Sashe 138
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
ce "oh saboda Ikilima zaki dinga zare mini ido? Sannu gyambo uwar son girma! Haka kike yiwa Yaya Tijjani?" Ta ce "Ai shi yayana ne kuma duk da hakan girmama ni yake kamar me saboda ya yarda surkuta gaskiya ne. Sai kawai kukan da take danne wa tunda ta ga jaririyaya ya kwace mata duk da dai wasa suke yi. Kowa ya yi k'asa da kansa ana taya ta kukan da take yi. Domin tun fil-azal idan akwai amintattun da ba cikinsu daya ba a gidan Marina to Yaya Ummi da Bulkachuwa ne. Akwai shakuwa da kauna a tsakaninsu mai yawa. A sanyaye ya ce "Ki yi hak'uri ummilolo! Ai yana fad'in hakan sai kuwa ta sake rushe wa da kuka na sosai. Don kuwa Bulkachuwa kad'ai yake ce mata ummilolo. Daada ma ta bare baki ta shiga taya ta suka dinga yin sa kamar me. Da k'yar suka yi shiru. Aliyu ya tafi jiki a sanyaye. Yana fad'in ba zan sake zolayar ki ba Ummi har sai d'an-uwan ki ya fito. Har dare babu nishadi a tare da mu.