Sashe 24
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ko shayi. Haka idan zai fita zai bata mukullin dakinsa ta je ta gyara masa. Bai zame masa komai ba, ya kawo mata kayansa matu'kar zai ga tana wanki, yana fa'din "Ga karo". Bata damuwa hakan zata karba, ta wanke, ta goge. Shi kenan sai yake sassauta mata ya daina yarfa ta. Ita kuma ta dauki son duniya ta d'ora masa bata ko lura da rashin nagartarsa, duk kuma wanda zai zo da nufin yana sonta bata sauararansa, sai Dada ta yi mata wuta wuta. Matu'kar kuwa yana gida ba zata yarda ta fita ba, duk tijarar Dada kuwa. Tunda mahaifiyarta ta ce bai cancanci a bashi aurenta ba, ya dauke mata wuta, ya daina kula ta, ya koma muzurai ne a tsakaninsu shi kenan sai ta k'aratanwa kanta walwala, tunda ba yadda bata yi ba, ya fahimce ta shi kuma ya taurare. Saura kwanaki biyu aure domin tuni gidan ya fara cika da jama'a ana ta hidima tuni an yi wa amare jere. Da ni aka je jeren Adda Nazi, na dinga k'walla a dalilin irin rufin asirin da Ubangiji ya yi mana. Komai ya yi, ba wanda ya zaci za'a samu hakan. Na dawo Yaya J ya rutsa ni a soro. Murya a dushe ya ce "Yabi mene ne ya yi zafi ne, shin gaba zamu yi?" Da sauri na ce "Eh mu yi gabar kawai, yafi mini sauki da na saurare ka." Ya numfasa ya ce "Oh no! Kada ki yi mini hakan, ya miko mini leda mai dan dama. Na dauke kai na ce "Bana bukatar komai na ka". Ya rausayar da kai ya ce "saboda zumunci na baki fah". Na ce "To kuwa bana so, domin na shafe alakar da ta ha'damu". Ya fusata, sai kuma ya ha'diye dukkan fishin ya ce "To karbi dan Allah, dan soyayyar da nake yi miki". Na mika hannu na kar'ba ba tare da na ce uffan ba. Ya sassauta ya ce "Wannan auren ba zabina ba ne Yabi, ba abin da zuciyata ta za'ba mini ba ne. Dan haka zan yiwa kaina auren da zuciyata take so take kuma muradi. Na rok'e ki, kada ki juya mini baya. Kada ki haramta mini farin ciki a zuciyata da rayuwata." Yana diga aya sai kawai na rushe masa da kuka mai tsananin gaske. Fadi nake "Lallai kuwa wato zan yi ta zaman jiran ka ko? To ko dai kallon Yabin mahaukata kake mini ba ta Marina ba?" Ya ki'dima ya ce "me ya kawo wannan maganar? To ai ni ko a turu nake kallon ki ra'ayil aini, zan cigaba da son ki babu gazawa, cikin kowanne hali son ki nake yi, zan kuma cigaba da son ki YABIN J". Na ha'diye kukan da nake yi. Na zuba masa ido na ce "Na gode da soyayyar ka, Allah ya bada lada". Kafin ya yi magana Bulkachuwa ya shigo, ya kalle mu kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya kasa ha'diye maganar ya ce "Poor baby haka kawai kin zuba ido an k'wace miki abin da yake na ki ne, ni fa akan abin da nake so sai dai ayi kare jini, biri jini da ni." Ya kalli J ya ce "Jabir ka daina tare yarinyar nan tunda dai an baka wata ka karba, bar ta ta ji da suyar da kirijinta yake yi mata kawai". Yaya J ya daure fuska ya ce "Menene hakan kuma Bulkachuwa?" Ai kuwa ya ce "Gaskiya ce mana Jabir, ni yanzu da aka hana ni Nasiba ka ga na damu ne? Ai saboda dama soyayyar ba mai karfi ainun ba ce. Da son ya zama so deep da komai zai faru, ba zan yarda na musanya ta da wata ba".