← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 146

Sashe 64

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

na ga ya ajiye mini burodi. Na ga kuma kusan duk kayansa har wanda ban ga ya sa ba, ya wanke su, ya shanya su a igiya reras. Ashe fitar da yake yi da asuba aiki ya samu a gidan burodi. Kullum ya je suka yi aikin kwabi da d'aure wa. Za'a bashi babban burodi d'aya da donot guda hudu, da ku'di dubu da dari biyar. Idan ya dawo kuma ya huta sai ya fita gurin aikin saka tiles ko na gyaran setlite ko had'awa. Duk abin da ya samu a ranar zai yi. Na burodin ne sau hudu a sati. Dan haka baya rasa yan k'udade hidimar yau da kullum tunda ya k'i jikinsa. Mafi yawa kullum sai ya shigo da taliya daya ko macaroni. Wani lokacin kuma magi rabin leda sai da na ga robar maggin ta sake cika duk da bamu cinye kayan abincin namu ba. Da na yi tsam sai na fahimci baya son kayan abincin su k'are ne. Shi yasa kullum sai ya siyo wani abu ya ajiye akan kayan abincin, duk da har yanzu girkinmu ba kankama ya yi ba, sai na ga dama nake dafa wa. Jiya da garin rogo ya shigo rabin kwano. Ban ce masa komai ba, da na ga ni. Amma har zuciyata na fara gamsuwa Tijjani ba zai bar ni da hidimar gidansa ba, kamar yadda ake hasashe. Sai dai bazan yi saurin shaidar hakan ba sai nan gaba. Shiru bai dawo ba, yan k'unshi suka zo. Na rasa yadda zan yi, rana ta take barandar ba zata zaunu ba tunda inuwa bata zo wajen ba. Ni kuma ina k'yashin yi a falona. Na kasa samun mafita. Kan dole na ce musu "Ba ni da lafiya bazan iya yi ba. Suka tafi suna mini fatan samun lafiya, tunda sun san ni, sun ga kuma ramar da na yi. Suna fita yana shigo wa da alamu sun yi kicibus ma. Na kalle shi na dauke kai. Ya zuba mini ido ya ce "Sai yaushe zaki fara yi mini oyoyo da barka da dawowa ne?" Na gatsina fuska na ce "Eh ai ka yi mini sallama da zaka fice, bare ka saka ran zan yi maka sannu idan ka dawo". Ya girgiza kai ya ce "kullum fa sai na yi miki sallama Asiya. Yau ma sai da na leko na ga barcin na ki ya yi nauyi. Ni kuma wai kada na katse miki shi yasa na fita. Amma ki yi ha'kuri". Na dauke kai na ce "To". Ya mik'o mini leda tare da ce wa "Ungo nasan ki da son gurjiya, ganin ta na yi manya manya da ita. Shine na siyo, na taho na kawo miki". Na kar'ba a hankali na ce "Na gode". Karon farko da na yaba masa har na yi godiya. Da'di ya kama shi ya ce "Nima na gode miki. Ko na zauna na bare miki ne?" Tausayinsa ya kama ni wanda nake kasa gane dalilin raunin da yake kama ni akan sha'aninsa. A hankali na ce "Na hutar da kai" Dadi ya sake kama shi, walwalarsa ta karu. Ya zauna kusa da ni ya ce "Fa'da mini sunan turare mai k'amshi, kuma mai sau'kin ku'di." Kamar bazan kula shi ba. Sai kuma na bu'de baki na ce Dagmar". Ya zuba mini ido sosai sannan ya ce "Na tsani turaren nan, duk yadda yake da dadi mai nutsar da zuciya Asiya. Ya mike ya girgiza kai ya ce "Na gode da wula'kanci! Ai na sha ganin kwalin turaren a dakin Jabir. Shine kike son nima na saka saboda ki dinga jin kamshinsa a tare da ni?" Ba'kin cikin da yake zuciyarsa ya kasa boyuwa. Ya juya ya bar gidan gaba'daya. Kafin na tashi, sai ga shi ya dawo ya kwashe kayansa ya shiga da su dakin ba tare da ya tsaya ninke wa ba. Ya fito a hanzarce ya fice tamkar kububuwa. Abin mamaki sai na ji babu da'di. Yadda idonsa ya canja launi duk sai na damu ainun. Ga shi ban roke ki shi ya bar ni na dinga zama a dakin da yake yi mini tijara a kansa ba. Na tashi na shiga d'akin. Na ga ya zube su akan tabarmar da take shinfide a k'asa. Kamar na ninke sai kuma na fasa. Na janyo na rufe masa. Da yamma sai ga shi ya dawo da cakwal da gawayinsa a leda. A tsakar gidan ya yi shimfida. Ya fita ban san inda ya samo rushi ba. Na ga dai ya zo ya zuba gawayi akai. Tunda ya fara gugar nan bai tashi ba, sai da ya kammala tsab. Ya kalle ni ya ce "kin dafa abincin, ko baki yi ba?" Ba walwala na ce "Na dafa". Ya ce "To a dan bani". Ya fa'da fuskarsa a tamke. Na tashi na zubo masa, na rufe sannan na kawo. A wajen ya ci. Sannan ya kwashe kayansa ya yi dakinsa da su. Zuciyata ta yi nauyi tabbacin da gaske ba zai bar mini dakin ba. Ya fito, ya shiga wanka. Ina zaune a barandar ya fito cikin farar shaddarsa wani irin kamshi sai dukan hancina yake yi. Kamshin da ban ta'ba jin irinsa ba, mai matu'kar da'di. Ya yi kyau tamkar wani hamshakin attajiri. Zuciyata ta buga da irin haduwarsa, ya taje sumar kan nasa da take cike. Gashi bai sanya hula ba. Shaddar ta gogu. Kuma babu dying tunda ya sake waccar mai cibiri cibiri lokacin bikinmu, bai sake b'ata ta ba. Ya dai tara amma babu rini ko murde wa. Na kasa gane me nake ji. Na gan shi a yadda nake son ganinsa. Bai wani tsaya ba ya ce "Sai na dawo ya fice da alama masallaci za shi. Amma ga mamakina bai dawo ba sai da tara ta gota. Sannan da ya shigo ina jinsa da Rafia a zaure da alamu ita ma unguwa ta je a lokacin ta dawo. Da k'arfi ta ce "Ka gaida amarya kwana biyu bana zama ne shi yasa ban shigo ba". Ban ji me ya ce mata, tunda bai daga tasa muryar ba. Wani irin abu mai tsananin gaske ya tokare ni. Shaidan ya shiga zuciyata ya ayyana mini tare suka dawo. Shashanci suka je suka yi abunsu. Hawaye ya b'alle mini. Ya tarar da ni ina matsar k'walla. A rikice ya zauna kusa da ni ya ru'ko ni. Na fizge cikin kuka sosai na ce "Ka je kun gama iskancin kun dawo shine zaka ri'ke ni?" Ya zauna ya ri'ke kansa. Ya kasa ce wa komai. Amma ba k'aramin kidima ya shiga ba.
Chapter 64 · 0% Book details