← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 146

Sashe 75

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

53&54. Ta ko ina nake jifan sa, gaba'daya na hargitse dakin. Da k'yar ya samu ya ri'ke ni ya dauke ni caraf ya d'ora a cinyar sa ya rungume ni tsam tsam. Gaba'daya na shige jikin na yi luf, sai kukana kawai yake tashi, wanda na shagwaba da kishi ne. Cikin rad'a yake ce wa "So ki ke ki illa ta ni ne?" Da k'arfi na ce "Eh. Wata'kila dan ka ga kana da kyau ne ya sanya kake ganin ko wacce mace ka ce kana so, ba zata tankwabar da kai ba. To gara na rugurguza ka. Tunda ni kyaun naka bai rud'e ni na makance akan ka ba" Ya sakar mini wani irin nishi a kunne, sannan ya dan cizar mini shi ka'dan. Yar na ji jikina ya amsa. Na fara fizge fizgen bazan yarda ba, sai nima na cije shi a nasa kunnen. Shi kuma ya dinga dariya yana cakuma ta son ransa. Babu zato ruwa mai k'arfi ya goce. D'akin ya yi duhu saboda ko ina rufe yake gudun kada ruwa ya shigo. Wannan yanayin ya sake susuta Tijjani. Ni kuma na dinga koke-koken jan rai. A ki'dime yake rarrashina. Fa'di yake "ki yi ha'kuri I will be soft and gentle." Ni kuwa sai botsare wa nake yi. Tare da ce wa "Ni dai ba da'de wa zaka yi ba." Da rawar murya ya ce "Nà yarda amma idan kika cije ni, ko kika yi mini fallashasshen kuka. Ki tabbatar kina cikin komar mala'iku". Na yi shiru. Amma zuciyata sai harbawa take yi. Domin har zuciyata nake jin tsoron al'amarin. Ina ji ina ga ni, ya shiga yin yadda ya ga dama da ni. A farkon tafiyar gaba'daya na kankame jikina ina sauraron jin matsanancin zafi. Amma ga mamakina sai ban ji ba. Har na sakankace na saki jikina. Wanda hakan ba k'aramin dadi ya yi masa ba. Ya k'ara haifar masa da kuzari mai yawa. Dan haka lokacin da ya shafe yana abu daya, bai dame ni ba. Bayan ya nutsu. Ya rungume ni yana ta faman sakin kalaman yabo da soyayya. "Asiya da hakan kike yi mini, to me zai sa ma na yi fishi da ke? Bare har na yi tunanin k'arin aure. Na gode sosai, Ubangiji ya sanya albarka a rayuwar ki gaba'daya." Na yi shiru. Amma zuciyata sai kai kawo take yi akan abin da nake son amayar wa. Na kasa jarumtar ha'diyewar murya babu amo na ce "Yo ni ai tunda wula'kanci ka shiryo mini daga yin aure za'a ka fara neman wani dan kawai ka nuna wa duniya bani da wata kima a idonka. Wallahi ba zama zan yi ba. Zaka wayi gari ne ka ga na bace maka." A diririce ya sake ru'ko ni sosai tare da ce wa "Kar ki tayar mini da hankali dan Allah. Na fasa, dama dan na rasa yadda zan yi ne. Amma yanzu indai kin daina yi mini abubuwan da kike yi. Wallahi bazan sake tayar da maganar ba. Ke ko hanyar da ta bi, bazan sake bi ba". Cikin kuka na ce "Daga baya ke nan. Wadanda suka ganka kana zuwa tadi ai tuni sun san baka son Yabi. Dan haka kuwa ba yarda zan yi ba. Ka je ka cigaba da abin da kake yi, ni ma zan samu mafita Wallahi". A raunane ya ce "Bana son kukan ki Asiya! Amma sai ki ta yi mini, dan kawai ki gigita ni. Ban iya yaudara ba. Na ce miki, na fasa, na janye, to ba shikenan ba?" A zabure na ce "Ba shike nan ba". "Da azama ya ce "To fa'da mini yadda za'a yi, me kike so na yi dan ki gamsu?" Na dinga gunjin kuka da na tabbatar yana jijjiga shi. Ya dinga shafa kaina, yana fa'din " Sorry Asiyata! Na ce bazan sake ba, ki yi ha'kuri da gaske na fasa. Dan Allah mu rufe maganar nan haka. Me kike son ci na dafa miki?" Na fara kokarin fizgewa daga rugumar da ya yi mini, amma na kasa. Cikin tab'ara na ce "Bazan ci ba. Yau kwana nawa rabon ma da ka tsaya ka saurare ni akan maganar abinci. Ko na ci, ko kada na ci ai babu ruwan ka". Ya sake sassauta murya ya ce "Wula'kanta ni fa kike yi. Ta ya ya zuciyata zata ji da'din kyautata miki? Yanzu kuwa ai komai yi miki zan yi da kaina". Na cuna baki na ce "Abar maganar abinci. Ka tashi tunda ruwan ya tsaya, ka kwaso kayanka da ka kai mini wanccan d'akin dan kawai kana nema na da jidali". Ya zabura ya tashi. Ya lalubo jallabiyarsa ya d'ora akan gajeran wandon bai ce komai ba ya fice. Ya kwaso su tsab. Ya mayar dasu inda suke. Ya juyo ya ce "Na kwaso, shike nan?" Na bata rai na ce "Ba shike nan ba. Kada mu samu sabani ka sake yi mini hakan. Tijjani ba ruwanka da d'akin can. Nan ne dakinka. Idan kuma zaka dinga fitina ta akan dakin to ka sani zan tattara kayan gadon na mayar maka can din. Tunda nan d'akina ne da shari'a ta ce ka bani shi tilas. Idan anan nake sana'ata ban shiga cikin dakin ba, ai na tsira ko?" Ya yi wani irin murmushin da na fahimci mai harshen damo ne. Ya numfasa ya ce "Namiji ai ba yi masa shamaki a gidansa. Dan haka mu zauna lafiya mu mutuntata juna shine kawai. Amma bazan yarda ina tattala ki, ke kuma ki ce zaki dinga wula'kanta ni, sannan kuma na yi miki yadda kike so." Ya girgiza kai ya ce "Ba haka Tijjani yake ba. Ba kuma zai zama hakan ba". Na kura masa ido na tabbatar iyakacin gaskiyar sa ya fa'da. Na rasa me zance masa domin na tabbatar duk bala'ina. Idan ya kunsa mini ba'kin ciki daya tak kwana zan yi na yini cikin ba'kin ciki mai tsanani. Dan haka sai kawai na buge da sake fashe wa da kukan. Daga inda yake tsaye, ya ce "Allah dai ya taimake ni ki hau ko na samu sau'kin wannan rikicewar da gangan. Idan kina ganin baby a hannunki wata'kila kya daina yi irin wannan sakalcin." Yana rufe baki na fara nuna kaina cikin kuka ina ce wa "Tijjani ni ce sakaliya?" Kafin ya amsa mini na rausayar da kai na ce shike nan na gode da wannan tukuicin". Ya taho da sauri yana kuma dariya. Ya rike k'afafuna ya ce "Ina nufin sakaliyata fa". Na yi tsuka na juya. A sanyaye ya ce "Bana son tsuka Asiya. Amma na yafe miki, ban yi fishi ba". Daga hakan ya koma ya fita. Na tabbatar kuma kicin zai shiga. Ni dai daga nan barci ya sure ni. Sai bu'de ido na yi na ganshi ya yi wanka ya shiraya tsab. D'akin ma ya cika da kamshin turaren nasa. Yana daga jikin sif din yana saka links ya ce "Yanzu dama zan tashe ki, na kai miki ruwan wanka". Ban ce komai ba, na tashi, na daura zani a kirji sannan na saki zanin gadon na sauko. Ya kalle ni babu riga a jikina. Ya ce "Asiya Toro a gabana babu riga. Sai na sake ganin ki wata yar kwaila, a hakan tamkar ba zaki iya komai ba. Nan kuwa al'amarin da yake tare da ke azimin ne". Na cuna baki na ce "Ai ni na gode Allah ma da aka baka yar mitsil din. Kai da rusa rusan mata sai kallo daga nesa. In juninka cusawa mutum takaici ne. Har abada kai da zunduma zunduman mata". Ya murmusa duk da dai yana kokarin shanye dariyarsa. Ya ce "Wato baki ji da'din yabon da na yi ba, sai kika dauki abin da bai yi miki da'di ba, kika yi raddi?" Na share, na dauki tawul na fice abina. Na dawo na tarar da shi ya gyara gadon tsab. Ya share dakin. Na kasa hakuri na ce "Tijjani wai a ina ka iya gyaran gado ne, tunda kullum dakinka na gida a hargitse yake, sai asarrariyar can ta gyara maka shi yake yin fasali". Ya dauko mai yana murmushi ya tarar da ni a bakin gadon. Na yi kamar na hana shi shafa mini mai din sai na fasa kuma. Domin a dan zamanmu na fahimci yana matu'kar son ya shafa mini mai, kafin na sanya komai a jikina. Ina ji ina ga ni ya dinga shafe ni da sunan shafar mai wanda ni kaina ina matu'kar jin sakon nasa a dukkan jikina. Yana cikin murzar tafin kafata. Wanda kafin ya zo kafar ya shafe mintina sha biyar. Murya dakushe tabbacin so yake ya koma ruwa ya ce "Nasiba ce asarrariyar Asiya?" Na fizge kafata na tashi. Na ce "Ina dalilin gatsa sunan matar wani ne Tijjani? Kusan mintina ashirin da yin maganar ashe duk yadda na barka kake yin yadda kake so da sunan shafar mai, zuciyarka na tunanin suntumemiyar halitta ko? Wallahi bazan iya da bala'in ka ba Tijjani! Ganin da gaske na fitittike, zan birkice masa. Jikinsa na bari ya ce "Allah ya baki ha'kuri, na yi kuskure. Sai dai ya kamata ki mini shaidar tun ma kafin a mini babban alherin ba ni auren ki ai na fita a dukkan sha'aninta. Bare kuma yanzu da take matar wani. Dan Allah mu bar maganar, bana sonta. Ki yi hakuri." Ya dauko mini wata riga ya ce "Ga gifts din ki na zama matar aure, tun first night dinmu nw so baki, to bata iso a lokacin ba." Cotton yar kanti. Gaba'daya rigar tafi dacewa da yara y'an shekaru goma. Domin har da teddy wacce aka yi jakar goyo da ita. Sannan da hula irin mai malafar nan. Kalar ruwan hoda (pink )da yarfin filawa mai ruwan lemon tsami (lemon green) ce. Ba karamin kyua ta yi ba. Ya mik'o mini sabon pant. Ya ce na saka miki?" Na juyar da fuska. Ban amsa ba. Sai da na shanye kunyar na na ce "Tijjani da gaske dai kallon yarinya kake mini. Ban da haka wannan rigar ai ta yiwa Iklima ka'dan bare ni. Kasan kuma Anas ne yake bina ba ita ba." Kai-tsaye ya ce "Na sani. Sha'awa ta bani, shine na yi kundubalar d'auko miki ita, rabin ku'din na bayar.
Chapter 75 · 0% Book details