← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 146

Sashe 86

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*End of part 2.*

*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*

*WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE BIYA KUDIN KARATUN KI TA WANNAN ASUSUN DAN GUJE WA BAKAR TA'ADA!*
*REGULAR 500*
*VIP 1K*
*VIA*
*2384876855*
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*

*KO*
*7061488065*
*SURAYYA DAHIRU IBRAHIM*
*OPAY DIGITAL SERVICES.*

*TURA SHAIDAR BIYA TA WADANNAN LAMBABOBIN*
*08032773332*
*09069067488*.

*MARUBUCIYA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*Tana farincikin sanar muku da sabon littafin ta mai suna YA ZA A YI? Wanda za ta sake shi ranar d'aya ga watan Oktoba (first October) wannan karon ma marubuciyar taku ta shirya sosai domin nishad'antar daku tare da fad'akarwa🥰 Ba sai na tsaya yi muku bayanin rubutunta ba domin da yawa daga cikin masu bibiyar litattafanta sun san cewa tana k'okari gurin ganin ta yi rubutu akan abubuwan da suke faruwa, mussaman a zamantakewar aure da tarbiyar yaranmu, Uwa uba kuma litattafanta akwai soyayya mai tsafta da nishadi da 'karuwa! Kada dai ku sake a baku labarin wannan littafin mai suna( YA ZA A YI)❓ Zaku iya yi mata magana ta Whatsapp da wannan numbers*
*08089965176*
*07084653262*

Har muka isa gidan ba wanda ya yi magana.
Kai tsaye daki ya shige ya yi kwanciyarsa. Ni kuma na shiga kicin na sama wa kaina abin da zan ci. Sannan na yi wanka. Na gyara jikina sosai, na isa dakin na tsaya gaban madubi na bi ko ina na goga turare.
Na tarar da shi idon sa biyu. Na zauna na tausasa murya na ce "Fa'da mini abin da na yi, mu shirya kafin Yaya Ummi ta zo".
Ko motsi bai yi ba, bare ya yi magana.
Na zuba masa ido ina tuna yadda yake rawar jiki da tsoron fishina. Amma tunda ya fahimci na fa'da komar sa shikenan abu ka'dan zai fitittike ya yi mini fishi.
Na kai hannu na fara shafa sumar kansa da nufin lallashi tunda na gane shi mutum ne mai son a rarrashe shi tamkar mace.
Da kakkausar murya ya ce "Bari Asiya Toro".
Nan da nan kuwa na cire hannun nawa domin gargadi ya yi mini mai kauri.
Haka muka kwana duk rai babu da'di.
K'arfe takwas sai ga Yaya Ummi da alamu tare suka fito da yaranta yan makaranta su suka wuce ita ta taho nan.
A falo muka zauna.
Ita ta fara ce wa Yaya Bulkachuwa ka ga yadda ka koma kuwa me yake faruwa ne?"
Ga mamakina yana bu'de baki sai ce wa ya yi "Ba'kin cikin Asiya ne yake neman kassara ni".
Gabana ya takarkare ya fadi. Me nake yi masa ni Yabi?"
Yaya Ummi ta ce "me ya faru haka Yaya Bulkachuwa?"
Na kasa kunne sosai dan na fahimci abin da zai ce da kyau.
Sai ji na yi ya fara rattabo laifukan da nake yi.
Cikin nutsuwa ya ce "Ummi tunda aka rufe gidan burodi da nake zuwa na shiga yanayin rashin ku'di. Har ta kai bana iya yin abin da ya kamata. A farko rimi rimi Asiya ta ke ha'kuri da duk abin da zan kawo. Tare zata sarrafa mu ci, ko da garin kwakai ne. Amma tafiyar bata yi nisa ba sai ta fara gazawa. Ta fara raina kokarina saboda an riga an cusa mata akidar watarana ita ce zata rike mini gidan. Komai zan siyo na bata ba zata yi amfani da shi ba. Kwanaki na siyo sabulun wanka Gif har yau bata ta'ba ba, ta bayar an siyo mata wanda ya dace da ita.
Duk ban ce komai ba. Sai shekaranjiya kuma ta ce mini zata fita, ban zaci wai gida gida zata dinga bi tamkar dilalliya ba. Tun safe da ta fita sai yamma lis ta dawo wai ashe gida je ta dinga bi tana yin k'unshi ana biyanta saboda kawai ta fahimtar da kowa ita ce take ri'ke da ni!
Ya nisa ya zarce da fa'din tana shigo wa ta tarar na yi komai Kamar yadda ta sani tun farko ni aikin gida bai zame mini komai ba, amma kinsan me ta ce mini?"
Yaya Ummi ta girgiza kai cikin sanyin jiki.
"Tana bude baki sai ce mini ta yi wai na zama Yabi. Wato na zama mace mai zaman gida, ita kuma ta zama namiji mai fita ya yi gwagwarmaya. Duk yadda maganar ta buge ni hakan na daure na ha'diye maganar na kawar mata da kai!
Ya fa'da yana hucin b'acin rai.
Gaba'daya jikina ya mutu, zufa sai keto mini take yi. Na tabbatar duk abubuwan da ya lissafo ina yinsu tabbas. Amma ko ka'dan a zuciyata ban daukesu zasu b'ata masa rai ba. Domin ko ka'dan ban yi da nufin wula'kanci ko na muzanci ba. Asalima ni na yi ne da nufin kyautatawa.
Kafin Yaya Ummi ta ce komai sai ya cigaba da fa'din "Jiya kuma ta ce mini zata fita ban amsa mata ba. Sai kawai na dawo na tarar bata gidan, tun azahar nake zaman jiranta bata dawo ba sai tara saura. Fa'da mini Ummi me ta mayar da ni, me kuma take nufi da ni ne?"
Yaya Ummi ta yi shiru ta rasa abin fa'da domin ta fahimci ransa ba k'aramin baci ya yi ba.
Sai kawai ta buge da ba shi hakuri tare da ce wa"Tabbas ta yi kurakure, amma ka yi hakuri zata kiyaye."
Ya girgiza kai ya ce "Ba fa zan yi hakuri ba tunda ba zan dauki wadannan BAK'AK'EN TA'ADODIN da ta fara tsirarsu tun daga yanzu ba. Gara manyammu su san halin da muke ciki kada abu marar da'di ya faru ace na bawa marar d'a kunya."
Yaya Ummi ta yi maza ta ce haba dai, haba dai Yaya Bulkachuwa ba abin da zai faru sai alheri. Ai gata nan duk ta ji abin da ka fa'da, za kuma ta kiyaye."
Ya girgiza kai ya ce "Kin san kafiyarta, ba ji zata yi ba, ni kuma ba zan yarda ba. Kin ga gara komai a yi shi a bayyane ba sai abu ya yi tsananin da rayuka zasu baci da yawa ba".
Ni gaba'daya ma mamaki ya ba ni, ya fitittike akan sai na tafi, ita kuma Yaya Ummi sai wani lallab'a shi ta ke yi. Yo ni ban da ina jin tsoron al'amarin da zan fuskanta a gidnman Marina ma zunde da dariya, da ba'kin cikin da zan jefa iyayena da na girgije na bar masa gidansa.
Ta kallo ni tare da mini signal din na ba shi hakuri. Na dauke kai na juyar da fuskata. Domin nima na hauro ai komai nake yi dominsa ne. Amma tunda shi ba zan yi masa alheri ya yaba ba, sai dai ya bini da sarhutu to shi kenan na daina yin komai. Fita k'unshi da sunan Home service kuwa na soke sai ya nemo wani laifin kuma. A k'asa zuciyata kuma sai hirji nake yi tare da fatan Yaya Ummi ta kashe wannan matsalar domin duk yadda na hauro nake kurarin zan iya tafiya din, zuciyata tafi son zaman, nafo son ya huce ko ba dan ahalin Marina ba. A karan kaina na damu da fishinsa.
Da k'yar Yaya Ummi ta shawo kansa ya ha'kura da maganar sai mun je gaban Baban Marina. Ta bu'de murya ta ce "Ki ba shi hakuri".
Fuska a daure, amma cikin azama na ce "Allah ya baka hakuri".
Daga haka na tsuke fuskata da bakina.
Tare muka karya da ita. Sai da zai fita suka tafi tare ya sauke ta a gidanta.
Ban zauna ba sai da na yi abinci na zuba a flask.
Na gyara ko ina, sannan na fara yiwa wata da ta zo k'unshi. Bai dawo ba sai yamma, kafin lokacin kuwa na yiwa mutum hudu duk sun tafi. Budurwa d'aya ce ta rage da yake ita zan mata bak'i da kuma kitso.
Da azama na saki kitson na fita ina yi masa barka da dawo wa, domin ya tsani ya dawo ban bar abin da nake yi, na je gare shi ba.
Idan wani ne ya fa'da mini Bulkachuwa zai dinga yi mini irin wannan mulkin mallakar zan k'arya ta shi kai tsaye. Ni da kaina mamakin kaina na ke yi. Na yadda nake rawar jiki a kansa. Wata'kila kuma yadda yake sarrafa ni ne sirrin. Gabadaya tsoron fishinsa nake yi tamkar me.
Ya mik'o mini ledar hannunsa mai dauke da karas da atile.
Hannu biyu nasa na kar'ba na dinga fa'din "Na gode, Allah ya k'ara budi.".
Na wanke hannuna, na yi kicin na ha'da abincinsa na kai masa.
Na debo pure water masu sanyi guda biyu na saka a plate. Na ajiye a gabansa.
Na fita na debo masa karas da atilen na zuba a bowl na wanke na kai gabansa.
Na dan yi jim na kalle shi yana cin abincinsa cikin nutsuwa. A hankali na ce "zan je na k'arisa kitso."
Da walwala ya ce "To".
Na fita, a raina kuwa sai fa'din nake yi sarkin son mulkin tsiya. Kai Tijjani baka bai ni haka ba, Yasin"
Da daddare ya dinga laluba ta, na maze ban yi masa abin da nake yi masa ba.
Ya fara ce wa "Amma dai kin san bana son haka, sannan kuma kin san kin ci bashina jiya".
Da sauri na ce "Ba wani bashin ka da na ci. Kai ne ka kawar da kai, alhalin ka ce ko mun yi fa'da kada mu saka aurenmu a ciki. Amma jiya sai da ka saka su tsundum."
Cikin kwantar da murya ya ce "Hankalina ne ya tashi matu'ka da gaske. A ce matar aurena tana garanranba a gidajen mutane har almuru da sunan sana'a? Ai k'arshen tozarci ke nan. Amma ai na ha'kura kin san ina sonki fiye da komai Asiya. Ban so wani abu a duniyar nan da ya zarta ki ba. Uwa da ubana ne kawai a gaban ki. Dan haka ki daina damun kanki akan wasu matan. Ba sonsu nake yi ba. Da gaske ba wacce nake so a zuciyata sai ke. Amma zan iya ganin wata ta burge ni ko ta bani sha'awa a dalilin Ubangiji ya sanya sha'awar mace sama da d'aya a zuciyar mazaje. Kullum ina ro'kon Ubangiji ya tsare ni da sha'awar wata macen fiye da ke. Duk sadda na ga wata zata burge ni ko ta ba ni sha'awa gida zan garzayo na ga halalina, na yi abin da nake so da ita. Ke dai idan kin gan ni afujajan na dawo miki, to ban da musu da bijire wa da sunan jan aji".
Dan haka ki saki ranki da ni, ke nake so, ke ce halaliya ta, da ke nake fatan na rayu muddin rai".
Na fara k'ananun hawaye na ce "To kuma nufinka korata da ka yi da daddare a ganduna ne? Ya tafi a bilis?"
Ya tarairayo ni cikin rad'a ya ce "Ai ya wuce tunda da kaina na je na dawo da ke".
Na fara turza k'afa ina fa'din "Alkur'an ban yarda ba".
Ya sheke da dariya ya ce "Dole sai kin nuna mini kina da alaka da mutanan Gwaram da Birin kudu domin a bakinsu nake jin wannan rantsuwar".
Na ce "To mahaifiyata ta fito daga yankin ai kuwa kasan jininsu ce".
Ya ce "Haka ne. To yanzu me zan yi ki yarda ki huce".
Na shiru ina tunani sai kawai na ce "Yi mini kukan zakara".
Ya ce "kukan sa wanne a ciki?"
Na ce "oh kukan zakaran kala kala ne?"
Chapter 86 · 0% Book details