← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 146

Sashe 71

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Yanayinsa ya saka kukan ya tsaya cak. Na rasa gane tausayi yake bani ko kuwa mene ne? Washagari bayan ya dawo daga gidan burodi ya gama duk abin da zai yi mana. Ya kawo mini abin karyawar har d'aki. Fuskarsa babu walwala ya ce "Sai na dawo". Ban amsa ba. A dalilin kuttun da ya shak'e ni. Don me zai fita? Ba zai zauna ya kula da lafiyata ba. Ya tafi bai jira amsawa ta ba. Na dinga kuka. Zuciyata tana kissima mini ai ya samu abin da yake so shi yasa bai damu da ya tsaya na yi wanka ko na karya ba . Da rana ya dawo, ya zauna ya kalle ni. Yayin da ni kuma na d'aure fuska sosai. Ganin hakan ya mik'e shima fursakarsa a d'aure ainun ya ce " Ban samu ku'di na siyo abin da zaki ci ba. Me kike son ci na dafa miki?" Cikin son na wahalar da shi na ce "Faten doya da wake. Sannan da alaihu da kifi a ciki." Ya nisa ya ce "Ba ni da kudin da zan sayi kifi yau. Zan dai je na siyo alaiyahun. Ya fara tafiya da nufin fita. Na bu'de baki na ce "Zo ka kar'ba. Ni ina da kudin". A zafafe ya juyo "Cikin kaushin harshe ya ce "Asiya Toro baki da kudin da zaki yi mini cefane matu'kar ina da lafiya, ina kuma kan k'afafuna. Ba zaki yi ku'din da zaki aike ni, na siyo abu sannan na zo na girka miki ba, har abada kuwa". Ganin yadda ya rikice ya koma Bulkachuwan sa sai na yi maza na kame, domin na sani yana iya dauke ni da mari. Na laluba na kasa gane fishin me yake yi tun dare. To me na yi masa? Ni da ya ganawa azaba ma ban yi masa zafin kai ba sai shi zai dinga yi mini muzurai da hargagi?. Ya yi k'wafa ya fice bayan ya jira na tanka, amma na yi muk'us. Ina ta jin b'ab'atunsa a kicin. Ga mamakina sai ga shi ya kawo mini lafiyayen faten doya da wake a ciki. Ya ji alaiyahu da albasa mai lawashi. Nabi bayansa da kallo. A dalilin bai zauna ba fice wa ya yi. Ina jinsa a kan baranda ya zauna yake cin nasa. Haka kawai sai na ji guiltiness na kama ni to me na yi masa?. Da ya gama bai lek'o ba. Daga inda yake ya ce "Sai anjima". Na rasa gane manufar wannan abin da yake yi. Da daddare ma da ya dawo bayan ya yi wanka. Ya dube ni ya ce "Zaki ci donot da tea ne, ko kuwa da abin da kike son ci?" Cikin kuka na ce "Bazan ci komai ba Tijjani. Na hutar da kai" Na cigaba da gunjin kuka. Da farko kamar ba zai tanka ba. Sai kuma ya kasa jarumtar share ni. Ya ce "Wannan kukan fa? Ko dan na fa'da miki bana so shi yasa kike ta yi, tunda burinki ki kassara ni da ba'kin cikin ki".
Chapter 71 · 0% Book details