← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 146

Sashe 73

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

Ga shi yanzu yanayin damina ne. Idan ruwa bai zuba ba rana ake yi, idan kuma an yi ruwan ba damar zama a waje.
Ya shigo na ha'diye haushinsa na yi masa sannu. Na kawo donot da flask din shayi. Sai da muka kammala. Na dauko dukkan cinikin da na yi a ranar. Na tura gabansa.
Na sassauta murya na ce "Tijjani ka ga cinikin da na yi yau ka'dai. Na ro'ke ka daina hana ni. Na yarda kullum kana da kaso a cikin ku'din da zan samu".
Ya fusata irin sosai din nan.
Ya nuna ni da hannu.
Ya ce "Ke ce kike mutunta ku'di irin haka. Na kuma sha fa'da miki ce wa baki da kudin da zan sa ido akansu bare har ki yi mini iyashege saboda su. Ya jijjiga kai ya mike tsaye bayan ya dangwarar da kofin shayin.
"Da nasan zaki kalli idona ki yi mini irin wannan tayin na raini Billahillazi da dazu ban yarda na karbi ban hakurin ki ba. Amma shike nan. Daga yau din nan bana bu'katar ayi mini lalle da kitso a gidan nan gaba'daya ma".
Ina jin hakan na takarkare na ce "Bilhiillazi ba zai yiwu ba, komai kake ji da shi Tijjani, baka isa ka hana ni sana'ar da ka gan ni da ita ba! Duk masifar ka kuwa".
Ya murmusa ya ce "Lokacin da aka dauke ki aka ba ni babu shawarata ai ba a ce mini mata zasu dinga yi mini zarya a gida ba. Dan haka yanzu da na ga bazan iya d'auka ba, na dakatar da su".
Na sake hassala na ce "To wai dole aka yi maka ka zauna da ni?
Na ce ba na sonka, kai ma baka sona, to mu rabu mana. Mugunta ce kawai ta sanya ka ri'ke ni, kake musguna mini."
Ya ce "Shike nan bar shi a muguntar ne kawai. Sai dai ki sani na riga na samo wa kaina mafita. Ki saurari abin da zai biyo ba. Ban karbi auren ki ba sai da na kudire wa zuciyata komin rintsi bazan bari mugun halinki ya sanya na kunyata Baban Marina da Babah ba.
Ki je ki karaci diban albarkar ki. Ai Ubangijin adalci ya riga ya samar mini mafita a cikin wula'kanta ni da kike yi tun kafin a halicce ni".
Daga haka ya fice.
Gaba'daya na kasa gane manufar maganganunsa. To wacce manufar ya samo?
Na kwana ina tauna maganganun Tijjani. Zuciyata ta yi nauyi a wajen son na fahimci inda ya dosa.
Ko dokar da ya sanya mini ta hana ni sana'ata bata tokare mini wuya ba. Irin son na gane mafitar da ya samo.
Kwanaki biyun da suka biyo baya, zaman namu ya sake yin tsami bisa dalilai guda biyu. Na farko ya tire kan ra'ayinsa na kada a ayi masa lalle a cikin gidansa. Sannan ya tsiri ya yi wanka ya sheka kwalliyar da ni na koya masa yin ta. Da daddare zai dauki wankakken kaya kuma gogagge ya fesa turaren da duka gidan sai ya amsa tsabar bulbulawar da yake yi, sannan ya fice ko kallon inda nake ba zai yi ba bare ya yi mini sallama.
Ba zai dawo ba sai goman dare ta shud'e.
Wannan al'amarin ba k'aramin ci mini kwarya yake yi ba.
Na rasa inda zan tsoma raina da ba'kin cikin da Tijjani yake guma mini. Mussaman na barina a gida da daddare ni ka'dai kamar mayya.
Ranar da muka yi sati a cikin wannan halin. Na bugawa Yaya Ummi waya, ji na babu kuzari ya sanya ta dinga fa'din "Mene ne, me ya same ki Yabi?"
Na kasa bu'de baki na ce mata uffan, illah kukan da nake yi mai cin rai, mai kuma sauti sosai. A lokacin kuma dare ne sannan yana gidan.
Ya ji ni sarai, tunda a lokacin yana falo. Amma ya yi kamar bai ji ba.
Washagari da asuba sai ga Yaya Ummi ta diro mana gidan.
Tausayinta ya kama ni. Yargale yargale da ita. Da alamun ma kukana bai barta ta yi barcin kirki ba.
Ta same ni kad'ai a dalilin bai dawo masslaci ba.
A gigice take tambayar me yake damuna?
Murya a dashe tsabar kuka na ce "Tijjani yana shirin kashe ni da raina ne. Haka siddan ina zamana ya saka mini rai zai mayar da ni makaranta na samu shaidar kammala sakandire.
Yanzu ya zo ya ce ya fasa. Hakan bai ishe shi ba sai ya ha'da har da soke sana'ata. Sannan dan yasan Baban Marina ba zai saurare ni ba, sai yake amfani da hakan yake musguna mini. Fiye sati yana gaba da ni. Sannan kulllum dare sai ya sheka wanka sannan ya fice ya bar ni a gida sai dare ya raba zai dawo. Ni nasan Bak'ar TA'ADAR sa ya koma. An cuce ni Yaya Ummi."
Na fa'da ina rushe wa da kuka sosai.
Daidai lokacin kuma ya dawo, amma kukan da Yabi take yi tamkar na mutuwa shi ya hanasu jin motsinsa. Ya zauna a barandar yana son fahimtar abin da yake faruwa.
Jikin Yaya Ummi ya yi sanyi. Ta ru'ko hannuna ta ce "Yabi nutsu ki ji ni. Shin me kike masa yake yi miki hakan?".
Cikin kuka na ce "Bana yi masa komai".
Ta numfasa ta ce "Me yasa kike gaba da shi? Da kina gaishe shi, na tabbatar Yaya Bulkachuwa zai masa miki."
Na yi shiru dan kuwa gaskiya ta fa'da.
Ta sake ce wa "Da kin ja shi a jikin ki, da ba zai iya fitar da yake yi ba. To me zai yi a wajen bayan yana da d'anyar amarya mai cike da shiriritar kuruciya?"
Na bata rai na ce "Kawai saboda ke da shi akwai amana da yarda shi yasa kike shaidar sa a bayan idonsa ni kuma kike bani laifi a kan idona ko?"
Na fa'da hawaye na ziraro mini.
Ta tsananta ri'ke mini hannu ta ce "Gaskiya ai bata bu'katar ado Yabi. Babu ruwan alk'alami akan kina so ko ba ky so. Kawai girman hakkinsa da ya rataya a kan ki za'a duba. Idan baki sau'ke ba Wallahi halaka zaki yi Yabi. Ni yanzu son nawa mijin nake yi? Amma na yarda kaddara shi ta zaba mini. Dan haka na yi hakuri nake yi masa biyayya, duk da shi din ba duka yake sauke hakkin da shari'a ta gindaya masa ba. Amma na sani ina rabo mai girma a wajen Azza wa jallah".
Na tsananta kallonta domin gaskiya ta fa'da. Har zuwa yanzu da ta zarce shekaru goma da aure bata son mijinta, ni shaida ce akan hakan, amma kuma ha'kuri da biyayyar da take yi akan sha'aninsa mai yawa ne.
Ta numfasa ta ce "Yabi ba kya yarda da Tijja
Yaya Bulkachuwa. Su kuma maza da kike ganinsu komai zaki yi musu na kyautata wa matu'kar ba kya mutunta shinfidarsu, to fa komin kokarin ki a banza ne a idonsu. Saboda haka ki d'auki matakin gyara a tsakaninku."
Na nisa na ce "Baya gamawa da wuri Yaya Ummi. Ni gaskiya bazan iya ba."
Ta ce "Ahab dama da labarin neman auren da yake yi ya riske ni, sai da na ce na tabbatar ke ce silar k'arin auren sa. Ai sai ki yi tunda al'amarin kishiyata bai saka kin k'yamaci kishiya ba".
Wani irin abu ya soki k'irjina, ban san mene ne ba. Amma gaba'daya ji na yi tamkar zan shid'e.
Na rushe da kuka mai tsananin gaske.
Ta ce "Ai indai kika cigaba da tafiyar da shi a hakan, tabbaskuka na gaba. Ba ki ga Bilkin da yake zuwa wajenta ba, gansamemiya ta yi biyu da rabin ki."
Da rawar murya na ce "Me za'a yi da mai BAK'AR TA'ADAH irin ta Tijjani. Aure ko rufa wata biyu ba'a yi ba har ka fara neman wani auren. Na rantse Yaya Ummi sai dai a tsine mini. Amma bazan taba zama da wata macen a k'arkashin ikon Tijjani ba".
Ta sake ru'ko hannuna ta ce "Idan kina son ki zauna lafiya, ki yi sana'arki, ki cigaba da tallafa mana. To ki zauna lafiya da mijin ki, ki daina gudunsa, ki yi hakuri da shi watarana sai ki ga kun kai ga babban bigire. Ni fa na dauka ma ciki ne da ke. Jiya nan na je gidan Ubaida na tarar tana ta kwarara amai. Da kaina na rakata asibiti aka tabbatar ciki ne da ita. Kin ga kuma ai kanwar ki ce duk k'uruciyar ki ai kin fita a haife. Jabir din da kike ta kulafacinsa matarsa wata tara ta haihu. Sai ke ce zaki zama shasha wacce bata san me yake mata ciwo ba. Da ace kin kwantar da hankalinki da wata'kila ke ma da na ki cikin a jikinki".
Kunya ta rufe ni, na ce "To yanzu dai ki fa'da masa ya bar ni na yi sana'a ta."
Ta ce "A yanzu bazan yi masa magana ba. Idan kin canja kin daina gudunsa, bai bar ki ba, sai na yi masa magana. Amma yanzu ai ke ce zaki fara zuwa da gyara".
A sanyaye na ce "To".
Amma k'irjina tamkar ya fa'do a dalilin nauyin da yayi akan batun tsohuwar budurwar Bulkachuwa wacce aka kai masa ku'din aurenta aka k'i karb'a. Tun lokacin ya fita a harkarta amma ita take ta nacin ya yi hakuri.
Tijjani da ya yi bakam yana sauraronsu. Ya saki gauron numfashi yana k'ara ganin hankalin Ummi. Sai dai mamakin da ta bashi a ina ta ji yana zuwa wajen Bilki?
Shi yasan tunda aka yiwa su Baban Marina wula'kanci bai sake taka gidansu ba har yau. Idan Ummi ta fa'di hakan da nufin yiwa Yabi barazana. Ya tabbatar liki ta b'allo masa.
Duk yadda Yabi take kirarin bata son sa amma kuma kishi take yi akan lamarin sa ba ka'dan ba. Duk da dai ya yi amanna kishi dabi'arta ce.
Amma ya tabbatar wannan maganar sai ta ri'ke ta a ranta.
Ya saki gauron numfashi yana fatan a sami dai-daito a tsakaninsu.
Tsawon lokaci yana sauraronsu, yana jin irin yadda Ummi take ta wasa shi tare da ban baki a madadinsa. Wanda hakan ba k'aramin kaunarta ya k'ara ji ba.
Jin tana haramar tafiya ya sanya shi mike wa ya maze tamkar bai ji me suke fa'da ba.
Da murmushi ya ce "Ummilolona ke ce da sassafen nan?"
Ita ma da walwala ta ce "Eh Yaya Bulkachuwa barka na je nan gabanku ka'dan, shine na biyo na gaisheku ko na yi laifi?"
Da sauri ya hau girgiza kai tare da fa'din"kin yi daidai Ummi. Allah ya bada ladan zumunci".
Ta ce "Ameen."
Ya bita suka fita da kafarsu. Wata'kila har gidanta ya rakata domin ya jima bai shigo ba.
Hadari ya hadu mai k'arfin gaske. Daidai lokacin ya dawo tamkar jifa.
Sai da ya rufe k'ofar d'akin da yake yi mini isa, ya rufe tagogin falo.
Sannan ya shigo d'akina. Na kalle shi na dauke fuska domin haushinsa ya sake kama ni sosai.
Ya zauna a gefen gadon ya sanyaya murya ya ce "Albarkacin zuwan Ummi na ajiye fishina. Na huce, komai ya wuce".
Na yi kamar ban ji ba. Ya matso jikina sosai ya ru'ko ni, na fizge a fusace na ce "Bana son ka huce Tijjani. Domin dai ni bana ha'da sabgata da marar imani bare kuma tausayi."
Ya sassauta ya ce "me na yi na rashin tsoron Allah Asiya?"
Murya na rawa ina shirin kece wa kuka na ce "Ban da ka tabbata baka da tausayi mene ne zai sa ka jajibo aure alhalin ko wata biyu baka rufa da yin auren ba. Mene ne hakan inba rashin tsoron Allah da rashin imani ba?."
Ya sake matsowa jikina ta yadda bayansa na shafar cikina.
Ya yi k'asa da murya ya ce.
"Wallahi Asiya Toro tsoron Allah nake ji sosai. Shine shaidar hakan. Asalima saboda ina tsoronsa ya sanya na fara neman auren. Ya zan yi? A d'an zaman da muka yi ya kamata ki fahimci bazan iya ri'ke kaina alhalin ina ganin ki, muna kwana gida d'aya ba.
Ke kuma gaba'daya kin bijire , kin k'i saurara ta, tunda ba sona kike yi ba. Sanin zan iya fa'dawa halaka ya sanya na samu wata bazawara mai gajeran buri muke tattauna wa. Idan Allah ya yi zan aure ta. Kin ga shike nan na magance tashin hankalin da yake tsakaninmu, sannan na samu mafita daga hatsarin fa'dawa zina da aurena".
Yana rufe baki ba zato na mik'a hannuna na d'auko wata doguwar robar mai ta kokobota. Na kwad'a masa a goshi. Ina kwada masa tare da ce wa "Allah ka yi mini tsari da mugun k'ullin da yake zuciyar wannan bawan naka. Bilhiillazi kana da fitina Tijjani."
Chapter 73 · 0% Book details