha. Da alamu yunwa yake ji sai tsotson hannu yake yi".
A hankali ya na ce "A a ai ya d'an sha d'azu. Zafi Wallahi!.
Cikin tausayi ya ce "Ki yi ha'kuri, zafin na d'an lokaci ne k'alilan".
Kan dole na yarda na ba shi. Shi kuwa yaro sai zuka yake yi babu jinkiri da alamu sai yafi d'an uwansa tsotso.
Ana hakan na hannunsa shi ma ya fara nasa sukur sukur din.
Ya mike ya saba shi a kafa'da, yana dan juyawa.
Daidai nan su Babah suka shigo. Ta kalle shi ta ce "Bawa Ummi shi, ka zo ka tafi. Ka zo ka yi kane kane ko kunyar iyayen pka baka ji".
Ya bada yaron ya fice ba tare da ya sake ce wa komai ba.
Kwana na yi da yini sannan aka sallame mu. Yara lafiyarsu k'alau.
Kai tsaye gida aka zarce da mu. A dakin Gwaggo muke yin jego. Hidima kan hidima Tijjani da mahaifiyarsa suke yi. Har sai da Baban Marina ya ce "Ka bi a sannu Tijjani kada ka yi bashi". Tun kafin ranar suna aka lankayawa Yusuf(Hanif). Muhammad Sani kuma (Hamim)
Har ranar suna ta zo aka yi taron sunan tagwaye cikin rufin asiri. Na yi kwalliya da leshi, da kuma kyawawan sabbin material din Umm Nihla....
Har kala biyu. Kyaunsu da sau'kinsu ya sanya Tijjani ya siya mini kala biyu. Leshi kuwa a cikin na lefena na dauka na dinka.
Fayyace irin kayan da muka samu ni da yan biyu bata lokaci ne. Domin gadajen Gwaggo duka biyu sai da suka cika da kayayyakin barka.
Babbar matsalar da ta fara damuna rashin warke wa ta. Tafiya ta a bubbude. Na je asibiti sun ware d'inkin. Suka ce na dinga kama ruwa da ruwan dumi da dan gishiri a ciki zan warke.
Sosai Gwaggo take kula da ni. mun warware mun ciko ni da yara. Na murje tamkar ba yara biyu nake shayarwa ba.
Matsala biyu ke damuna ta farko kukan yara. Domin idan dare ya fara nisa suka fara kuka, babu me yin barci a k'ofarmu. Da daya ya fara, d'ayan ma zai dauka, su taru su kidamamu. Basa dainawa sai an yi assalatu.
Dada kuwa sai fadi take yi "Ai kuka ma basu fara ba, tunda an riga an yi musu sanadin wahala. Waye zai sha mataccen nono ya share k'alau?"
Matsalar ta gaba kuma nake jin na bu'de. Ina jin yadda iska ke shigata. Nasan na karu amma ban yi zaton dinkin ba zai ha'de ni ba.
Ga shi ban fasa kama ruwa da ruwan zafi ba. Na kasa jin da'din kaina. Na kasa fa'dawa Gwaggo. Yaya Ummi na zuwa na fa'da mata. Ta ce "na sa a kawo sassake da saiwowi kalakala da ake kawo wa daga chadi."
A kunya ce na ce "Na gode.
Kwana biyu a tskani sai ga ta dawo da kayan. Da kanta ta dafa mini, ta ware mini butar da zan dinga zuba maganin.
Dan kama ruwan da na yi da ruwan maganin har na fara jin da'din jikina. Da zata tafi ta hada kan kayanta ta tafi da su. Ina son na ce ta bani koren maganin da na dafa kazar, amma na kasa a dalilin kunya ta yi mini k'awanya.
Na tuna ranar sunan Ubaida yadda su Nasiba da su Maijida suke koda kyaun kayan da suke siya daga Kano ta hannun Yaya Ummi. Na tuna sadda ta bani ina amarya na ki kar'ba.
Chapter 98 · 0% Book details