← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 146

Sashe 13

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

7&8. Maganar Baban Marina ta dawo da ni tunanin da nake yi. Kamar a sama na ji ya ce "Na gode miki Asiya! Duk yadda nake jan kunnenki akan b'atawa Dada rai, da kuma dukan yaran gidan nan ba kya ji, saboda kin riga kin zama y'ar kuka. Uwarki kullum cikin yi miki kashedi akan shiga fa'dan yara da kuma tsokanar Dada, amma duk a iska ko? Na gode sosai da wannan bacin rai da kika sanya ni, Allah ya shirye ki". Ya tsugunna gaban Dada ya ce "Ki yi ha'kuri! Halin Asiya ni kaina ha'kuri nake yi da ita, amma zan dauki mataki akan ta'ba ki da take yi". Ta kyabe baki ta ce "To ka fara dan takidin aurensu. Jiya mun tattauna da kannenka sun ce su babu matsala ko yaushe auren ya zo a shirye suke, kai dai za'a fa'dawa ka fara tanadin tunda yaran ka har biyu ne". Ya yi gyara murya cikin k'arfin hali ya ce "Babu damuwa Dada ina saka rai Ubangiji zai kawo mini hanyar da zan samu na yi musu iya abin da zan iya." Ta murmusa tamkar ba ita ce mai kuka tana face majina ba. Ta ce "To babu laifi Allah ya basu na gari, masu kuma ha'kuri, domin mai yakana ne zai iya zama da Yabi dan wuyar zamanta ya kai inda ya kai, ba inda ta baro uwarta". Cikin sanyin jiki Baba ya mike yana cewa"Dada sai da safe mu kwana lafiya". Ta amsa masa da fa'din "Allah ya tashe mu lafiya". Na mike, Nazira ma ta biyo ni muka fice, ba tare da mun ce uffan ba. Domin na sake fusata da ta ce sun tattauna da kannensa amma shi ba'a saka shi cikin zaman ba. Muna jin ta tana fa'din "Wanda Allah ya bashi tsawon rai zai yi kallon tak'ama a wajen ki Yabi. Yarinya da ke amma kusan ke kike juya shashinku gaba'daya. Kina tashi Yayarki ta biki zungui zungui ko sallama ta kasa yi mini saboda tana rarrashin zuciyarki?". Ban juya ba, bare na tanka mata, balle kuma Nazira da take da sau'kin hali. Muna shiga shashinmu muka yi turus a dalilin halin da muka ga mahaifinmu a ciki, zaune yake akan tabarma a tsakargida. Sai fifita Gwaggo take yi masa, gumi na yanko masa babu kakkautawa. Muka isa gabansa, muka tsugunna, baki na rawa na ce "Sannu Babanmu! Abin mamaki sai ya daga mini hannu tabbacin ya amsa gaisuwar tawa. Nazira ma ta yi masa sannu ya amsa ta hanyar gyada mata kai. Mama ta fito daga bandaki ta kalle ni ta ce "Wannan ja'irar yarinyar sai kin zama sanadin mayar da kananun ya'yansa marayu, fitananniya tabtacciya. Ai duk gwanin na iya a rana ya ke" Ta ja tsaki mai tsanani ta wuce d'akinta. Bata jima da shiga ba ta k'walawa Nazira kira, ta mike a hanzarce ta nufi dakin nasu. Daidai lokacin Baba ya dan samu sau'kin zufar da take karyo masa. Ya yafito ni, jiki na rawa na isa gabansa. Ga mamakina sai ya mik'o mini hannunsa na dama. Hannu bibbiyu na ri'ke hannun nasa, cikin barin jiki gaba'daya. A sanyaye ya ce "Ina alfahari da ke Yabi! Kafatalin ya'yana ke nake da tabbaci akan ba zaki cigaba da yin mini *Bak'ar Ta'ada* ta y'an ubanci ba, na tabbatar da hakan. Ina saka rai ta dalilinki yarana zasu dawo tsintsiya. Na so ace da wuri na haife ki Yabi. Da al'amuran da suka dame ni basu yi mini tsananin da nake ciki ba. Amma Alhamdulillah! Ubangijinmu baya kuskure na gode masa, ina kuma tuba a gare shi." Hawaye tuni ya goce mini dukkan zuciyata a jagule take da tsananin tausayin Mahaifina da a yau nake ganin wani irin tashin hankali da raunin da ban ta'ba ganinsa a ciki ba. Gwaggo tana fifita, tana kuma share k'walla.y Ya numfasa ya ce "Idan na mutu Yabi, duk runtsi ku gaisa da yan'uwana, ko ba zasu taimakeku ba, to lallai ku dinga saka su a cikin al'muranku, idan kina yi, sannu a hankali zaki samu wanda zasu yi koyi da ke, tunda tun yanzu al'amura sun haska ke ce mai tsayayyen ra'ayi wanda yafi kusa da kyau da kuma dace wa." Murya na rawa na ce "Mu sasu a alamuranmu ko da ba zasu taimakemu ba, ko da idan mun fa'da musun ba zasu dauki al'amarin namu da girma ba?" Ya sake damk'e hannuna ya ce "Haka nake so Yabi". Da karfin zuciya na ce "Da Ikon Ubangiji zan yi yak'i da dukkan zuciyata na yi hakan. Amma ina ro'kon arziki ka mini afuwa, ka yafe mini muzancin da na janyo maka dazu". Ya girgiza kai ya ce "Baki yi laifi ba, na sani. Sannan su d'in ma bana son ki d'auki abin da suka yi mini a matsayin muzanci ko tozarci, na sani baki da sauki, kina da ru'ko, dan haka na umarce ki, ki manta komai". Na murmusa hawaye na kwaranyo wa na ce "Shi kenan Babanmu! Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, yadda a ke mini habaicin tunda aka haife ni ka tsiyace, ina ro'kon Ubangiji kullum, ya saka idan na girma na samu sanadin da arzikinka zai dawo ta dalilina fiye da wadda ka rasa a shekarar da na iso duniya". Ya ce "Rabu da maganar jahilai, ko iya hakan na ga ni ai na gode, sanadin sana'arki na daina fargabar a tambaye ni ku'din sabulu a gidana. Alherin da kika janyo mini mai yawa ne, mafi farin-ciki a ciki shine wanda kike yarda ya'yan da na haifa duka daya ne a wajenki ta fuskantar mua'amala ta zahiri." Da'di ya tsirga mini ban ta'ba zaton Baba ya fahimci yadda nake da ra'ayin rikau akan kannena ba, bansan ya fahimci ina tare musu fa'da ba, hakanan ban san hakan yana yi masa da'di ba, tunda kullum a cikin kirarin bani da hakuri yake. Sannan kuma baya ta'ba nuna mini ina abin a yaba, sai dai ya ce ai duka yan'uwane tunda ragowar ma y'ay'ansa ne da yan'uwansa suka haifa masa. Cikin son na sake k'arfafa nasa guiwa na ce "Duk d'an da ka haifa ina jin sonsa har cikin zuciyata Baba". Idonsa ya ciko da k'wallah cikin k'arfin hali ya ce "Allah ka shirya mini yarana, ka saukaka musu, ka basu lafiya, ka cika zuciyarsu da tsoronka, ka jefa soyayya da tausayin juna a tsakaninsu. Allah ya yi miki albarka Yabi". Daga ni har Gwaggo muka hau fa'din "Ameen ameen". Na kalli Gwaggo na ga hawaye ya goce mata, jikina ya sake yin sanyi, domin ita din wata irin mace ce mai k'arfin zuciya k'warai da gaske, abin da zai saka ta yi kuka to kuwa ya girgiza ta ba ka'dan ba, duk tsananin da take fuskanta a rayuwar gidanmu ban ta'ba ganin ta yi kuka ba. Na yi kasa da kaina cikin rauni mai yawa na ce "Ameen Baba! Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai albarka. Na gode sosai". Duk muka yi shiru kowa na cikin alhini. A hakan Nazira ta fito rai a bace da gani Mama sababin yadda ta like mini ta yi mata. Kusa da ni ta zauna, cikin sanyin murya ta ce "Sannu Baba". Murya ba amo ya ce "Sannu kadai Nazira, Allah ya kara miki ha'kuri kin ji. Ki cigaba da jajirce wa a kan gaskiya ko da hakan ya ci karo da ra'ayin kowa, ku so junanku, ku binne a tsakaninku, kin fi Yabi ha'kuri, a duk sadda kika ga zata yi aikin nadama yi amfani da fikon da kika yi mata ki dakatar da ita, komin runtsi kada ki bari ta dauki hukunci cikin fishi. Ke kuma Yabi kul kika ki jin shawararta, idan ta ce yi ha'kuri, to na roki ki bar abin nan komin girmansa. Ina jaddada muku ne dan ku ri'ke su da kyau, ko babu ni idan kuka ri'ke maganganuna ba zaku ta'be ba. Allah ya yi muku albarka ya ha'da ku da maza na gari, ya raba ku da sharrin shaidan a cikin zumunta". Muka amsa da Ameen amen cikin sanyin jiki. Nazira ta mika hannu ta karb'i Maficin hannun Gwaggo ta cigaba da yi masa fifita, duk da gumin ya yi sau'ki. Har lokacin kuma bai saki hannuna ba. Ya jima kafin ya saki hannuna yana sake cewa "Na hore ki da ha'kuri Yabi! Ku zauna da yan'uwana lafiya, ku mutunta su, ku gaishe su da girmama wa". Na gyada kai yayin da Nazira ta ce "Duk yadda kake so hakan zamu yi, amma ka taimake mu ka daina sanya damuwa a ranka Baba! Fatanamu mu ganka a tsaye akan kafafuwanka, idan muna ganinka cikin walwala ba abin da zai dame mu sosai." Haka muka kwanta ni da Nazira tana ta jan kunnena na kiyayi Dada, tunda zata iya yin ha'din kitifo har ya zama sanadin da za'a samu damar cin zarafin Babanmu akan idonmu. Tun daga wannan ranar na kame bakina a gaban Dada, duk karatun da zata yi bana tankawa, haka nan ban cika zama na yi doguwar magana da ita ba. Zanje gaishe ta babu fashi, kuma sai na tabbatar mun ha'da ido sannan zan kama sunanta na gaishe ta. Na daina jan magana a tsakaninmu ne kawai. Sannan na soke zuwa hirar dare, amma matu'kar zata d'ora karatu sai ta sa an kira ni. Janye war da na yi da ita kuma sai ya dame ta, amma ta kasa bu'de baki ta yi magana. Tunda Nazira ma ba wani sake wa take yi ba, balle ta yi mata korafi. *** Karshen wata Yaya J ya dawo. Mun taso daga Islamiya muka ganshi zaune akan dandamalin kofar gidanmu. Sanye yake cikin kananun Kaya da suka yi matu'kar kar'barsa, sai kamshin turaren Dagmar yake tashi sannu a hankali. Dukkan y'anmatan suka hau rige-rigen gaishe shi, yayin da ni na sunkuyar da kai kasa alamun kunya. Na zo wucewa ta gefensa na saci kallonsa ai kuwa karaf muka hada ido, wani irin abu ya tsikare ni, kwalliya da tsabtar Yaya J ko mace ce ta kai a sata a masu tsabta, sannan kankantarsa tana sawa na ji mun dace da juna. Domin da ka'dan ya zarta ni cika ido da tsayi. Babban abin burgewa mai nutsuwa ne, sannan mai ha'kuri ne,
Chapter 13 · 0% Book details